SUNAN ta Bilkisu Salisu. ‘Yar kimanin shekaru 11 a duniya, ita ce ta fito a matsayin Amira a cikin shirin talbijin mai dogon zango, wato ‘Sirrin Ɓoye’. Manyan jaruman Kannywood ne a cikin wannan shiri, amma ita ce ƙashin bayan labarin, inda ta fito a matsayin wata hatsabibiya wadda idan ta kalli mutum ko za a kashe shi ko kuma zai kashe wani. Kafin iyayen ta da kuma jami’an tsaro su gano bakin zaren rayuka da dama sun salwanta, an kuma shiga bin bokaye da malamai domin warkar da ita daga kamun baƙaƙen aljanu kamar yadda aka yi zargi daga farko.
Jami’an tsaro masu kaifin basira da iya bin diddigi sun shiga matsanancin ruɗani a yayin nemo hanyar bayar da kariya ga waɗanda ta kalla don ceto su daga halaka.
Labari ne mai matuƙar sarƙaƙiya da tayar da hankali da fasihin marubuci Ibrahim Birniwa ya ƙirƙira tare da rubutawa gami da haɗakar zaƙaƙuran matasan marubutan Kannywood.
Ko yaya za a samo sabuwar jaruma mai ƙarancin shekaru da za ta iya hawa wannan babban matsayi na hatsabibiyar yarinya? Mai shirywa, Maje El-Hajeej Hotoro, ya shiga shawagin neman wannan yarinya wacce samun ta na da matuƙar wahala, musamman domin ba kowaɗanne iyaye ne za su ƙyale ‘ya’yan su masu ƙarancin shekaru shiga fim ba, kamar yadda ba kowace yarinya ce za ta iya samar da abin da ake so ba bayan ba ta taɓa yin fim ba.
A ƙarshe, an samu Bilkisu a dalilin wata jaruma, Nafisat Salisu, wacce ta ke jan fim mai dogon zango ‘Macen Sirri’ inda ta gabatar da ƙanwar ta uwa ɗaya uba ɗaya domin gwada sa’ar ta, wanda nan take a wajen gwaji ta samar da abin da ake so.
Bayan tara manyan jaruman Kannywood, Amira ta dake kamar wata tsohuwar jaruma, ta ja wannan babban fim. Shin ko yaya ta ji kafin ɗaukar wannan fim da kuma bayan ɗaukar sa? “A’a ban taɓa yin fim ba sai a kan ‘Sirrin Ɓoye’ wanda kamfanin Sirrinsu Media su ka shirya?”
Ga dai yadda hirar Bilkisu Salisu da mujallar Fim ta kasance:
FIM: Mai karatu zai so ya ji sunan ki da tarihin ki.
BILKISU SALISU: Suna na Bilkisu Salisu, Amira kuma a cikin fim ɗin ‘Sirrin Ɓoye’. An haife ni a watan Maris, a shekarar 2010 a Ƙaramar Hukumar Tarauni da ke Jihar Kano, a unguwar Hotoro Ɗanmarke.
Na kuma fara makarantar firamare a ‘Excellent International School’ duk a Hotoro, har yanzu ban gama ba ina can.
FIM: Ya aka yi ki ka shiga masana’antar Kannywood?
BILKISU SALISU: Na shiga ne ta hanyar yaya ta, lokacin da aka ce a kawo ni na yi fim, wanda kafin ma na fara sai da aka yi mani gwaji, wato ‘audition’, sai aka ga na dace kuma zan iya.
FIM: Ya ki ka ji ranar farko da aka fara sa miki kyamara?
BILKISU SALISU: Kai! Tab, na ji tsoro gaskiya domin kuwa gani na yi ma kamar ba zan iya ba, amma daga baya da aka fara sai na ji tsoron ya gudu. Sannan na yi murna sosai fa, na ji daɗi a rai na, kamar ba ni ba.
FIM: Bayan fara ɗora miki kyamara, wane abu ne ya fi burge ki a cikin fim ɗin?
BILKISU SALISU: Wurin da ya burge ni su na da yawa amma inda aka je gurin Malam aka harbi malamin sannan aka ɗauko ni aka yi gudu, nan ne ya fi burge ni gaskiya don idan na tuno haka a rai na sai in ji daɗi. Sai kuma gurin da aka kai ni makaranta na kalli wani yaro na yanke jiki na faɗi, to nan ma ya na burge ni sosai fa.
FIM: Bayan wannan fim ɗin naki na farko, ki na so ki ci gaba da fitowa a finafinai?
BILKISU SALISU: Ina so da gaske sosai.

FIM: Duba da cewa wannan fim ɗin kin fito kamar wata mayya wanda idan ki ka kalli mutum sai ya mutu ko wani abu mummuna zai same shi, ba kya ganin idan fim ɗin ya fito mutane za su riƙa ɗaukar ki kamar wata mayya?
BILKISU SALISU: Ni ba na wannan tsoron saboda na san cewa wannan fim ne kuma kowa ma ya san fim ne.
FIM: Ba kya ganin yin fim zai iya tsayar miki da karatun ki?
BILKISU SALISU: Ba na tsammanin fim zai iya tsayar da ni, saboda ina karatu ina yin fim ɗin, don ko lokacin da mu ke zuwa lokeshin sai mun tashi daga makaranta sannan sai mu tafi wajen ɗaukar fim ɗin, ka ga kuwa ba yadda za a yi fim ya hana ni yin makaranta ko kuma ya kawo min cikas a karatu na.
FIM: Ko me iyayen ki su ka ce lokacin da za ki fara fim?
BILKISU SALISU: Lokacin da Oga Maje El-Hajeej Hotoro ya kira maman mu ya gaya mata kawai sai ta ce ba damuwa, sannan ni kuma ta ce min in je Allah ya bada sa’a, in dage na yi ƙoƙari.
FIM: A ƙarshe, wane kira za ki yi wa jama’a ko kuma yara ‘yan’uwan ki?
BILKISU SALISU: Ina gaida kowa da kowa, musamman Mama na da Baba na. Sannan ina yi wa Oga na, Maje El-Hajeej Hotoro, fatan alkairi.
Ina kuma kira ga ‘yan’uwa na yara da mu dage mu yi karatu saboda sai da shi ne za ka iya yin komai musamman ta wajen cimma burin sa, mu daina wasa mu kuma bi iyayen mu sau da ƙafa saboda malaman Islamiyyar mu su na cewa duk wanda ya bi iyaye kullum zai dinga samun nasara a rayuwa.
Mujallar Fim ta tambayi Nafisat Salisu a matsayin ta na yaya ga wannan jaruma mai tasowa abin da za ta ce game da wannan ƙanwa tata da ta fito a wannan matsayi.
Sai ta amsa da cewa: “Kusan zan ce ni taimako na ma aka yi kuma na ji daɗi sosai. Kamar yadda na bayyana a kwanakin baya, na sha wahala sosai lokacin da zan shiga Kannywood, to ka ga da ƙanwa ta ta nuna ta na son wannan abin ba zan so ta sha wahalar da ni na sha ba, ga shi kuma ta samu abin cikin sauƙi. Maganar gaskiya, na ji daɗi.”
Fim ɗin dai ya zo da sabon salon labari mai jan hankali gami da ruɗani, wanda a masana’antar Kannywood ba a taɓa samar da irin sa ba, kamar yadda aka yi ƙoƙarin samar da kayan aiki na zamani masu nagarta gami da ƙwararrun ma’aikata. Abin jira a gani shi ne ko yaya ‘yan kallo za su karɓi wannan hatsabibiyar jaruma? Shakka babu, lokaci ne zai tabbatar da hakan.
