HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ba da umarnin kulle dukkan gidajen wasanni na gala da ke faɗin jihar domin shigowar watan Ramadan.
Wannan sanarwa ta fito ne ta hannun
jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman.
Sanarwar ta ce, “Wannan na zuwa ne biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin ‘yan ƙungiyar masu gidajen galar reshen Jihar Kano a ofishin sa.”
A cewar hukumar, wadda ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-Mustapha, dokar za ta fara aiki ne tun daga yau Lahadi har zuwa 1 ga Shawwal, wato ranar bikin Ƙaramar Sallah.
Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu gidajen wasannin da su guji karya doka domin duk wanda ta samu da laifin karya dokar za ta ɗauki tsattsauran mataki a kan sa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na dindindin.
A zaman, El-Mustapha ya gode wa jagororin tare da ‘ya’yan ƙungiyar haɗi da al’ummar jihar saboda da haɗin kan da su ke ba hukumar a kowane lokaci.
A ƙarshe, ya ƙara tunatar da dukkan al’umma cewa ƙofar sa a buɗe take domin ba shi shawara ko sanar da hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar ayyukan da ta saka a gaba.
![]()







