• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa na ke hidimar agaza wa marasa galihu – Rasheeda Maisa’a

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 6, 2019
in Tattaunawa
0
Rasheeda Adamu Abdullahi

Rasheeda Adamu Abdullahi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
TSOHUWAR jaruma kuma furodusa Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a) ta yi fice a wajen tallafa wa marayu da sauran mabuƙata a gidauniyar ta, wato ‘Maisa’a Charity’. A ƙarƙashin wannan gidauniyar, mabuƙata masu yawa sun samu ’yanci ta hanyar ba su ilimi da samar masu da lafiya da sauran abubuwan buƙata inda ta ke shiga lungu da saƙo don ganin ta warware matsalolin su.
 
A zantawar su da wakilin mujallar Fim, MUKHTAR YAKUBU, jarumar kuma ’yar siyasa ta yi bayani a kan tsawon lokacin da ta yi ta na gudanar da gidauniyar da irin nasarorin da ta samu.
 
 
FIM: Za mu so ki sanar da masu karatu yadda aka yi ki ka samar da Gidauniyar ki ta ‘Maisa’a Charity’ da kuma abubuwan da ki ke gudanarwa a gidauniyar.
 
RASHEEDA MAISA’A: To ita dai wannan gidauniya tawa ina ganin na kafa ta ne yau kusan shekaru takwas kenan. Koda yake a baya da na kafa ban yi  mata suna ba, ina yin abubuwa ne haka na taimako, sai na ga akwai buƙatar na rinƙa tafiya da zamani, don haka sai na mayar da shi a matsayin gidauniya, na yi mata suna, na ci gaba da yin abubuwa da sunan gidauniyar. 
 
Ina taimaka wa marasa ƙarfi, idan mutum ba shi da lafiya  na kai shi asibiti, kuma na kan shiga asibiti duka, na je ɗakin yara masu yoyon fitsari ina kai musu tallafi. Kuma sai ya zama na buɗa abin, na ɗauki ma’aikata da za mu rinƙa yin aiki da su. Sai kuma na gano akwai mutanen da su ke son tallafa wa jama’a, sai dai ba su da kafar da za su bayar, wasu kuma su na son su yi tallafin amma ba su da kuɗin da za su yi, to a haka sai mu ka haɗu, wasu su bayar kuma wasu da ba su da halin bayarwa sai su zo mu tafi mu raba kayan tallafin da su. Ka ga sun yi da ƙarfin su. 
 
Mu na shiga lungu da ƙauyuka kamar wajen ’yan gudun hijira mu na kai masu kayan abinci da kayan sakawa da magunguna, har mu na yin gwaji na cutar HIV da ƙwayar foliyo, mu haɗa kai da ƙungiyar lafiya.
Kuma mu na ƙoƙarin gyara, kamar saka rufin kwano da tabarmi da butoci har ma da fanka. 
 
Kuma mu na samar da makarantun Islamiyya; don akwai wani ƙauye da mu ka kai tallafi na sabulu da omo, to akwai wata mata da ta tashi ta ɗaga hannu ta ce ita ba burin da ta ke da shi kamar ta kai shekara 40, amma ba ta iya fatiha ba, don haka su na son mu kawo masu malaman addini da za su rinƙa koyar da su. To a wannan waje a take mu ka nemi mai unguwa  ya sahale mana mu yi makaranta ta Islamiyya ta langa-langa, kafin mu samu damar da za mu gina masu. Haka kuma aka yi; aka samar masu, na zo cikin gari na samar masu da malamar da ke zuwa ta na koyar da su. To yanzu an kusa shekara guda kenan ana ba su ilimi. A yanzu har mun zama ’yan’uwa da su. Har kayan miya za ka ga sun aiko min kwandon tumatur.
 
FIM: A yanzu yaya tafiyar da gidauniyar ta ke idan ki ka kwatanta ta da ta baya?
 
RASHIDA: E, a yanzu an samu ci-gaba sosai. Ka ga da ni kaɗai ce, ɗan abin da na samu shi ne na ke yin hidima da shi, amma yanzu da na samu muƙamin gwamnati a matsayi na na mai ba Gwamna shawara a kan harkar mata ka ga samun kuɗi na ya ƙaru. Kuma ina bin manyan mutane waɗanda ba za su iya fitowa da kan su su yi ba, in bi ina kai wa mutane takardar neman taimako, don akwai buƙatar da za ta taso wadda ta fi ƙarfin mu, sai mu rubuta takarda mu kai wa masu hali, kuma ckin hikimar Allah duk inda mu ka je ba ma rasawa.  
 
FIM: A wannan aikin da ki ke yi, ko wanne mara lafiya ne ki ka samu wanda ki ka matsu ko ta halin ƙaƙa ki ga an samu taimako don ya samu lafiya?
 
RASHIDA: To akwai wani yaro wanda na san maganar sa ta yaɗu a Kano har Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya je ya duba yaron, za a yi masa aikin ƙoda. 
 
Wata rana mun dawo daga wani ƙauye wajen rabon tallafi sai na ce mu bi ta Asibitin Nassarawa don mu duba jikin yaron. Mu ka je mu ka tambaya menene matsalar sa? Aka ce za a yi masa dashen ƙoda naira miliyan goma sha ɗaya. Cikin ikon Allah, da na zo na saka abin a cikin shafi na, ina jin sha biyu na dare na saka, amma ƙarfe uku na dare sai ga wani mutum daga ƙasar Jamus ya ce na tura masa komai na asibitun da kuma aikin da za a yi masa, da kuma kuɗin da za a kashe a aikin. 
 
Amma wani al’amari na Allah, bayan mun je mun gama magana iyayen sa sun ba da asusun ajiyar su Allah Ya yi wa yaron rasuwa!
Kuma mun ƙara samun wani mutum ya na da ciwon ƙoda, ya na da ciwon suga da HIV, kuma ya na da kansa ta cikin jini. To ana son a fita da shi zuwa Indiya don yi masa magani, sai na sanar da wannan mutumin ga halin da wannan ya ke ciki. Kwanaki uku ya turo da miliyan bakwai, sai aka shirya tafiya.
 
Wannan mara lafiya sai da ya kai wata uku a Indiya, Allah Ya sa ya rabu da ciwon duka. A yanzu mutumin ya na cikin ƙoshin lafiya, kuma kullum ya na yi min fatan alheri. A yanzu ma da shi mu ke harkar raba kayan tallafi na gidauniya ta. Don daga wannan ya kawo min wasu marasa lafiya an nema masu magani.
 
FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a rayuwar ki ta ɓangaren tallafa wa jama’a?
 
RASHIDA: Babbar nasara ita ce sa farin cikin zuciyoyi, don a duk lokacin da na tallafa wa jama’a na kan samu kai na cikin farin ciki. 
 
Kuma na samu lambobin yabo da dama da aka karrama ni da su; har ma London na je na karɓi lambar girmamawa, kuma nan gaba kaɗan zan je ƙasar Jamus. Shi ya sa kullum mu ke buɗa abin, don yanzu akwai kaya da mu ka ɗinka na ’yan mata da yara wanda za mu kai Tudun Maliki gidan masu taɓin hankali, akwai ’yan mata da samari da su ke buƙata. 
 
Haka akwai wata uwar marayu da ita ma za mu kai mata ta bai wa yara don su yi hidimar Maulidi don tunawa da haihuwar fiyayyen halitta. 
 
FIM: Wasu ƙungiyoyin idan su na neman tallafi na mara lafiya akan turo musu kuɗin ta asusun ajiyar su. Ke ma haka ki ke yi?
 
RASHIDA: To gaskiya ni ba haka ba ne. Na kan tura asusun ajiyar ’yan’uwa ko iyayen mabuƙata ne, idan na tura nawa ka ga yau ba ka san yadda rayuwa za ta kasance ba; to idan ta Allah ta kasance sai abin ya zama da matsala, don haka ba na yin amfani da asusun ajiya ta. Kuma duk kuɗin da mu ke samu ba ma amfani da shi a buƙatar kan mu sai dai mu tura ga masu buƙata.
 
FIM: Daga ƙarshe, menene fatan ki na ƙarshe a game da wannan gidauniya taki?
 
RASHIDA: Fata na shi ne har ’ya’ya na da jikoki na su gaji abin da na ke yi. Kuma ina godiya ga ɗimbin jama’a da su ke bada gudunmuwa, musamman gwamnatin Kano da sauran jama’a.
 
 
 

Loading

Previous Post

An shiga tsananin jimami sakamakon rasuwar Umar Sa’idu Tudunwada

Next Post

Adamu Ability ya zama mai igiya 3

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Amarya Maryam (Ummy) tare da ango Adamu Ability a wajen dinar auren su

Adamu Ability ya zama mai igiya 3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!