* Zango ba ɗan Kannywood ba ne, cewar Alhassan Kwalle
DA alama, har yanzu ta na ƙasa ta na dabo tsakanin Adam A. Zango da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, domin kuwa hukumar ta ce har yanzu fitaccen jarumin bai yi rajista da ita ba.
Hasali ma, hukumar ta ce ko kaɗan jarumin bai fahimci dokokin ta ba, don haka ya kamata ya nemi wani ya wayar masa da kai a kan su.
Idan kun tuna, kwanan nan ne Zango ya shelanta cewar ya yi mubayi’a ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, to amma shi har yanzu ba ɗan Kannywood ba ne, kawai dai ya yi rajista ne a matsayin sa na jarumi mai cin gashin kan sa.
Baya ga haka, ya bayyana a wata hira da ya yi da BBC Hausa cewa a kan sa ne hukumar ta fara yin rajistar jarumai, sannan kuma dokokin da hukumar ke yi a kan sa daban ne da na sauran jarumai.
Dangane da waɗannan maganganu ne mujallar Fim ta nemi ƙarin bayani daga bakin shugaban hukumar, Malam Isma’ila Na’abba (Afakallahu), wanda shi kuma ya ce: “Shi Adam A. Zango, sam bai ma fahimci dokokin Hukumar Tace Finafinai ba ne, domin fa har yanzu shi ba ya cikin waɗanda su ka yi rajista da hukumar, kawai dai ya na cikin masu neman hukumar ta yi musu rajista, domin kuwa a yanzu matsayin sa shi ne wanda ya sayi fom.
“Don haka ya zo ya sayi fom ya je ya cika ya dawo mana da shi, kuma har aka shiga hutun aiki saboda (cutar) korona bai cike fom ɗin ba.
“Don haka sai ya dawo mana da fom ɗin mun ga ya yarda da dokokin mu sannan za mu ba shi lasisin yin aiki. Don haka har yanzu a matsayin sa na mai neman a ji masa rajista ya ke.”
Dangane da cewar Zango ya yi rajista ne a matsayin jarumi mai cin gashin kan sa kuwa, Afakallahu ya ce, “To ai bai san dokokin hukumar ba ne, shi ya sa, amma ya duba fom ɗin da ya saya mana ya ga yadda dokokin hukumar su ke.
“Wannan duk wani abu ne da idan ya je cikewa zai gani.
“Amma mu da ya ke bai dawo mana da fom ba, to ba mu san yadda shi ya fahimci dokar ba. Amma dai idan bai sani ba ya kamata ya samu na kusa da shi su karanta masa don abu ne da ya ke a rubuce cikin fom ɗin da ya saya, don haka sai ya duba ya gani.”
A kan batun cewa Zango ne aka fara tantancewa kuwa, Afakallahu ya ce, “Mu a aikin mu, mu na yin abu ne don gyaran tarbiyya, kuma dokokin Hukumar Tace Finafinai da man akwai su tun kafin na zo, kuma ba a yi su ba don wani mutum shi kaɗai.
“Abin da mu ka ce shi ne a bi su. Don haka ba za mu yarda wani ya zo ya karya doka mu zuba ido mu na kallo mu ƙyale shi ba.
“Alƙawari mu ka ɗauka na kare mutunci da addinin mutanen Jihar Kano, don haka idan wani ya zo zai ɓata su dole ne mu ɗauki mataki a kan sa.”
Daga ƙarshe, Afakallahu ya yi kira ga masu sana’ar fim da su fahimci cewar ana son a gyara harkokin masana’antar ne, kuma a cikin aikin gyara duk wanda ya nemi ya karya doka to doka za ta yi aiki a kan sa.
A wani labari mai alaƙa da wannan, shugaban ƙungiyar ‘yan wasan fim ɗin Hausa ta Nijeriya (‘Hausa Actors Guild of Nigeria’), Malam Alhassan Kwalle, ya bayyana cewar mutane su daina kallon Adam A. Zango a matsayin ɗan ƙungiyar su domin har yanzu ba su ma san da zaman sa ba duk da maganganun da ake yaɗawa cewar ya dawo Kannywood.
A cewar sa, har ya yanzu Zango ba ɗan Kannywood ba ne, domin fa bai yi rajista da ƙungiyar ba.
A hirar sa da mujallar Fim kan lamarin, Kwalle ya ce a cikin wannan ƙungiyar ne jaruman Kannywood su ke kuma ƙungiyar ce Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yarda da ita.
Ya ƙara da cewa, “Duk wani ɗan ƙungiyar shi ne cikakken jarumin da hukumar ta yarda ya gudanar da aikin sa, amma shi Adam A. Zango ba shi da rajista da mu har zuwa yanzu.”
Da mujallar ta tambaye shi ko ba ya ganin Zango ya je ya yi rajista da hukumar, sai ya ce, “To ni dai ban sani ba, domin a ƙa’ida duk wani jarumi da Hukumar Tace Finafinai za ta yi wa rajista, sai ya zo ya bi ta ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan fim a ɓangaren da zai yi aiki.
“Kamar darakta, sai ya je ya yi rajista da ƙungiyar daraktoci, haka furodusa; don haka shi ma Adam A. Zango, a matsayin sa na jarumi, dole sai ya na da rajista da ƙungiyar jarumai sannan Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano za ta yi masa rajista.
“Haka dokar ta tsara, kuma har yanzu ba canzawa aka yi ba.
“A saboda haka, Adam A. Zango ba ɗan Kannywood ba ne, kuma har yanzu ba shi da wani hurumi da doka ta ba shi ya gudanar da duk wani aiki na fim a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood.”