• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abubuwa uku na ke sha’awa a rayuwa ta – Fati Nayo

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 3, 2022
in Taurari
0
Fati Nayo (Kyauta Dillaliya)

Fati Nayo (Kyauta Dillaliya)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR nan wadda aka fi sani da Kyauta Dillaliya a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, Fati Nayo, ta bayyana harkar fim a matsayin abin da ta ke sha’awar sa tun ta na ƙarama, kuma a yanzu da Allah ya sa ta girma Allah ya cika mata burin ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim.

Fati ta ce: “Abubuwa uku na ke sha’awa a rayuwa ta tun ina ƙarama kuma da na girma duk Allah ya cika mini buri na a kan su.

“Domin kuwa a rayuwa ta ina da sha’awar na yi fim da harkar koyarwa da kuma kwalliyar mata, kuma duk sun zama sana’ar da na ke yi a yanzu, domin baya ga fim ma har waƙa na ke yi. Don haka ni Allah ya yi mani baiwar da ba kowa ya ke samun haka ba a rayuwar sa.”

Da ya ke an fi sanin ta a ‘Daɗin Kowa’, mun tambaye ta ko daga shi ta fara?

Sai ta ce, “E to, akwai wani fim mai suna ‘Kuyanga’, da shi na fara, wanda maigida na Salisu Officer ya shirya, kuma gaskiya na ji daɗin aikin don Mustapha Musty shi ne mai ba da umarni, don ka san ni ba na son irin daraktocin nan masu hantara, saboda wasu idan aka ga sabuwar fuska ce sai a riƙa ci maka mutunci.

“To a wannan fim ɗin na fito a matar Waziri. To bayan shi dai na yi finafinai kamar guda uku amma dai ban riƙe sunan su ba. Daga nan kuma sai Allah ya sa na samu shiga a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’.

“Kuma gaskiya da na shiga shirin ‘Daɗin Kowa’ ban taɓa zata zan yi suna ba kuma sai ga shi Allah ya ɗaukaka ni kuma ina jin daɗi sosai yadda jama’a su ke girmama ni, tun abin ya na ba ni mamaki har ya zama jiki.

“Ko da yake wani lokacin akwai ɓacin rai, don sai ka je waje ka ga mutane sama da ashirin kowa ya na taɓa ka, wannan ya ce ya Adama da sauran jama’ar da mu ke aiki tare ana ta tambayar su To, sai dai ka yi sauri ka bar wajen.”

Mun tambayi Fati ko halin ta ne abubuwan da ta ke yi a cikin shirin?

Sai ta ce, “Gaskiya ni ma abin ya na ba ni mamaki, don sai na ji kamar ba ni ba, don ba hali na ba ne.

“Kuma abin mamaki, sai na ga yara ƙanana su na ƙauna ta saboda rol ɗin da na ke takawa. Kuma har yara su na ɗaurin ɗankwali irin nawa, wai ‘ɗaurin Kyauta’! Sai abin ya ke ƙara ba ni mamaki. “

Fati Nayo ta ce, “Babu wani abu da zan ce sai dai godiya ga Allah, domin ya sa na cimma buri na. Kuma ina godiya ga Allah da wannan nasarar da na samu a rayuwa ta.”

Loading

Tags: Arewa24Daɗin KowaFati NayojarumaKannywoodKyauta DillaliyaMustapha MustySalisu Officertaurari
Previous Post

Ina alfahari da baiwar da Allah ya yi mani a harkar fim – Hadiza Muhammad

Next Post

Mawaƙiya Hajjo Idi Moris ta zama maiɗakin Mika’il

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Hajara Idi Moris a ranar auren ta

Mawaƙiya Hajjo Idi Moris ta zama maiɗakin Mika'il

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!