* Jaruma mai kama da Jamila Nagudu ta bayyana dalilin ta na shigowa harkar fim da inda ta dosa
KAMAR dai yadda ku ka sani, a kullum sababbin mata shigowa harkar fim su ke yi. To, ita ma Sharifa Ibrahim sabuwa ce a farfajiyar finafinan Hausa. Amma kuma ita ta bambanta da sauran matan da ke shigowa harkar, domin kuwa ita ta zo ne da dutse ɗaya ta jefi tsuntsu uku. Sharifa dai jaruma ce, mawaƙiya ce, sannan kuma furodusa ce.
Jarumar dai kyakkyawa ce, son kowa ƙin wanda bai samu ba. Da yawa ana cewa ta na kama da Jamila Umar Nagudu, domin idan ba ka duba da kyau ba, ba za ka taɓa gane cewa ba Jamilar ba ce.
Wakilin mu ya zanta da jarumar a lambun shaƙatawa da ke Ƙofar Gamji a garin Kaduna, lokacin da ta ke ɗaukar kundin waƙoƙin ta na bidiyo.
Jarumar ta fara da cewa, “Suna na Sharifa Ibrahim Nagudu. Ni ’yar Kaduna ce, amma na zauna a Yola. Na yi makarantar firamare na a nan Kawo, Kaduna, daga nan kuma na koma Yola na yi sakandire na, inda a halin yanzu ina NCE a can Yola.”
Ko me ya ba ta sha’awar shiga harkar fim? Sai ta ce, “Na jima ina son harkar fim. Sannan kuma idan na ga ana waƙa a fim sai in ji da ma a ce ni ce na ke yi. Da haka na fara sha’awar waƙa, har na zo na fara yi da kai na. A haka Allah ya albarkaci abin, ga shi ina shirya fim, kuma ina fitowa a fim.”
Jarumar ta ƙara da cewa ta yi waƙoƙin siyasa dama. “Ban da na siyasa kuma na yi waƙoƙi waɗanda zan yi album da su. Yanzu haka aikin ka ɗaukar album ɗin ka same mu mu na yi.
“Sannan kuma a ɓangaren fim, na shirya wani fim mai suna ‘Soson Ƙarfe’ da kuma wani ‘Gidan Duniya’. A yanzu haka su na kan hanyar fitowa.
“Sannan halin da ake ciki yanzu na shirya tsaf domin fara ɗaukar wani sabon fim ɗin nawa,” inji ta.

Wace matsala Sharifa ta fuskanta a harkar fim? Sai ta ce, “Gaskiya ban samu matsala a harkar fim ba. Sai dai harkar sai ka daure, domin akwai gajiya, ga tafiye-tafiye irin wanda ba ka saba ba. Amma kuma ta ɓangaren iyaye, na na fuskanci matsaloli da dama, don iyaye na ba su son harkar, ba su ma yarda ba da farko, amma yanzu na fahimtar da su, kuma sun yarda.
“Kuma alhamdu lillah, na samu nasarori da dama, musamman ma a ɓangaren waƙoƙin siyasa da na yi, na samu alherin da ba zan taɓa mantawa ba.”
Ko menene alaƙar ta da Jamila Nagudu? Sai jarumar ta ce, “Gaskiya ina kama da Jamila Nagudu, domin da dama idan na je wuri ana ɗauka Jamila ce. Mun taɓa haɗuwa da Jamila lokacin da na yi wani albun na siyasa, ni da ita mu ka yi aikin tare; kamar da mu ka yi ce ta sa ake kira na da Nagudu.”
Menene burin Sharifa? “E, gaskiya ina da buri babba, kuma sai na cika buri na da yardar Allah, sannan sai in yi aure. Amma kuma ko yanzu a kasuwa na ke, ban taɓa aure ba!”
Shawarar ta ga ’yan fim ita ce: “Gaskiya ana yi wa ’yan fim kallon da ba haka ba ne, domin gani ake kamar ’yan fim abin da su ke yi iskanci ne. Gaskiya ni dai ban gani ba da na shigo harkar. Don haka masu yi wa ’yan fim kallon ’yan iska su bari, domin ɓata suna ne ga duk masu sana’ar fim.
“Sannan ina yi wa masoya na godiya ta musamman. Kuma ina tare da su a duk inda su ke.”