TSOHUWAR jaruma kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Mansurah Isah, ta samo wani babban tallafi daga Cibiyar Haɓaka Fasahar Yaɗa Labarai ta Ƙasa, wato National Information Technology Development Agency (NITDA), wanda take da burin yin amfani da shi wajen taimaka wa matan Kannywood domin su dogara da kan su. Ta ce ya dace da su a maimakon su riƙa fitowa a matsayin jarumai kawai, wanda daga an daina yayin su ko suka yi aure, shi kenan sana’ar tasu ta tsaya. A ganin ta, wannan tallafi wata dama ce ta samu da za ta koyar da matan duk wasu harkoki na sana’ar fim don a kawar masu da tunanin cewar sai aktin kawai za su iya.
A Turance, kayayyakin da NITDA ta ba Mansurah su ne:
-
1 Alienware M18 R2 gaming laptop
-
1 TraceMR178i gaming desktop
-
2 4K monitors
-
1 Maverick 1550VA UPS
-
1 Adobe Premiere 2024 software
-
internal and external SSD drives
-
1 40-inch smart TV
-
1 DaVinci Resolve Studio
-
PluralEyes software
-
1 cinema line camera
-
high-quality lenses
-
memory cards
-
1 professional tripod
-
a mini drone
A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, Hajiya Mansurah ta bayyana yadda ta samu wannan tallafin daga Gwamnatin Tarayya da kuma hanyoyin da ta bi don ganin an cimma nasarar samun sa.
Haka kuma ta bayyana burin da take da shi don ganin masana’antar Kannywood ta ci moriyar wannan tallafin.
FIM: Mansurah Isah, mun samu labarin wani tallafin kayayyakin bunƙasa harkar fim da kika samu daga Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙashin National Information Technology Development Agency (NITDA). Ya aka yi kika samu wannan tallafin da kuma yadda za ku yi amfani da shi don bunƙasa harkar fim?
MANSURAH ISAH: To, da farko bayan sallama zan gabatar da kai na a matsayin jaruma, furodusa, darakta, kuma a matsayi na na mace a cikin Kannywood duba da yadda maza ne suke da ƙarfi a kowane ɓangare na harkar, zan iya cewa ma sun mamaye komai, saboda furodusa ɗin za ka ga duk maza ne, darakta da sauran ɓangarori za ka ga duk maza ne.
To wannan abin ya sa na zauna na yi nazari na ga to mu matan nan me muke yi ne? Kuma duk wata mace idan ta zo harkar fim ba ta da wani tunani sai na ta zama jaruma, duk da cewa akwai ɗimbin arziki a cikin harkar ta hanyoyi da dama a cikin harkar wanda mu mata sam ba ma kula da shi ko ba mu san da shi ba. Sai ya zama mu burin mu mu zo mu sayar da kyaun fuskar mu da kyaun jikin mu a saka mu a fim mu yi kuɗi mu samu ɗaukaka, kuma daga lokacin mu ya wuce an daina yayin mu, wata ta zo ana yayin ta, sai kuma mace ta shiga cikin wani irin yanayi, ko ta fara shaye-shaye, ko ta dawo ci da sha ma ya gagara, har ma ta kai duk inda ta je ma ana korar ta saboda ba ta da wani amfani, lokacin ta ya wuce don ba ta da wata damar da za ta bai wa harkar fim ɗin kariya. Lokacin ki ya ƙare. Amma mazan za ka ga sun ɗauki tsawon lokaci a matsayin masu gudanar da rayuwar su a cikin harkar fim, ko mutum ya kasance a matsayin furodusa ko darakta ko mai ɗaukar hoto da sauran su, kuma za a daɗe ana damawa da su. Ga su nan da yawa da muka sani a yanzu sun yi kuɗi sun zama furodusa ɗin kan su, har ma ‘ya’yan su sun gaje su.
Amma mu mata, sai ka ga mace ta yi aure daga nan matsayin ta a jaruma ya ƙare. To me mace za ta iya yi bayan ta yi aure a cikin harkar fim? Don za ka ga yawancin auren ma da muke yi na sha’awa ne ake yi mana. Namiji ne zai aure mu ba don wai yana son mu tsakani da Allah da Annabi ba, sai don samun wata biyan buƙatar sa. Wanda kuma daga kin yi auren za ki shiga wani irin yanayi na ƙuncin rayuwa. Domin mu mata muna da taushin zuciya wadda ko da mutum ya zo mana da mummunan hali ba za mu gane ba, tunda mun ɗauki zuciyar mu da soyayyar mu mun ba shi, sai mu rinƙa kallon kamar shi ma haka yake yi mana.
Ko kuma ka ga ‘yar fim ta yi aure ta shiga cikin wani irin garari, saboda ta saba ta yi aiki ta samu kuɗi kuma ta yi aure a yanzu ba ta aikin komai don haka babu inda kuɗi zai shigo mata, kuma babu mamaki mijin da ta aura ba mai ƙarfi ba ne. Irin wannan sai ka ga aure ya mutu!
To wannan dalilin ne ya sa na yi ƙoƙarin na nemi na samu ganin shi Babban Darakta na NITDA, kuma sai aka yi sa’a aka ba ni lokaci muka je da ni da wata ƙawa ta, na bayar da duk wasu bayanai na da kuma buƙatar da muke da ita a masana’antar Kannywood, na yi musu bayani a kan yadda mu mata muke buƙatar taimako a masana’antar Kannywood domin ceto rayuwar mu daga mamayar da maza suka yi mana, wanda a dalilin wannan mamayar da maza suka yi mana za ka ji yarinya ta na cewa da ta zo an kai ta wajen wane ya je ya ce zai kwana da ita. To irin wannan mamayar da maza suka yi ne yake kawo hakan, saboda mata ba su da ƙarfin da maza suke da shi.
Yanzu da na fara furodusin har na fara samar da manyan jarumai, kuma a yanzu kusan kullum sai mata sun kira ni a kan suna son ‘ya’yan su su shigo harkar fim amma suna son su shigo ta hannu na saboda ni mace ce ‘yar’uwar su kuma babu abin da zan yi na illata rayuwar su, don dole su bi dokoki na yadda za su yi komai cikin sauƙi, don za ka ga wasu da gaggawar su suke zuwa su kai ga buƙatar su, ba sa son jira.
To, duk irin wannan bayani na yi musu kuma suka ga muhimmancin abin da nake da burin yi, don haka suka ce na zo na rubuta duk abubuwan da nake buƙata wanda ni ma zan zama wata a cikin harkar fim ɗin domin a samu a ɗaga darajar mata a Kannywood a kan mataki na ci gaban zamani.
Duk da harkar gwamnati ce mun ɗauki tsawon wata biyar muna cike-ciken takardu da bibiya, har lokacin da muka yi nasara aka kira ni aka ce kaya na ya iso kuma za a kawo shi Kano.
Alhamdu lillah, kaya ya zo, kuma duk wani abu da na rubuta muna buƙatar sa an ba mu. A yanzu muna so mu samar da babban waje da zai zama wajen gudanar da aikin, saboda wajen da muka tanada kafin zuwan kayan sai da kayan ya zo muka ga wajen ya yi kaɗan, don haka saboda yanayin tsaro dole ta sa za mu sauya waje.
Kuma duk kayan da suka ba mu su ne dai wanda ake aiki da su a yanzu a duniya, babu wani tsoho. Kayayyakin duk wani aikin da za a yi a masana’antar Kannywood da akwai shi a ciki – tun daga kyamara, kwamfuta, da duk wani abu da ake amfani da shi a harkar fim ta duniya. Gaskiya an yi niyyar a tallafa wa harkar fim ɗin Kannywood don ɗaukaka darajar mata don su ma su samu sana’ar su ta kan su ba wai aktin kawai ba.

FIM: Ta wace hanya matan Kannywood za su ci moriyar wannan tallafin?
MANSURAH: To, mun shirya samar da aikin yi ga mata da kuma wayar musu da kai, mu nuna musu cewa a matsayin su na matan Kannywood akwai hanyoyin dogaro da kai ga mace ko da ta yi aure wadda a yanzu mun samar da wasu ƙwararru da za su bayar da horo a kan hakan. Don haka za a rinƙa horas da mata da matasa, ba wai mata kaɗai ba, su ma matasa za mu horas da su ta yadda su ma za su samu hanyar dogaro da kai.
Don haka muna albishir ga duk wata mace da take son ta koyi wani abu na kasuwancin zamani da sana’a a cikin harkar fim ta fannin soshiyal midiya kamar YouTube, Instagram da sauran manhajoji da suke samar da kuɗi ba tare da mace ta fita daga cikin gidan ta ba. Sannan ya za ta koyi harkar tacewa da kuma sarrafa hotunan fim ta yadda tana zaune a cikin gidan ta za a rinƙa kawo mata.
Kuma ka ga muna da ƙarancin mata a ɓangaren tace finafinai, don haka ake ganin kamar duk harkar maza ce, kuma su maza ba su cika mayar da hankali kan abin ba, don ko ni akwai fim ɗin da sai asarar sa na yi a wajen waɗanda na bai wa aikin, saboda ba su da wani takamaiman wajen zama. Don haka za mu yi amfani da wannan kaya wajen magance irin waɗannan matsaloli.
FIM: Wannan harkar bayan kayan da kuka samu tana buƙatar kuɗin tafiyar da ita. Ko akwai wani tsari da kuka yi na samun kuɗaɗen gudanar da ita?
MANSURAH: E to, muna ta ƙoƙarin samar da hanyoyin, amma dai a yanzu abin da yake hannun mu da shi za mu fara. Kamar yadda muka yi ƙoƙarin samun kayan haka ma kuɗin gudanarwa za mu nema kafin zuwa lokacin da wajen zai iya riƙe kan sa. Duk da dai mun ce yawancin abubuwan da za mu rinƙa koyarwa a wajen kyauta ne, amma za mu yi ƙoƙarin samar da hanyar da wajen zai iya riƙe kan sa yadda za mu rinƙa biyan ma’aurata da sauran ayyukan gudanarwa na yau da kullum.

FIM: Kamar yadda kika ce, duk wata mace idan ta shigo harkar fim burin ta shi ne ta zama jaruma. Ko wace hanyar za ku bi wajen nuna masu cewa ba aktin kawai ba ne sana’a a cikin harkar fim?
MANSURAH: To, na farko dai ina jin a cikin sa’anni na da muka shigo harkar fim, ina ga kusan ni ce a cikin harkar fim ɗin. Gaba ɗayan rayuwa ta ban fita ba har yanzu kuma mata suna kallo na suna alfahari da ni saboda suna na na Mansurah Isah bai ɓaci ba. Tun da na shigo harkar babu wani darakta ko furodusa da nake bi don ya samo mini wata hanya. Duk da a yanzu ba wani fim nake yi ba, ko da idan ta ɗauro nan gaba za a gan ni a cikin fim ana gani na da mutunci saboda ni nake nemowa na yi da kai na.
Don haka mata su sani, idan babu aktin akwai zama furodusa ko darakta ko ɗaukar hoto da dai sauran su. Don haka ba sai da aktin kawai za a samu kuɗi ko ɗaukaka a cikin harkar fim ba, domin harkar tana da faɗi sosai.
Yanzu idan za a yi fim sai ka ga mutanen da za a ɗauko sun ninka jaruman da za su fito a cikin fim ɗin sau uku ko sau huɗu, don sai ka yi fim da jarumai ashirin, amma sai ka ga ma’aikatan sun fi hamsin, tun daga kan masu rubutun labari har zuwa masu tace hotunan fim ɗin idan an kammala har zuwa tallar fim ɗin da kuma sakin sa a kasuwa.
To amma me ya sa mu mata za mu tattara mu ce sai aktin kawai? Wannan ba daidai ba ne kuma za mu yi iya yin mu wajen wayar da kan mata a kan wannan tunanin da suke da shi.
FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
MANSURAH: Saƙo na na ƙarshe ina so na yi amfani da wannan dama wajen isar da saƙo na ga National Information Technology Development Agency (NITDA) a kan yadda suka taimaka wa masana’antar Kannywood a matsayi na na mace da suka ba ni wannan tallafin don ganin masana’antar Kannywood ta amfana kuma ina mai tabbatar da cewa za mu yi amfani da wannan dama da muka samu wajen ciyar da masana’antar Kannywood gaba. Mun gode, muna ƙara godiya sosai.
Kuma in-sha Allah za mu ci gaba da wayar da kan mata a kan fasahar cigaban zamani da kuma koyar da su yadda su ma za su zama abin alfahari, ba wai kawai su tsaya a matsayin aktin kawai ba, wanda daga lokacin da aka daina yayin su kuma rayuwar ta tsaya kenan.
FIM: To madalla, mun gode.
MANSURAH: Ni ma na gode sosai.