• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abubuwan da mata masu yabon Annabi ke yi sun fi na ‘yan fim muni – Maryam Fantimoti

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 12, 2022
in Mawaƙa
0
Hajiya Maryam Saleh (Fantimoti)

Hajiya Maryam Saleh (Fantimoti)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR mawaƙiya Hajiya Maryam Saleh (Fantimoti) ta bayyana cewa irin matsalolin da ke faruwa a cikin harkar wakokin yabon Annabi abin sai dai addu’a.

A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, Fantimoti ta ce yanzu mata sun fi shiga cikin wannan harkar fiye da harkar fim.

Sai dai Fantimoti, wadda ke cin tudu biyu, wato waƙoƙin nanaye da na yabon Annabi, ta nuna cewa abin babu tsarin da ya kamata.

Ta ce: “A yanzu mutanen da su ke shiga harkokin waƙe-waƙe sha’awa ce; idan mace ta kalli wata a kan mumbari ta na waƙa, kawai sai sha’awa ta fizgo ta, kawai ta shiga, ba kamar a baya ba da yin waƙar baiwa ce ta ke sa mutum ya shiga.

“Mu Allah ne ya ba mu baiwar waƙar; a jikin mu ta ke. To a yanzu a taro kawai ka tarar ana waƙa wai kai ma daga nan ka zama mawaƙin Annabi!

“To abin da aka rasa a wajen su masu shiga harkokin waƙe a yanzu ba su san waƙa ta na da matakai da dokoki ba. Sai dai su da yake ba su sani ba kuma sha’awa ce ta kawo su, sai ka ga wata ma waƙar ƙawar ta za ta hau ko ba da izinin ta ba, idan an yi mata magana ta ce ai ita ta ba ta izini. 

“Mu a baya ba haka mu ke yi ba; sai mutum ya ba ka izini za ka zama halifan sa ko idan mutum ya mutu a yi taro a naɗa halifan sa. Amma a yanzu ka na da rai sai ka ga halifofin ka sun kai goma ko sama da haka.

Ana taɓa su sai su ce ai halifan wane ne – tun mawaƙin bai mutu ba!

“Ni kai na da na ke yin magana da kai, sai na ji an bugo mini waya an ce, ‘Ai halifiyar ki ce’. Sai na ce, ‘Ni ba ni da halifa, don ni ban taba yin naɗi ba’.

“To, irin abubuwan da su ke faruwa a yanzu kenan. Sai ka ga  mutum ya na da halifofin da bai san yawan su ba. 

Maryam Fantimoti

“Don haka abubuwan da su ke cikin hallara ta yabon Annabi wallahi ba a yin su a cikin waƙoƙin fim na nanaye, saboda kowa ya kwana ya tashi ya san ni Maryam Saleh Fantimoti ina cikin harkar waƙar nanaye, kuma ina cikin harkar yabon Annabi. 

“To abin da ya ke cikin hallara ta yabon Annabi ba ya cikin harkar fim ta nanaye, saboda a nanaye babu yadda za a yi mutum ya ɗauki waƙar ka ya yi amfani da ita ba tare da ka ɗaure shi ba, amma a yabon Annabi sai ka je cikin taro za ka yi waƙar ka sai kawai ka ji wata ta hau ta na yi, ka na yin magana sai a ce ai Annabi ne. To babu yadda za ka yi. To ka ga a wajen babu kare haƙƙin mallaka. Idan ka yi waƙar, mutane goma sai su ɗauka su yi amfani da ita kuma ba ka da ikon ka yi magana, sai a ce Annabi ne.”

Fasihiyar ta yi kira ga matan aure masu shigowa harkokin waƙen yabon Annabi da su riƙa neman izinin mazajen su  haka nan su ma ‘yan mata su riƙa neman izinin iyayen su, “domin ana samun matsaloli irin waɗannan sosai a wannan harkar ta yabon Annabi.”

Loading

Tags: Begecopyrighthaƙƙin mallakaMaryam Saleh Fantimotimawaƙayabon Annabi
Previous Post

KILAF 2022: Mun zo da sabon tsarin bikin finafinai na Afrika – Abdulkareem Muhammad

Next Post

Tsugune ba ta ƙare ba, Gwanja da 442 za su saki sabuwar waƙar ‘Chass’ da su ka yi tare

Related Posts

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta
Mawaƙa

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta

July 15, 2026
Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Next Post
Fostar 'Chass' ta haɗakar mawaƙa Ado Gwanja da Mr. 442

Tsugune ba ta ƙare ba, Gwanja da 442 za su saki sabuwar waƙar 'Chass' da su ka yi tare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!