ALLAH ya albarkaci tsohuwar jarumar Kannywood Abida Muhammad da samun ɗa namiji.
An raɗa masa suna Al-Mustapha.
Abida ta haihu ne a ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2020 a gidan mijin ta da ke Legas.
Majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa ita da yaron da ta haifa su na cikin ƙoshin lafiya.
Mu na fatan Allah ya raya Al-Mustapha cikin aminci, kuma ya sa mai jinƙan iyaye ne, amin.
Ita dai Abida, ta auri mijin ta na biyu mai suna Al-Mustapha Abubakar, wanda soja ne mazaunin Legas, a ranar Juma’a, 26 ga Janairu, 2018. A lokacin da aka yi auren ma, ya na bakin daga a Jihar Borno inda sojojin Nijeriya ke yaƙar ‘yan ƙungiyar Boko Haram.

Wato dai sunan sa ne aka raɗa wa ɗan nasu.
A auren ta na farko, ta auri furodusa Hamza Muhammad Ɗanzaki ne, shugaban kamfanin shirya finafinai na Home Alone Production, amma sai Allah ya yi masa rasuwa bayan shekaru.
Akwai ‘ya’ya a tsakanin su.
Bayan rasuwar Hamza, Abida ta shafe shekaru da dama ta na zawarci, amma ba ta dawo harkar fim ba har ta sake yin aure.
A lokacin zawarcin nata har ta zama marubuciyar littafin hikaya kuma memba a ƙungiyar mata marubuta.