A ƘASAR Hausa mun ɗauki fiye da shekara ɗari biyar mu na da tsarin ilimin addinin Musulunci kafin ilimin Nasara ya riske mu. Kafin zuwan karatun boko, karatun allo mu ke yi.
To amma a yanzu sai ka sami mutum Alaramma ko Hafizi ko Gwani ko Gangaran a fannin karatun Alƙur’ani, amma wai gwamnati ba za ta ɗauke shi aiki ba. Amma wanda ya gama sakandare, ko da ya fita da F9 gaba ɗaya a karatun sa, a hukumance sai a ɗauke shi aiki, ya fi wancan gangaran ɗin.
Haka kuma Gwani ko Gangaran bai isa ya yi takarar kansila a garin su ba saboda bai yi karatun sakandare ba.
To ya kamata mu farka, mu riƙa nuna wa ‘yan majalisun mu cewa shi ma wannan karatun ilimi ne. Duk da yake shi ba manufar sa duniya ba, amma dai ya dace a sanya shi a cikin dokokin ƙasa, ko da kuwa a matakin jihohi ne.
Misali:
1. Duk wanda ya yi saukar Alƙur’ani a ce ya gama karatun firamare;
2. Wanda ya haddace izu 30 ya gama karatun sakandare;
3. Wanda ya haddace Alƙur’ani a ce ya yi digirin farko;
4. Wanda ya haddace ya rubuta kuwa, a ce Mastas;
5. Wanda ya rubuta ya haddace da ruwayoyi 5 a ce ya samu Ph.D.;
6. Haddacewa da rubutawa da sanin ulumul Ƙur’an ko tafsirin sa, a ba mutum Farfesa.

Ko wani abu dai makamancin wannan tsarin.
A samar da makarantu da ɗalibai a inganta su domin irin wannan tsarin. Waɗanda kuma su ke da tsangayoyi su ma a tara malaman a faɗakar da su ire-iren waɗannan abubuwa ta hanyar da za su fahimta. Mutum ya zama ya na da zaɓi, in ya ce na boko ya ke so, ya je ya yi, idan na allo zalla zai yi, a ba shi dama. Amma in sun gama darajar su ɗaya.
Wannan bai hana a tsarma nazarin harshen Larabci da na Ingilishi ba.
Haka nan digirin girmamawa da jami’o’i ke bayarwa a fannin adabi, ya kamata su ma ire-iren waɗannan alarammomi a riƙa ba su, ta la’akari da gudunmuwar su a cikin al’umma.
* Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya malami ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Nazarin Harshe a Jami’ar Jihar Kaduna da ke Kaduna
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com
![]()







Gaskiya wan nan sako ne mai muhimmaci, Allah ya isa ga gwamnati duk da dai aikine babba.