TSOHON Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya bayyana cewa babu wani mugun abu da zai faru tsakanin ‘yan Kannywood da gwamnatin sabon zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), don ƙalilan da ka cikin su ne su ka mara masa baya.
Iyan-Tama ya yi wannan magana ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim a yau bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ba da sanarwar cewa Abba na jam’iyyar NNPP ɗin ne ya lashe zaɓe a jihar.
Akwai masu hasashen cewa sabuwar gwamnatin da za a kafa za ta iya tafiya ba tare da kyautata wa ‘yan fim ba saboda sun yi tallar abokin adawar Abba, wato Dakta Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Shi kuwa Iyan-Tama cewa ya yi, “Bayan Kwankwasiyya da ka faɗa, mutanen NNPP ne. Sannan kuma waɗanda su ka taimaka don ganin cewa Abba Kabir Yusuf ya kai gaci, ba mu da yawa daga cikin harkar fim kamar yadda ka faɗa, ba na jin za ka ƙirga sama da mutum bakwai ko takwas a iya sani na.
“Akwai waɗanda sun faro su ka ga kamar ba za a yi nasara ba su ka ja da baya, akwai kuma waɗanda su ka shiga kamar wata uku da su wuce su ka fara tafiyar.”
“Gwamnatin da ta fara taimaka wa harkar fim, ta kafa Hukumar Tace Finafinai, gwamnatin mai girma Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ce. Shi ne wanda ya kafa hukamar, duk gwamantin da ta zo ɗorawa ta yi a kai. Ka ga ko duk kulawa ce wannan.
“Da ya dawo a Dawo-Dawo, mai girma Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne wanda ya ƙirƙiri ‘Film Academy’, wanda aka yi a Bagauda, wanda ranar da ya rantsar da kujeru da komai, ina daga cikin wanda mu ka je. Bayan ya ƙaddamar da ita, aka zo aka ce za a yi makarantar fim a wajen.
“Sannan na uku, ya ja ‘yan fim da yawa a jikin sa tun a wancan karon. Ko ni ina ɗaya daga ciki, lokacin da zan tafi Amerika, na rubuta wa gwamnatin Jihar Kano, gwamnati ta ba ni kuɗin tikiti da komai da komai da ɗaki da yadda za a karrama ni a Amerika.
“Don haka mu na da kyakkyawar alaƙa da shi. Sannan kuma ita gwamnati ta kowa ce. In Allah ya sa Abba Kabir ya fara aiki, mu na sa rai zai taimaka wa masana’antar fim a inda ya dace ya taimaka mata. Mu na kuma sa rai zai taimaka wa waɗanda su ka taimaka, tunda za su iya ba da gudunmawa a cikin ita gwamnatin kan ta, wajen tafi da gwamnatin wurin samun nasara.
“Mutum ne wanda da ma duk wanda ya taimaka masa, shi ma zai taimake shi. To, mu ba ma tunanin mu a taimake mu ba, tunanin mu shi ne mu mu taimaka wa gwamnatin ta yi nasara, a ce an yi gwamnatin da ta yi nasara, ta taimaki al’umma, ta yi aiki kamar ta Abba Kabir Yusuf, shi ne tunani na. Saboda haka, mu na sa rai in-sha Allahu, adali ne, mutum ne na kirki, kuma ya na da kula da mutanen da ke kusa da shi da kuma waɗanda su ka yi masa hidima.”
A ɓangaren Hukumar Tace Finafinai, shin ko Iyan-Tama ya na ganin gwamnatin Abba ta na iya ɗauko ɗan fim kamar yadda gwamnatin baya ta yi, ko kuma bare za ta ɗauko? Sai ya amsa da cewa, “To, Allahu a’alam. Allah ne kaɗai ya san me gobe za ta haifa a kan wannan maganar taka. Domin shi dai ya na da ‘plan’. Kuma ya na da team, ya na da kwamiti, ya na da daraktoci waɗanda aka kafa duk da dai ina cikin tawagar kamfen ɗin sa, amma ba na cikin daraktocin da ake rufe ƙofa, amma dai mun yi imani in an ɗauko na waje an ba shi, mu dai buƙatar mu in dai zai taimaka wa masana’antar, ita Hukumar Tace Finafinai mutane su na ɗauka ta ‘yan fim ce. Ta gwamnati ce, ma’aikatan ta na gwamnati ne. Dangantakar hukumar da ‘yan fim shi ne ka yi fim ɗin ka ko kafin ka yi ka kai labari, in littafi ka rubuta, ka kai kafin ka buga su duba. Haka shi ma fim, idan ka kai kuɗi ma za ka biya su, ba kyauta su ke yi ba, in sun gama su ce mun amince ga wannan takarda ku sayar da shi a Kano, wanda ba ɗan Kano ba babu dole sai ya yi ‘censorship’ ɗin Kano.
“Amma idan Abba Kabir ya ce zai ɗauko ɗan fim ya ba shi, akwai waɗanda su ka dace da yawa a cikin ‘yan fim. Sannan in kuma ya ce zai ɗauko na waje, da ma hukuma ce da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu, idan Allah ya an ɗauko na wajen, tunda a baya an yi na wajen a lokacin Kwankwaso na farko, da ya dawo na biyu, da ma an yi yarjejeniya, shi Kwankwaso ga wanda ya ke so ya ba wa, su kuma su ka haɗa kai su ka ce ga wanda su ke so, shi kuma Kwankwason ya ɗauko na baya, ka ga sun yi wa kan su.
“To, wannan ma da aka yi ina tabbatar maka wasu mutane ne su ka haɗa kai su ka samu farkon gwamnatin su ka ce su ga wanda su ke so a ba wa, ko ya cancanta ko bai cancanta ba. Ita kuma gwamnatin tunda ta ga waɗannan mutane sun ba ta gudunmawa, sai ta ce to shi kenan, ku ku ka kawo shi? E.
“Daga baya kuma aka samu matsaloli da shi da gwamnatin da mutanen ma da su ke ‘yan fim ɗin, haka aka samu rashin fahimta. Duk wanda aka ba shi wannan kujera, an ba shi ne don ya kyautata alaƙa da ‘yan fim, mawaƙa, da marubuta da gwamnati. Duk wanda aka ba shi, ba an ba shi ba ne don ya riƙa kama mutane ya na ɗaurewa, da gaskiya, ba gaskiya, Allah shi ne masani. Don haka mu na sa ran za a tafi da jama’ar.
“Akwai waɗanda su na cikin tafiyar NNPP, akwai irin su Abba El-Mustapha, ana kiran shi Abba Na Abba, akwai irin shi kusan mutum uku d zan iya kiran su a iya sani na.
“Akwai waɗanda su ke ganin APC za ta ci zaɓe, sai duk aka raja’a can, saboda yanayin da ake ciki, ana ɗan tsakuro wani abu ana ba su. Sai kuma Allah ya yi ikon sa, ya ɗauko wanda ba a tunani ya ba shi.
“Mu ‘yan ƙalilan ɗin da mu ka yi Abban mu na sa rai in-sha Allahu, za a tuna da waɗanda su ka ba da gudunmawa, da yardar Allah.”