• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buhari ya karrama Minista Sadiya da kyautar inganci da sadaukarwa a aiki

by DAGA WAKILIN MU
October 22, 2022
in Nijeriya
0
Shugaban Ƙasa Buhari ya na miƙa kyautar karramawa ta ingancin aiki ga Hajiya Sadiya Umar Farouq

Shugaban Ƙasa Buhari ya na miƙa kyautar karramawa ta ingancin aiki ga Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da kyautar karramawa ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, saboda gamsuwa da kyautatuwar ayyukan ta na taimako da jinƙan jama’ar Nijeriya.

Shugaban ya ba da kyautar mai suna Karramawa kan Kyautatuwar Aikin Jama’a ta Nijeriya (Nigeria Excellence Award in Public Service, NEAPS) ga ministar da kuma wasu mutum 44 a ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A bikin, Buhari ya bayyana cewa an ba da kyaututtukan karramawar ne bisa la’akari da mutanen da su ka yi zarra kuma su ka zama misali wajen wa al’umma aiki bilhaƙƙi da gaskiya.

Ya faɗa wa waɗanda aka karrama ɗin cewa: “An samar da wannan kyautar karramawar ne bisa sahihiyar hujjar nasarorin da ku ka samu a sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasar nan.

“Za a ba ku wannan karramawa ne saboda kun yi zarra wajen yi wa al’umma aiki kuma ku ka ba da gudunmawa ga kawo canji mai ma’ana a ƙasar nan.

“Wannan abin koyi ne ga shugabannin yanzu da masu zuwa nan gaba domin su ƙara himma wajen aikin ciyar da ƙasar nan gaba.”

A jawabin da ta yi bayan an yi mata wannan karramawa, Minista Sadiya ta bayyana jin daɗi da aka zaɓe ta aka ba ta wannan kyauta ta NEAPS.

Ta ce: “Wannan wani muhimmin zango ne, musamman a rayuwa ta, domin wannan karramawa  shaida ce ƙarara ta gamsuwar da aka yi da ‘yan nasarorin da na samu a wajen ayyukan da na yi wa jama’a ya zuwa yanzu da kuma alhakin da aka ɗora mani a fagen ayyukan inganta rayuwa da jinƙai a cikin ‘yan shekarun nan.

“Ina so in ƙara miƙa matuƙar godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa saboda damar da ya ba ni na yi wa ƙasa ta aiki a matsayin Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, sannan ta hanyar wannan muƙamin na yi ƙoƙarin bautata wa ɗimbin mutane marasa galihu waɗanda ke cikin buƙatar a inganta rayuwar su da taimakon jinƙai cikin gaggawa a faɗin ƙasar nan.

Shugaba Buhari tare da waɗanda aka karrama da kuma jami’an gwamnati a hoton da su ka ɗauka a ƙarshen taron

“Haka kuma ina godiya matuƙar gaske ga kamfanin ‘TBS Media’ da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da su ka ga dacewa ta har su ka ba ni wannan babbar kyauta ta NEAPS ta shekarar 2022 a ɓangaren ayyukan jinƙai, kuma su ka ɗora ni kan matakin shiga da’irar sauran manyan ‘yan Nijeriya waɗanda su ma aka karrama su tare da ni a yau.”

Ministar ta sha alwashin za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarin ta wajen yi wa ƙasar nan aiki wanda yin shi ne gudunmawar ta wajen taimakawa a tsamo Nijeriya daga cikin matsalolin da su ka addabe ta.

Mai taimaka wa ministar a fagen aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta yi ƙarin bayanin cewa wannan kyautar karramawa da aka yi saboda aiki ga jama’ar Nijeriya “manufar ta ita ce a karrama muhimman ayyukan da aka yi wa jama’a a Nijeriya ta hanyar gudunmawar da jama’a ɗaiɗaiku da jihohi da mutanen unguwa su ka bayar wajen shugabanci da aikin jama’a da jinƙai.”

Waɗanda su ka shirya bikin karramawar dai su ne Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) da wani kamfani mai suna ‘The Best Strategic Media’ (TBS).

Loading

Tags: aikin jama'a.harkokin jinkaikarramawar ingancin aikiMuhammadu BuhariNneka Ikem AnibezeOfishin Sakataren Gwamnatin TarayyaSadiya Umar FarouqTBS Media
Previous Post

Har yanzu na ɗauki kai na a mawaƙi, inji jarumi Auwal Ishaq (Yawale Ɗankurma)

Next Post

Abin da ya sa na ɗauki salon waƙoƙin Uji – Yahaya Dauda

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Yahaya Dauda (Sabon Uji) da gurmin sa

Abin da ya sa na ɗauki salon waƙoƙin Uji - Yahaya Dauda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!