• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, November 1, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Abdul D. One: Ba zan taɓa yafe wa Sa’adatu Marana ba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 4, 2019
in Labarai
0
Sa'adatu Marana da Abdul D. One a cikin raɓar soyayya

Sa'adatu Marana da Abdul D. One a cikin raɓar soyayya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FITACCEN mawaƙi Abdul D. One ya bayyana cewa ba Ali Nuhu ne ya hana shi ya auri jaruma Sa’adatu Abubakar Marana, kuma duk maganganun da ta ke yi a kan sa a soshiyal midiya yunƙuri ne na ta ɓata masa suna, amma shi bai san da su ba. 
 
Ya ce kuma maganar da ta yi na cewa wai ya biya sadakin ta, bai san da ita ba. 
 
Haka kuma ya yi mata Allah-ya-isa, ya na faɗin ba zai taɓa yafe mata ba.
 
Idan kun tuna, a mujallar Fim ta Nuwamba 2018 mun ba ku labarin tsananin soyayyar da mawaƙin mazaunin Kaduna da jarumar ‘yar ƙasar Nijar su ke yi, wadda har ta fito a sarari. 
 
Kowa ya san yadda jarumar ta ke matuƙar son Abdul, domin kusan duk lokacin da za ta yi ɗora hoto a shafin ta na Instagram, hotunan sa ta ke sakawa da kalamai masu sanyaya zuciya. Saboda irin ƙaunar da ke tsakanin su har suna jarumar ta ƙirƙira wanda ta ke kiran Abdul da shi; sunan ta haɗa shi ne da harufan farko na sunan ta da kuma haruffan farko na sunan sa, wannan haɗi ya bada  ‘SA’AB’, wannan shi ne sunan da ta ke kiran sa. 
 
Ko a ranar zagayowar ranar haihuwar Abdul, duk wanda ya ɗora hoton sa ya taya shi murna, za ta bi ƙasan hoton ta rubuta “mun gode”. 
 
Mujallar Fim ta gano cewa soyayyar tasu ta yi nisa, har maganar ta kai gun magabata, an fara maganar aure. 
 
To amma kwatsam sai wasan ya yi tsami tsakanin matasan biyu, aka wayi gari aka ga Sa’adatu na yin rubutu mai zafi na cin fuska ga wani wanda ba a daɗe ba aka gane cewar Abdul ɗin ne.  
 
A rubutun farko da Sa’adatun ta yi kan lamarin a shafin ta na Instagram, cewa ta yi, “Sa’adatu Abubakar Abdullahi SAAB, AKA Marana. Sau ɗaya na ke yi tak, ban taɓa yi sau 2 ba, don ba na maimaita aji. Ina jin saƙonnin ka, ka jira nawa.” 
 
Ta cigaba da rubutu kamar haka: “Mai kwaɗayi!!! Maciyin amana!!! Mayaudari!!! Mai sharri!!! Mai ƙarya!!! Mai zamba cikin aminci!!! Mai haɗa ɗa da iyaye!!! Mai munafurci!!! Mai fuska biyu!!! Mai roƙo!!! Mai hadassa fitina!!! Makiri!!! Mai zalunci!!! Mai mugunta!!! Mai take alheri ya maida shi sharri!!! Mai maida saɓon Allah ado!!! Mai borin kunya!!! Mai ganin zai yi ma Allah  wayau!!! Mai gulma!!! Mai iƙirarin shi babban sheɗani ne!!! Shin irin wannan mutumin ya kamata a ɗaga masa ƙafa???” 
 
A wani rubutun kuma ta ce, “Ka ci kuɗin mace ta zama abar zagi  wajen ka??? Ka tara abokan ka ku na zagin ta a office ɗin da kuɗin ta ne a ciki??? Har ka je mai siyar da kaya ka na zagin ta, shin kai bakin ka ba shi da linzami ne? Wanda ya maka rana shi ne abin zagi a wurin ka? 
 
“Ka nuna min kai abin tausayi, saboda kowa ya na maka baƙin ciki, yanzu ma da ƙyar ne Allah Ya taimaka aka fara ba ka aiki. Ashe kai ne azzalumin kan ka. Allah Ya isa da haƙƙin ‘yan matan da ka yaudara ka na tunanin shi ne zai bar ka ka ci gaba? Ai idan ka ga ka ci gaba ka fi yadda ka ke yanzu to ka ji tsoron ƙarshen ka, don ba zai yi kyau ba wallahi. Haƙƙin wani ba kyau a kan ka balle na wasu. Ko ba ka ga yadda abokan ka su ke ci gaba ba? Ko kuma an faɗa maka wannan rayuwar ce su ka saka a gaba? An faɗa maka da abin hannun mata ne su ka dogara? 
 
“Sai ilimin zagin mutane bayan kai ne abin zagin. Dan Allah, dan Annabi a biya ni bashi na kafin na zo office ɗin na cire abin da na san nawa ne. Ko da yake ma sun tsufa, sabbi na ke buƙata ko kuɗin malam mai zuciyar kwaɗayi da cin mutuncin wadda ya masa rana ga yi wa mutane sharri kai kam abin ya maka yawa Wallahi. Ya kamata ka tuba haka nan, amma shawara ne.” 
 
Haka dai ta ci gaba da waɗannan rubuce-rubuce, wanda dukkan rubutun nata ya na nuni da cewa ya yaudare ta ne. A wasu daga cikin rubutun da ta yi akwai inda ta nuna ya gama lalata yaran mutane, ya yaudari ‘ya’yan mutane sun fi a ƙirga, amma a haka ya ke neman Allah Ya ba shi mata tagari. 
 
A yadda waɗannan masoya suke, babu wanda ya yi tsammanin haka zai faru tsakanin su. 
 
Ganin rubutun ta ya sa jama’a su ka yi wa jarumar caa, wasu na ba ta haƙuri, wasu kuma su na faɗin bai kyauta ba. Ita kuwa ko a jikin ta, ta ci gaba da irin waɗannan rubuce-rubucen. 
 
Da mujallar Fim ta tambayi Abdul D. One game da rubuce-rubucen na Sa’adatu, sai ya ce, “To, ni iya abin da zan iya cewa, za ka iya alaƙa da mutum ba dole sai soyayya ba. Shi kuma mutum zai iya neman soyayyar, in Allah bai ba shi ba babu abin da ba zai iya faɗi a kan ka ba. 
 
“A iya sani na dai, komai mu ƙaddari ne daga Allah, sannan duk wanda ya yi imani da Allah shi ke yarda da ƙaddara. Kuma duk mutumin da ke so ya yi rayuwa da kai babu abin da ba zai iya faɗi a kan ka ba. 
 
“Amma maganar sadaki ni ban san da shi ba. Maganar kayan ofis ɗi na da ta ke yi duk ban san da shi ba. Hasali ma, maganganun da ta ke yi ni ban san ta na yi ba. Saboda abin da ke faruwa, duk mai neman ka da sharri, kai kuma sai ka neme shi da alheri. Haka Manzon Allah SAW ya ce. 
 
“Ba na neman ta da sharri, Allah Ya sani. Sannan duk abin da za ta yi, sai Allah Ya so, kuma Ya nufa. Abin da mutane su ka kasa ganewa, duk wanda Allah Ya kafa shi, duk iya yunƙurin ka ba ka isa ka ture shi ba. Wannan abu ya kasance ɓata suna ne da maganganun banza waɗanda su ka fito daga bakin ta. 
 
“Gaskiya ban san komai da ta ke magana ba. Kawai dai ta na amfani da wani dama nata ne, don ta na ganin kamar an san ni da ita, ni kuma ban ma san akwai wanda ya san ni da ita ba. 
 
Ya ce ko hotunan da ake ganin shi tare da ita, duk haɗi ne na komfuta. Ya ce, “Don a ce an ga hoton ka da wani, hoto ana iya yankawa a haɗa. A waya ma ana haɗa hoto ka ga mutum kamar da ma ya na wurin. Don haka duk maganganun da Sa’adatu ta ke yi, ni ban san da wannan magana ba. Hasali ma zan iya cewa na bar ta da Allah.” 
 
Wakilin mu ya tambayi Abdul gaskiyar abin da wasu ke faɗi cewa Ali Nuhu ne ya hana ya auri Sa’adatu, sai ya ce, “Gaskiyar magana Ali Nuhu babu ruwan sa a cikin wannan magana. Hasali ma Sa’adatu ita ke bibiyar shi, ta na zuwa har gidan sa. Ali Nuhu ba zai ce Abdul D. One dole sai ya auri Sa’adatu ba. Ali Nuhu ba shi ya haifi Abdul D. One ba. Hasali ma Ali Nuhu ya zama tamkar uba ne a wannan masana’anta. Amma ko uba mahaifi ba zai tursasa wa yaron sa ya auri wani abu wanda ba ya so ba.” 
 
Abdul ya ce don me zai auri jahila? A cewar sa, “Ana gina aure ne ta hanyar sunnar Manzo Allah SAW. Idan ba ka gina aure ta sunnar Manzon Allah ba, ba za ka taɓa samun zuri’a nagari ba. Kuma za ka yi aure cikin tashin hankali? Za ka auri mata mara ilimi ne? Wannan ba zai yiwu ba. 
 
“Manzon Allah ya ce mu auri mata mai ilimi. Ka auri mata mara ilimi, kai ka san ka kira ruwa. Don haka maganar Ali Nuhu ya yi kaza duk ƙarya ne. Ba ruwan Ali Nuhu a cikin lamarin auren Sa’adatu, ta na iya auren duk wanda ta ke so. Sannan aure ana yin shi da soyayya ne. Babu ruwan Ali Nuhu. Kuma wannan maganar ma ita ta ke faɗa, ba wani ya ke faɗi ba.” 
 
Ya sha alwashin ba zai maka ta a kotu ba saboda ɓata masa suna da ta yi. 
 
“Ba kuma zan ɗauki mataki a kan ɓata min suna da ta yi ba,” inji shi. “Duk wani mataki bai wuce na Allah ba. Allah Shi kaɗai zai yi maganin wannan al’amarin.” 
 
Abdul ya ce Sa’adatu ba ta isa ta sa ya aure ta a dole ba. Ya ce, “Duk yunƙurin ta da tada jijiyoyin wuyan ta ba ta isa ta yi abin da Allah bai yi ba. Kuma tunda ta fi ƙarfin iyayen ta, ba su isa su hana ta ba, ta bijire masu, ai sai a bar ta da Allah.” 
 
Ɗaya daga cikin zargin da Sa’adatu ta yi wa Abdul shi ne wai ya yaudari wata yarinya ya ɗirka mata cikin shege. A kan wannan, mawaƙin ya ce, “Maganar na yi wa wata ciki, wallahi ban san da wannan maganar ba. Hasali ma ta na daga cikin waɗanda su ka bada gudunmawa na yaɗa wannan abu a soshiyal midiya. Kuma Allah Ya isa ban yafe mata ba!” 
 
“Kuma Sa’adatu ba ni kaɗai za ta iya yi wa wannan abin ba. Kowa ta na iya yi wa, domin ta yi wa wasu a baya,” inji Abdul.

Loading

Previous Post

Mu dai a Arewa an sha mu mun warke!

Next Post

Ado Gwanja ya samu Asiya (Balarabiya)

Related Posts

Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja
Labarai

Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja

October 24, 2026
Zaɓen 2027: Gidan Dabino, Rarara, Abdul Amart da wasu ’yan Kannywood 14 sun shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano
Siyasa

Zaɓen 2027: Gidan Dabino, Rarara, Abdul Amart da wasu ’yan Kannywood 14 sun shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Abba da Tinubu a Kano

October 24, 2026
Gwamnatin Kano ta naɗa tsohuwar jarumar Kannywood Halisa Muhammad jakadiyar waɗanda suka tsira daga sankarar mama
Labarai

Gwamnatin Kano ta naɗa tsohuwar jarumar Kannywood Halisa Muhammad jakadiyar waɗanda suka tsira daga sankarar mama

October 23, 2026
Maikatanga ya shiga kwamitin alƙalan gasar Wole Soyinka ta aikin jaridar bincike
Labarai

Maikatanga ya shiga kwamitin alƙalan gasar Wole Soyinka ta aikin jaridar bincike

October 19, 2026
Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Next Post
Zahraddeen Sani

'Ko uwa ta ba ta isa ta sa in sasanta da Zahraddeen Sani ba'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!