• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, October 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ali Nuhu ya kama ragamar aiki a NFC tare da alƙawarin haɓaka harkar fim a Nijeriya

by ABBA MUHAMMAD
March 12, 2024
in Labarai
0
Ali Nuhu ya kama ragamar aiki a NFC tare da alƙawarin haɓaka harkar fim a Nijeriya

Ali Nuhu (a hagu) a lokacin da ya ke karɓar takardun kama aiki a yau a Jos

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Talata ne sabon Manajan Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya fara aiki a hukumance tare da yin alƙawarin hanzarta kawo cigaban masana’antar finafinan Nijeriya da kuzari da jajircewa.

Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar, Mista Brian Etuk, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ga ‘yan jarida.

Ya ce a ƙwarya-ƙwaryan bikin miƙa mulkin wanda aka yi a hedikwatar hukumar da ke Jos, Jihar Filato, Ali Nuhu ya ce ya ƙudiri aniyar yin amfani da ɗimbin sanin makamar aiki da ya samu wajen ƙara tsara yadda za a gudanar da aikin bunƙasa masana’antar finafinan ta Nijeriya.

Ali, wanda shi ne na bakwai a jerin waɗanda su ka riƙe hukumar, ya yi tsokaci ne kan tsammanin Gwamnatin Tarayya, finafinai da sauran masu ruwa da tsaki da kuma nagartattun al’ummar Nijeriya kan rawar da ya kamata hukumar ta taka a cikin tsarin ƙere-ƙere na ƙasa da na duniya.

Ya ba da tabbacin cewa zai jagoranci hukumar zuwa ga kyakkyawan aikin da ba a taɓa gani ba a cikin isar da aiki wanda zai kasance a kan lokaci, fa’ida, aune, ɗorewa da tasiri.

Ya ce, “Aikin yin amfani da damar da ake da shi a fannin ƙere-ƙere na Nijeriya, musamman fannin shirya finafinai, wajen ciyar da manufofi da manufofin Gwamnatin Tarayya wajen bunƙasa cigaban ƙasa, za a yi amfani da shi ne a kan tsarin hukumar NFC.

“Za a ba da kulawar da ta dace ga hukumar ta NFC a matsayin fitilar ƙwazo a cikin yanayin finafinai na ƙasa, nahiya da na duniya.”

Ali ya jero tsari da aiwatar da ingantattun tsare-tsare na masana’antar finafinai, inda ya ce za a haɓaka horaswa, iyawa, hazaƙa da ƙwarewa; kayan aikin shirya finafinai don haɓaka masana’antu da gasa, don ganin finafinan Nijeriya a cikin ƙasa da waje, haɗin gwiwa tare da manyan hukumomi da ƙungiyoyi na gwamnati da masu zaman kan su, da kuma masu ruwa da tsaki na duniya don haɓaka ƙirƙira, jawo hankali don zuba jari da kuma sauƙaƙa haɗin gwiwar yin fim.

Haka kuma ya bayyana matuƙar jin daɗin sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan naɗin nasa, kamar yadda ya yaba da kuma alƙawarin tallafa wa manufofin Barr. Hannatu Musawa, wato Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira wajen bunƙasa fannin finafinai.

Da yake nasa jawabin, Daraktan Shirye-shirye Da Bada Tallafa wa Industiri na hukumar ta NFC, Mista Edmund Peters, ya ce hukumar ta samu gagarumar nasara tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1979.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar gudanarwa da ma’aikata kan yadda Ali Nuhu zai jagoranci hukumar zuwa wani matsayi mai girma.

Peters ya ce, “Sabon babban jami’in ya yi dacen samun ma’aikatan masu sadaukarwa waɗanda a shirye su ke su tallafa masa yayin da aka fara wannan sabuwar tafiya ta hanyar amfani da ƙarfin hukumar NFC don zama babbar hukumar cigaban fannin finafinai gaba ɗaya.”

Ali Nuhu a tsakiyar dandazon jama’ar da su ka halarci bikin karɓar ragamar

Shugabanni da ma’aikatan na NFC, da manyan jami’an gwamnati da sauran jama’a sun halarci bikin miƙa mulki.

Mahalartan sun haɗa da Alhaji Abba El-Mustapha, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Barr. Ezra Jinang, babban mai tallafa wa gwamnan Filato kan Ƙirƙira da Nishaɗi; Alhaji Sani Muazu, tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), furodusoshi da jaruman Kannywood, Sir Eward Fom na ƙungiyar masu shirya finafinai (AMP), Alfred Mgbejume, Achor Yusuf, da Umar Tanko Ravi, Baballe Hayatu, Adam A. Zango, Al-Amin Buhari, Yusuf Lazio, Lawal Ahmad, wakilan shugabannin ƙungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta Nijeriya (AGN), ƙungiyar daraktoci ta Nijeriya (DGN) da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da kuma masu shirya finafinai da dama.

Loading

Tags: Ali NuhuHukumar Shirya Finafinai ta Nijeriyakama aikiNFC
Previous Post

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

Next Post

Marubuciya Halima Kurmin Mashi ta yi rashin mahaifiya

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Marubuciya Halima Kurmin Mashi ta yi rashin mahaifiya

Marubuciya Halima Kurmin Mashi ta yi rashin mahaifiya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!