• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta ja kunnen PDP kan yi wa shugaban ta ‘sharri da ƙarairayi’

by DAGA WAKILIN MU
March 13, 2023
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyar PDP cewa idan ta na da wani ƙorafi to ta garzaya kotu, amma ta daina ƙala wa shugaban ta abin da ta kira “sharri da jingina masa ƙarairayi”.

INEC ta ce maganganun ɓata sunan da PDP ke yaɗawa kan Farfesa Mahmood Yakubu za su iya janyo wa hukumar da shugaban nata su maka PDP a kotu domin su nemi haƙƙin su.

Kakakin Yaɗa Labarai na shugaban, Mista Rotimi Oyekanmi, shi ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da ya ke amsa tambayoyi game da kiraye-kirayen neman shugaban INEC ya sauka daga muƙamin sa.

Oyekanmi ya ce kiraye-kirayen da PDP ta yi kwanan nan cewa Yakubu ya sauka, kawai shirme ne ta ke yi.

Ya ce: “Abin takaici kuma abin dubawa, duk da tulin zargin da PDP ke wa shugaban INEC, waɗanda dukkan su marasa tushe ne ballantana makama, har yau ta kasa kawo hujja guda ɗaya inda ya aikata ba daidai ba, ko inda ya take doka.

“Tabbas, PDP ta kasa kawo ko da hujja guda ɗaya domin bai wa zargin da ta ke yi wata kariya cewa Yakubu ya aikata ba daidai ba ko ya karya dokar zaɓe ta 2022.

“Sannan kuma PDP ba ta bayar da hujjar cewa Yakubu ya yi maƙarƙashiyar ƙin loda sakamakon zaɓe daga na’urar BVAS ba.”

Oyekanmi ya ce abin takaici ne a surutan da PDP ta riƙa yi ba ta ce an yi maguɗi a dukkan sassan da PDP ɗin ta yi nasara a faɗin ƙasar nan ba.”

Kan haka ne INEC ta shawarci PDP idan ta na da wani ƙorafi a kan zaɓe, to ta garzaya kotu kawai.

Loading

Previous Post

A zaɓen gwamnoni za mu magance matsalolin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa – Yakubu

Next Post

Dakan-ɗaka-shiƙar-ɗaka: An saka ranar auren darakta Kamal Alƙali da jaruma Hauwa SG

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Tuwo-na-mai-na: Hauwa S. Garba da Kamal Alƙali

Dakan-ɗaka-shiƙar-ɗaka: An saka ranar auren darakta Kamal Alƙali da jaruma Hauwa SG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!