AN fi sanin Yahaya Dauda da laƙabin Sabon Uji. A da mawaƙin Kannywood ne, to kuma sai ya ɗauko salon waƙoƙin marigayi Alhaji Haruna Uji har ya shahara a wannan fagen.
A tattaunawar da ya yi da mujallar Fim kwanan nan, ta tambaye shi musabbabin rikiɗar sa zuwa Sabon Uji, shi kuma ya ce: “To ni dai tarihin waƙoƙin da na yi ɓangare biyu ne, akwai lokacin da na ke waƙoƙi a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, da kuma a yanzu da na ke amsa sunan Sabon Uji.
“Amma dai farkon waƙa ta zan iya cewa ni kamar ɗan gado ne, don tun ina yaro na ke jin waƙar Haruna Uji a gidan mu har na ke hadda. Amma dai farkon waƙa ta na yi ta soyayya guda ɗaya, na yi ta siyasa guda ɗaya. A 2008 kenan.
“Kuma yadda na ce da kai, na gaji waƙar shi ne Haruna Uji aminin mahaifi na ne; tare su ka tashi su ka yi yawon makarantar allo tare, har su ka girma kowa ya kama sana’ar sa su na tare.”

Dangane da abin da ya sa a yanzu ya fi sha’awar ya yi waƙoƙin Uji kuwa, cewa ya yi, “To, ni Bahaushe ne da na ke kishin yaren Hausa, kuma idan ka duba shi Haruna Uji waƙoƙin sa su na tafiya ne da bunƙasa harshen Hausa. Don haka da na ga na fi kusa da matsayin da na aminin mahaifi na, sai na ga ya kamata na ɗauki salon waƙoƙin sa.
“Sannan kuma na duba an samu magajin Shata, an samu na Ɗanƙwairo, to me ya sa ba za a samu na Haruna Uji ba? Don haka sai na ga bari ma na ɗauko gurmi don na zama magajin sa.
“A lokacin da na fara har ma wani kallo ake yi mani, ana yi mani dariya. Amma a yanzu su masu yin dariyar har sha’awa na ke ba su. Ka san a harkar an saba ba a zuwa da sabon abu, sai dai idan wani ya zo da na a yi ta yi. To ni kuma na fi so na samar da nawa ko da kuwa zan faɗi wajen samar da abin, saboda faɗuwar za ta koya mani darasi.
“Don haka a yanzu tun da na fara ina cikin shekara ta huɗu, amma sai ga shi na kai ga matsayin da na ke nema.”
Shin ko waƙoƙin Yahaya Dauda na Uji ne ya ke kwaikwayo, ko kuma ya na yin nasa? Sai ya amsa: “To, gaskiya ba haka yake ba, don in ban da waƙar Balaraba duk a cikin waƙoƙin Haruna Uji babu wadda na ke yi, duk salon waƙoƙi na ne. Kawai dai ina tafiya ne a wani salon waƙoƙi irin nasa. Har ma da ɗan sa ya ji ya ce da ni abin ya burge shi, don su da su ka gada ba za su iya yi ba.”

Da mu ka tambayi Sabon Uji idan ya taɓa samun wata matsala a game da harkar sa ta waƙa, sai ya ce, “E, babbar matsalar da na samu a waƙa ita ce da na je neman aure aka hana ni saboda ina waƙa. To wannan shi ne abin da ba zan manta da shi ba.”
Mawaƙin ya yi kira ga sauran mawaƙa da su riƙi al’ada, su watsar da waƙoƙin da ba su da ma’ana ko su ke rusa al’adar mu ta Hausa. Da fatan sun ji.