AN bayyana shirin ‘Rumfar Mai Shayi’ a matsayi fim wanda ya sha bambam da sauran finafinan da aka saba yi a Kannywood saboda irin salon da ya zo da shi.
Daraktan fim ɗin, Nasiru B. Muhammad, shi ne ya bayyana hakan a lokacin tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi.
Nasiru ya ce: “‘Rumfar Mai Shayi’ fim ne mai dogon zango, wato ‘short film’, da ake yin sa a waje guda, wanda ba ya wuce tsawon minti goma, da ake haska shi a kafar YouTube wanda kuma babbar manufar shirin shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa da ya kawo rashin cigaba a ƙasar nan.
“Kuma kamar yadda sunan fim ɗin ya nuna, rumfar mai shayi waje ne da ya ke tara mutane masu fahimta daban-daban, don haka za ka samu ra’ayoyi mabambanta a kan abin da ya shafi al’amuran yau da kullum. Sai dai mun ƙara da wata hikimar inda mu ka ajiye wata mai ƙosai a gefen rumfar domin wakilcin mata, don su ma a ji muryar su.
“Don haka manufar wannan fim ɗin dai shi ne a samo ra’ayoyin mutane da dama domin a samo hanyar da za a warware matsalolin da su ke haifar da cin hanci da rashawa. Wannan ya sa mu ka mayar da hankalin mu a kan abin da mu ka sa a gaba.”
Daraktan ya ƙara da cewa, “Fim ɗin ya bambanta da finafinan Kannywood, domin ko a zaɓe na gaba fim ɗin zai taka muhimmiyar rawa a wajen samar da shugabancin da mutane su ka zaɓa da kan su da kuma kauce wa cin hanci da rashawa.”
Nasiru ya yi fatan samun nasarar da su ka sa a gaba wajen gudanar da aikin.