• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

A zaɓen gwamnoni za mu magance matsalolin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa – Yakubu

by DAGA WAKILIN MU
March 5, 2023
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu (a tsakiya) a wajen taron da ya yi da kwamishinonin zaɓe

Farfesa Mahmood Yakubu (a tsakiya) a wajen taron da ya yi da kwamishinonin zaɓe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC za ta yi dukkan abin da za ta iya domin tabbatar da a lokacin zaɓen gwamnoni an kauce wa maimaita duk wasu cikas ɗin da aka fuskata lokacin zaɓen shugaban shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.

Yakubu ya yi wannan jaddadawa ce a lokacin da ya ke taro da Kwamishinonin Zaɓe na Ƙasa, domin bibiya da nazarin yadda hukumar ta gudanar da zaɓen 25 ga Fabrairu, 2023.

Ya ce maƙasudin taron na su shi ne a tattauna cikas ɗin da aka samu da kuma tabbatar da cewa ba a sake maimaita faruwar haka a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi ba, wanda za a gudanar a ranar 11 ga Maris, 2023.

“Babu shakka zaɓen da aka gudanar a satin da ya gabata ya samu cikas da ƙalubalen da ke buƙatar magancewa da kuma hana sake afkuwar su da gaggawa. An ɗauki lokaci tare da shan matuƙar walaha wajen tsare-tsaren yadda za a gudanar da zaɓe. Amma dai an fuskanci cikas wajen aiwatarwa.

“Waɗansu ƙalubalen da aka ci karo da su, bagatatan su ka faru, ba a yi zato ko tunanin hakan zai iya faruwa ba. Musamman matsalolin aikawa da kayan zaɓe, na’urorin sadarwa da tsarin fasahar zamani, halayyar wasu jami’an zaɓe, ɗabi’un wasu ejan-ejan na jam’iyyu da masu goyon bayan jam’iyyun sun ƙara kawo wa tsarin tafiyar da shirin naƙasu ko cikas.”

Yayin da ya ke yaba wa irin jajircewar da ‘yan Nijeriya su ka yi da halin dattakon da wasu shugabannin siyasa su ka nuna, Yakubu ya ce abin da ya faru a lokacin zaɓe ya zama wani babban darasi ga INEC, ta yadda ta gaggauta gano matsalolin da su ka faru, domin kauce wa sake faruwar irin haka a zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihohi, wanda za a yi zaɓen gwamnoni a jihohi 28, kuma za a zaɓi ‘yan majalisar dokoki har 996.

Yakubu ya ce a zaɓen ranar tilas ma’aikatan INEC su zage damtse sosai a lokacin zaɓen ranar 11 ga Maris.

Kwamishinonin Zaɓe a wajen taron su da shugaban INEC

“Duk ma’aikacin da aka kama ya na wasa ko rashin ɗaukar aikin sa da muhimmanci, ko na dindindin ne ko na wucin-gadi a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, to kada a kuskura a bar shi ya yi aikin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.

“Tilas kuma ya kasance an kai kayan zaɓe kwanaki kafin ranar zaɓe a dukkan ƙananan hukumomi.

“Kwamishinonin Zaɓe da aka tura jihohi za a ɗora wa laifin rashin kai kayan zaɓe zuwa ƙananan hukimomi da wuri. Haka babu wani dalilin da za a ƙi kai janareto a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.”

Yakubu ya ce za a tabbatar an yi amfani da na’urar tantance masu rajistar zaɓe, wato BVAS a ranar zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

Loading

Tags: BVASINECkwamishinonin zaɓemahmood yakubumatsaloliZaɓen 2023zaɓen gwamnonizaɓen shugaban ƙasa
Previous Post

Aure: Jarumin Kannywood Tijjani Asase ya zama mai igiya biyu

Next Post

INEC ta ja kunnen PDP kan yi wa shugaban ta ‘sharri da ƙarairayi’

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post

INEC ta ja kunnen PDP kan yi wa shugaban ta 'sharri da ƙarairayi'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!