FITACCEN marubuci Maje El-Hajeej Hotoro ya bayyana dalilin sa na fito da abubuwan ban-mamaki a fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Macen Sirri’ wanda ke jan hankalin ‘yan kallo yanzu a YouTube, ya ce wata dabara ce ta isar da saƙo ga jama’a.
Maje, wanda shi ne mamallakin kamfanin Sirrinsu Media da ke Kano, shi ne ya rubuta labarin fim ɗin.
Sabon fim ɗin nasa ya na yunƙurin kafa tarihi a Kannywood domin shi ne na farko a masana’antar shirya finafinan wanda ya haɗa tagwaye sama da biyar a cikin sa.
‘Macen Sirri’ labari ne mai rikitarwa kuma mai kama da almara. Ya na bada labarin wata mace mai suna Sarauniya wadda ke rayuwa a wata duniya daban, wadda kuma ta ke da wani irin shu’umanci har ta kai da ana tunanin mutum ce, aljana ce ko kuma fatalwa.
Matar ta samu wani mutum da ake kira Sarki wanda shi kuma ba abin da ya sa a gaba sai rayuwar bariki, ta shiga rayuwar sa ta samu nasarar tarwatsa ‘yanmatan barikin da su ke tare da shi, ta kuma hana su aikin su na shaiɗancin, ta rikita masu tunani alhali kuma bai san ta ba, bai san ma inda ta ke ba.
Daga baya da ya so sanin wacece ita, bayan ya tabbatar masa da cewa ta daɗe da rasuwa.
A kashi na farkon fim ɗin kenan, wato ‘Season 1’.

Sai dai tun bayan fara haska kashi na farkon a YouTube ‘yan kallo ke ta bayyana ra’ayoyin su, musamman kan yadda fim ɗin ya ƙunshi wasu abubuwan ban-mamaki.
A ranar Alhamis, 17 ga Disamba, 2020 aka ci gaba da ɗaukar fim ɗin, sai dai marubucin ya sauya masa salo ta yadda ya shigo da tagwaye, wato ‘yan biyu, a cikin sa.
Hakan wani sabon abu ne da fim ɗin ya zo da shi a masana’antar.
Mujallar Fim ta halarci lokeshin ɗin ɗaukar shirin inda ta tambayi marubucin saƙon da ya ke son aikawa ga al’umma, shi kuma ya amsa da cewa: “Abin da na ke so na nuna wa duniya ya na da yawa kamar yadda yake da darrussa da yawa, amma shi marubuci ya na da wata hikima ta isar da saƙo.
“Dole na gina labarin ne ta hanyar da zan ja hankalin mutane kamar yanda yanzu ana finafinai masu dogon zango da yawa kuma duk saƙon da na ke so na isar da shi idan ban yi amfani da salo na jan hankali ba, mutane ba za su so su kalla ba.
“Kuma sannan kasuwanci na ke yi, dole in yi abin da su mutane za su bibiyi abin.
“Ta haka ne zan samu damar isar da saƙo na kai-tsaye; kamar yadda shi wannan matashi ya yi barikanci da tara ‘yanmata, ka ga ai ba za ka ce ya daina ba kai-tsaye, amma ta hanyar yin fim dole mutane za su fuskanci abin da na ke nufi.”

Jaruman fim ɗin dai sun haɗa da Nafisa Salisu, Tahir Fagge, Hassana da Usaina na ‘Daɗin Kowa’, wato Gimbiya da Sa’adatu, Kamalu Sirrinsu, West ɗan Kibiya, Y. Saraki, Aisha Usman da sauran Hassan da Usainin cikin fim ɗin.