ABUBUWA biyu masu daɗi sun faru ga fitaccen jarumi Tukur S. Tukur (Ɗandugaji) kwanan nan: na farko ya cika shekara 50 da haihuwa, na biyu kuma an tabbatar masa da muƙamin shugaban sashen kula da kafafen sadarwa (ICT) na babban filin jirgin sama na Malam Aminu (MAKIA) da ke Kano.
Kafin wannan tabatarwar, jarumin ya kwashe shekara ɗaya da watanni a matsayin muƙaddashin shugaban sashen.
Hukumar kula da filayen jirage ta Nijeriya (FAAN) ta tabbatar masa da muƙamin a ranar 13 ga Maris, 2021.
Ɗandugaji na ɗaya daga cikin sanannun jarumai a ɓangaren barkwanci a Kannywood, kuma jigajigai wajen assasa wannan masana’anta.
A hirar sa da mujallar Fim, jarumin ya kuma bayyana cewa yanzu haka ya dawo harkar fim gadan-gadan.
Ɗandugaji, wanda ya gode wa Allah da ya ba shi damar cika shekara 50 a duniya, ya faɗi abin da wasu su ka ce da aka ba shi wannan muƙami.
Ya ce, “Gaskiya na tsorata matuƙa bisa wannan nauyin da aka ɗora min a matsayin wanda zai jagoranci wani sashe da ke filin jirgi, to amma duk da cewa mutane da dama sun sha faɗin cewa ya za a yi a ɗauki ɗan fim ɗin barkwanci a ba shi wannan muƙamin, su na ganin kamar ba zan iya ba, sai kuma ga shi Allah ya yi dole ni zan jagoranci wurin.

“Kamar yadda na samu takardar tabbatarwa daga hukumar kula da filayen jirgi ta Nijeriya, wanda a cikin ta su ka tabbatar mani da hakan, bayan na shafe kusan shekaru 18 ina aiki tun ina a matsayin mai aikin wucin-gadi, wato ‘casual’ a turance, daga baya kuma na zama cikakken ma’aikaci, na kuma samu goyon baya na ga soyayya da fatan alkairi daga cikin ma’aikata da ‘yan’uwa da abokanan arziki wanda da man idan lokaci irin wannan ya zo dole sai ka gamu da ƙalubale in dai a kan shugabanci ne.”
Ɗan wasan ya ƙara da cewa, “Shi wannan ƙarin girma da na samu ya zo ne a daidai lokacin da saura wata ɗaya da kwana biyar in cika shekara hamsin cif cif a duniya a ranar 18 ga Afrilu, 2021. An haife ni a 1971, ka ga shekara hamsin, to mai shekaru irin wannan a zamanin nan ba wasa ba ne don duk mutumin da aka ce ya shekara hamsin a duniya ya zama dattijo babu kuma wani mulki da ba zai iya riƙewa ba, babu kuma wata magana da ba zai iya shanyewa ba.
“Saboda haka wannan mulki ya zo min a shekarun dattijontaka, duk da cewar jiki na da yanayi na bai wuce ka kalle ni ka ce min ban wuce shekaru irin 35 ba zuwa 40 saboda yanayin irin ƙirar da Ubangiji ya yi mani, to amma dai shekarun su na da yawa; shekara 50 ba wasa ba ne; duk wani cikar hankali a yanzu ta zo wa mutum kuma duk wata martabawa da za a yi wa mutum don shekarun sa ba a min ba don shekaru na sun kai.
“Yanzu ba abin da zan iya cewa sai dai fatan nasara da gamawa lafiya domin yanzu ni na zama matashin dattijo. Ga yara a ƙarƙashi na, ga kuma iyalai da dama da na ke kula da su.”
A game da harkar fim kuma, tsohon jarumin ya ce, “Ni da man ban daina fitowa a finafinai ba kamar yadda a kwanakin baya na gaya wa wannan mujallar, domin kuwa ba zan ce na daina fim ba sai dai ni akwai yadda na ɗauki fim wanda ba sai na maimaita ba. Idan Allah ya sa an kirawo ni ina zaune, zan je na yi fim.
“Kuma da man ai tsarawa za a yi matuƙar bai taɓa yanayin aiki na ba, idan kuma ya taɓa yanayin aiki na ba zan bar aiki na in zo in yi fim ba. Duk wanda za mu yi harkar fim zan gaya masa yanayin lokutan da na ke da su, idan ya ga zai iya to, in kuma ba zai iya ba ka ga dai na gaya masa lokuta na sun fi zuwa ranar ƙarshen mako duk da ita ma ɗin wani lokacin mu na aiki amma zan san yadda zan yi na zo na yi wa wanda ya gayyace ni aiki.”
Wani ƙarin albishir daga jarumin zuwa ga masoyan sa shi ne: “A watan Fabrairu da ya gabata na 2021 na samu gayyata har guri uku inda na yi finafinai guda uku masu dogon zango wanda ɗaya za a riƙa haska shi a gidan talbijin na Arewa24, ɗaya kuma a Tauraruwa TV, na ƙarshen shi har yanzu ba a sa inda za a haska shi ba. Kuma in Allah ya yarda mutane za su ga irin rawar ganin da na taka wanda ba sai na faɗa ba, su da kan su za su yi alƙalanci, kuma a nan ne za su gane cewa har yanzu Ɗandugaji ya na nan bai mutu ba a harkar fim.”
A ƙarshe, Ɗandugaji ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da taya su da addu’a tare da yi musu fatan alkairi da kyautata zato a gare su da kuma a riƙe juna a matsayin ‘yan’uwa.
Ya ce babu shakka dole a rayuwa saɓa ni zai iya shiga tsakanin ka da wani, “sai mun zama masu yafiya da juna tunda wata rana duniyar nan yadda aka yi hirar nan da ni wata ran sai ka yi hira da wani nawa a kan mutuwa ta, ka ga kenan kowa zai mutu.
“Jan hankili na kawai mu zama masu yafiya, mu zama masu juriya da junan mu, mu kuma zama masu riƙe alƙawari.”