• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Karatun boko ko na allo: Mu tashi mu farka

by DAGA SULAIMAN S. MAI BAZAZZAGIYA
September 8, 2021
in Tsokaci
1
Karatun boko ko na allo: Mu tashi mu farka
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A ƘASAR Hausa mun ɗauki fiye da shekara ɗari biyar mu na da tsarin ilimin addinin Musulunci kafin ilimin Nasara ya riske mu. Kafin zuwan karatun boko, karatun allo mu ke yi.  

To amma a yanzu sai ka sami mutum Alaramma ko Hafizi ko Gwani ko Gangaran a fannin karatun  Alƙur’ani, amma wai gwamnati ba za ta ɗauke shi aiki ba. Amma wanda ya gama sakandare, ko da ya fita da F9 gaba ɗaya a karatun sa, a hukumance sai a ɗauke shi aiki, ya fi wancan gangaran ɗin.

 Haka kuma Gwani ko Gangaran bai isa ya yi takarar kansila a garin su ba saboda bai yi karatun sakandare ba. 

To ya kamata mu farka, mu riƙa nuna wa ‘yan majalisun mu cewa shi ma wannan karatun ilimi ne. Duk da yake shi ba manufar sa duniya ba, amma dai ya dace a sanya shi a cikin dokokin ƙasa, ko da kuwa a matakin jihohi ne.

Misali:

1. Duk wanda ya yi saukar Alƙur’ani a ce ya gama karatun firamare;

2. Wanda ya haddace izu 30 ya gama karatun  sakandare; 

3. Wanda ya haddace Alƙur’ani a ce ya yi digirin farko; 

4. Wanda ya haddace ya rubuta kuwa, a ce Mastas;

5. Wanda ya rubuta ya haddace da ruwayoyi 5 a ce ya samu Ph.D.;

6. Haddacewa da rubutawa da sanin ulumul Ƙur’an ko tafsirin sa, a ba mutum Farfesa.

Wani dattijo ya na rubutu a kan allo

Ko wani abu dai makamancin wannan tsarin. 

A samar da makarantu da ɗalibai a inganta su domin irin wannan tsarin. Waɗanda kuma su ke da tsangayoyi su ma a tara malaman a faɗakar da su ire-iren waɗannan abubuwa ta hanyar da za su fahimta. Mutum ya zama ya na da zaɓi, in ya ce na boko ya ke so, ya je ya yi, idan na allo zalla zai yi,  a ba shi dama. Amma in sun gama darajar su ɗaya. 

Wannan bai hana a tsarma nazarin harshen Larabci da na Ingilishi ba. 

Haka nan digirin girmamawa da jami’o’i ke bayarwa a fannin adabi,  ya kamata su ma ire-iren waɗannan alarammomi a riƙa ba su, ta la’akari da gudunmuwar su a cikin al’umma. 

* Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya malami ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Nazarin Harshe a Jami’ar Jihar Kaduna da ke Kaduna


 Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: AlmajiraiIlimiIlimin addiniIlimin NasaraIslamiyyaJami'aKaratun alloKaratun bokoKasar HausaMatakan ilimiTsangaya
Previous Post

Hotunan Adamu Nagudu da iyalin sa tare da fatan alheri

Next Post

Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Comments 1

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    5 years ago

    Gaskiya wan nan sako ne mai muhimmaci, Allah ya isa ga gwamnati duk da dai aikine babba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!