Taƙaitaccen jawabin da Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya gabatar a taron da Gidauniyar Hudaibiyya ta shirya a Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, Kano, a ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2019
GODIYAR gayyata zuwa ga Hudaibiyya Foundation, da fatan Allah ya albarkaci niyya da abubuwan da za a gudanar.
Ina yabon basirar yin amfani da wannan rana domin warware ƙasar mu don mu fahimci inda ta fito, inda ta sa gaba, da matsalolin ta da kuma hanyoyin da za a bi a yi maganin su. Na yi farin cikin ganin cincirindon matasa a wajen taron, domin babu abin da ya fi muhimmanci yanzu a ƙasar mu, musanman ma a Arewa, kamar reno da tarbiyyar matasa domin su yi amfani da basira da sani da sauran albarkar da Allah ya ba manyan su masu kishin ƙasa.
Lallai wannan Gidauniya ta yi ƙoƙari haɗa sanannu da masu abin faɗi a kan halin da ƙasar mu ke ciki, kuma ina godiya da aka sa ni a jerin waɗannan fitattun jama’a.
Matsalolin Nijeriya su na da tushe mai zurfi, kuma ba zai yiwu a fahimce su ba sai an gane wannan tushe da irin abin da ya haifa mana. Nijeriya dai ƙasa ce da Turawa su ka ƙwata, su ka gina ta ta hanyoyin da su ka yi daidai da buƙatun su, sannan su ka shirya tsarin ci-gaban wannan shiri ta hanyar tafiyar da mulki da siyasa da kuma tattalin arziki. Wannan tsarin shi ne su ka ƙaƙaba mana, kuma su ka tabbatar ko bayan su ba za mu kauce masu ba.
Waɗannan tsare-tsare ba su da alaƙa da addinan mu da ɗabi’un mu da su ka same mu da su, musanman ma mu Musulmi waɗanda addinin mu ya na nuna muhimmancin haɗa kai da maslaha a dukkan harkokin da su ka shafi jama’a.
Shi kuwa tsarin dimokiraɗiyya an kafa shi ne a ginshiƙin rabuwar jama’a tsakanin talaka da mai arziki, ko tsakanin waɗansu bambance-bambance waɗanda ba a iya maganin su sai an yi hamayya da tsari da zai ƙara ƙarfafa waɗannan rabe-rabe. Tun da aka kafa Nijeriya, ba a yi mata gyara ko wani bibiya mai inganci ba, in ban da ‘yan kintse-kintse da sojoji su ka yi ta yi idan sun ga matsalolin da mulkin su ya jawo.
Tarukan ‘yan siyasa da masana da a kan kira da sunan gyara tsari da ingancin ƙasa ba a ba su muhimmanci, ko kuma sai su zama wata hanyar yaudarar ‘yan Nijeriya ne domin samun biyan buƙatun shugabanni kawai. Sabili da haka sai ƙasa ta zama kamar gidan da aka bar shi ba a duba ginshiƙin sa, ba a yaɓe, ba a duba rufi, ba a tada katanga idan ta rushe, ba a gyara ƙofa ko taga idan sun karye, ba a duba lafiyar mutanen cikin gida, sannan kullum ana faɗa a kan wanene ke da cancanta da haƙƙin shugabancin gida.
Matsalolin da tsarin mulki waɗanda ba su da tushe a addinan mu da al’adun mu su ka haifar da matsaloli da yawa, waɗanda kaɗan daga ciki su ka haɗa da:
i) Mulki ya zama na mai abin saye, ko mayaudari ko na mai ƙarfin haɗa faɗa shi kuma ya gaji ɓarna;
ii) Yawanci shugabannin da ke samun muƙamai ta hanyar siyasa ba su cancanta ba ta hanyar sani, hali da ƙwarewa ko alamar riƙon gaskiya da amana;
iii) Jama’a da ya kamata su zama masu zaɓe da zaɓen shugabanni sun koma ‘yan rakiyar ɓarna ko ‘yan sa ido ko kuma sun ɓuge da Allah ya isa. Zaɓe ya zama kamar yaƙi, sai mai ƙarfi zai yi nasara, sannan sai ya bar ɓarna da taɓo da za su daɗe ba a samu maganin su ba.
iv) Waɗanda Allah ya ɗora wa nauyin shugabanci kamar sarakuna, malamai da masu sani da ilmi da masu arziki an sa masu takunkumi, ko sun sa wa kan su, sun zama ‘yan raka ɓarna. Su na mantawa da ranar da Allah zai tsaida su gaban sa ya tambaye su irin abin da su ka yi da iko, ko sani ko dukiyar da ya ba su.
Masana da masu ilmi sun yi gum saboda kwaɗayin abin da za su samu wajen ‘yan siyasa ko wajen aikin neman duniya. Sarakuna da jama’a su ke darajawa su na tsoron ‘yan siyasa, duk kuwa da cewa da yawan su sun fi ‘yan siyasar sanin hanyoyin mulki da tausayin talaka.
Masu arziki sun zama ɗaya da talaka, kowa ya tsuguna gaban shugabannin siyasa ya na jiran sallama.
v) Mun manta da muhimmancin gyara kan mu, da jajircewa sai shugabanni sun zama adilai da masu riƙon amana, sannan za mu yi masu biyayya ko kuma mu yi watsi da su idan dama ta zo.
vi) Zukatan mu sun mutu, mun koma mun raja’a mu na maula ko jiran ‘yan siyasa ko gwamnati ta nema mana mafita.
vii) Mulki ya zama tamkar direban da ke jan mota cike da fasinjoji, su na ta kukan motar da direban su na da matsaloli, amma shi direba ya na tafiya yadda ya ke so, ya na gaya masu ba matsala, kuma kada su dame shi.
Ina bada shawara a ɗauki waɗannan matakan:
i) A fito da sabon tsarin tsaro wanda zai kare jama’a daga munanan halayen da rashin tsaro ya sa su. Ya kamata Shugaban Ƙasa Buhari da gwamnoni su riƙa zagayawa su na ganin irin halin da jama’a ke ciki, domin idan talaka ya gaji da gudu daga masu hana shi ya zauna lafiya da talaucin sa, to shugabanni ma ba za su zauna lafiya ba.
ii) Idan kamar yadda ake cewa Shugaba Buhari mai gaskiya ne, to sai ya ƙara ɗamara ya yi yaƙi da rashin gaskiya, daga wacce ta ke kusa da shi har zuwa wacce ke nesa.
Akwai mummunar alaƙa tsakanin cin haram da ake wa dukiyar mutane da talauci da rashin tsaro wanda har yanzu shugabanni ba su fahimce ta ba. Babu ɓarnar da kan lalata zamantakewar jama’a kamar rashin adalci, kuma babu rashin adalcin da ya fi kasa tsare wa jama’a haƙƙin su ba.
iii) A ƙara ƙoƙarin gyara hanyoyin da za su tabbatar da cewa waɗanda su ka yi nasara a zaɓe su ne mu ka zaɓa. Satar da ta fin ɓarna a ƙasa ita ce satar mulki, domin ta na haifar da ƙiyayya tsakanin shugaba da jama’a da fitintinu waɗanda ke raba kan jama’a da ƙara haɓaka rashin biyayya da karya doka da satar dukiyar jama’a.
iv) Lokaci ya yi da za a ƙara duba yanayi, tsari da kamannin ƙasar Najeriya. Akwai matsaloli da yawa game da yadda ake tafiyar da ƙasar mu, kuma ko wane sashi ya na da nasa koke-koken a kan waɗansu matsalolin da su ke alaƙa da yadda tsarin ƙasa ya ke. Shugabanni su daina gaya wa jama’a cewa babu matsala ko tababa game da dauwamar Nijeriya ko ci-gaban matsalolin da su ka addabe ta saboda rashin gyara.
v) Ƙasar nan na buƙatar shugabanni masu tsoron Allah, waɗanda su ka san mulki, kuma masu riƙon amana. Ko a ina su ke, ya kamata su fito, jama’a kuma su fifita su a kan ‘yan siyasar da ba su da niyyar wani abu sai dai su samu biyan buƙatar su, su bar talaka cikin uƙuba.
Mu dai a Arewa an sha mu mun warke! Mun zaɓi shugabanni ‘yan Kudu an tafi an bar mu a tsugune. Mun zaɓi ‘yan Arewa sun bar mu cikin wahalhalu da ba mu taɓa shiga cikin su ba.
Ya kamata mu buɗe idon mu. Daga yanzu wanda kawai za mu zaɓa sai wanda mu ka gamsu ya na da niyya, kuma ya san yadda zai kawo mana ingantaccen tsaro da tattalin arziki, ya taimaki matasan mu su samu abin yi, sannan ya taimaka wa ‘yan Nijeriya kowa ya san ɗakin uwar sa ba da faɗa ba.
Na gode.
Dakta Baba-Ahmed ɗan siyasa ne kuma tsohon babban jami’in Gwamnatin Tarayya