• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Addu’ar samun auren mace ta bakwai ta tuno wa mutane auri-sakin da Adam A. Zango ya yi

* Ya yi addu'ar Allah ya ba shi wadda za su yi auren mutu-ka-raba. Masoya sun ce amin

by ALI KANO
April 3, 2024
in Labarai
0
Addu’ar samun auren mace ta bakwai ta tuno wa mutane auri-sakin da Adam A. Zango ya yi

Adam Zango da mata 5 daga cikin 7 da ya aura. Sama zuwa ƙasa: Amina, A'isha, Maryam, Ummukhulsum, da Safiyya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ADDU’AR neman macen aure ta bakwai da jarumin Kannywood Adam A. Zango ya wallafa a ranar Talata ta tuno wa da mutane irin halayyar sa ta auri-saki, a yayin da da dama su ke taya shi addu’ar Allah ya sa ya dace.

Zango, wanda yanzu haka gwauro ne, ya nemi jama’a da su saka shi a addu’a don samun matar da zai aura don alfarmar wannan wata na Ramalana, a wani saƙo na musamman da ya wallafa a Instagram.

Jarumin ya wallafa fosta ne mai ɗauke da kalamai kamar haka: “Don Allah ku saka ni a addu’ar ku Allah ya bayyana min matar da zan aura a cikin wannan wata mai albarka, daren lailatul ƙadri. Matar da zan yi alfahari da ita duniya da lahira. Allah ya sa mutuwa ce kaɗai za ta raba ni da ita.”

Saƙon ya jawo ka-ce-na-ce domin da yawa sun tuno da yadda jarumin ya yi ƙaurin suna wurin auri-saki, domin kuwa zuwa yanzu ya auri mata har shida, waɗanda ya saki.

In ban da tsohuwar jaruma Maryam A.B. Yola, kowace daga cikin matan nan ta haifi ɗa da shi.

Wakilan mujallar Fim sun lissafa matan tare da bayyana haihuwar da su ka yi da jarumin kuma mawaƙi, kamar haka:

  1. Amina Uba Alhassan (Amina Rani), wadda a yanzu ta na ɗaya daga cikin jarumai mata da tauraron su ke haskawa, ita ce matar sa ta farko, kuma ita ce mahaifiyar babban ɗan sa Haidar. Ya aure ta a Kaduna a cikin 2006.
  2. Bayan ya rabu da Amina sai ya auri ‘yar’uwar sa ta jini, A’isha Mukhtar, daga garin Shika da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Ta haifa masa ‘ya’ya uku – maza biyu, mace ɗaya, wato Khalifa, Sultan da Mubeena.
  3. Mace ta uku da ya aura wata jarumar Kannywood ce ‘yar Jihar Nassarawa mai suna Maryam. Ita ce ta haifa masa Ameer, wanda sunan sa na yanka Adamu.
  4. Da ya rabu da Maryam sai ya auro jarumar fim ɗin ‘Nas’ da su ka fito tare, wato Maryam A.B. Yola, daga Abuja, a cikin 2013. Ita kaɗai ce su ka rabu babu haihuwa a tsakani.
  5. Da ya saki Maryam sai ya tsallaka zuwa ƙasar Kamaru a cikin 2015, inda ya auro Ummukhulsum, wata yarinya Bafillatanar daga garin Ngaoundere. Ita ce mahaifiyar ɗiyar sa mace ta farko, wato Murjanatu. Zango na tare da Ummukhulsum ne ya saki ‘yar’uwar sa A’isha a lokacin ta na da cikin Mubeena, ya koma mai mace ɗaya. Bayan wani lokaci da ya koma Kano kasancewar babu ayyukan shirin fim sosai a Kaduna, ita ma ya sake ta a can.
  6. Zango ya na zaman gwauro sai ya samu Safiyya Umar Chalawa daga Birnin Kebbi, aka ɗaura auren su a a ranar 26 ga Afrilu, 2019. Ana ganin cewa daga kan ta ba zai ƙara sakin mace ba, domin ya yi wa iyayen ta alƙawarin ba zai taɓa sakin ta ba. To amma tun ta na amarya ya yi mata saki na farko.

Safiyya ta haifa masa Furaira, wadda da yake sunan mahaifiyar sa ne ya raɗa mata, sai ake mata laƙabi da Diana. Ita ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan sa (maza huɗu da mata uku).

Kwatsam , a cikin Afrilu 2023 Zango ya yi wa Safiyya saki na biyu. Sun yi zaman aure na shekara huɗu. A lokacin ta shafe watanni biyar ta na zaman yaji a Birnin Kebbi. Yanzu haka ta na zawarci.

Mai mata biyu: Zango da uwargida A’isha (a dama) da amarya Ummukhulsum

A watan gobe ne dai jarumi zai cika shekara ɗaya cur bai da aure duk da yake ana raɗe-raɗi a bayan fage kan soyayyar da ya ke yi da wasu matan da ake hasashen ko zai auri ɗaya daga cikin su ne.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda ya yi soyayya mai zafi da jaruma Meerah Shu’aibu kamar za a yi aure, amma sai aka ji shiru kamar an aiki bawa garin su. Ashe sun rabu.

Meerah ce ake zargi da zama ummulhaba’isin rabuwar sa da Safiyya.

Addu’ar Adam A. Zango a Instagram jiya

Sakamakon addu’ar da ya tura a Instagram jiya, mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su; wasu na cewa ai mai hali ba ya barin halin sa, wasu kuma na cewa rashin riƙe aure ba laifin sa ba ne, laifin matan ne.

Shi kan shi Zango a kullum cewa ya ke yi laifin matan ne, har ma ya taɓa yin alƙawarin cewa idan har ya rabu da Safiyya, to shi da ƙara aure haihata-haihata.

Idan kun tuna, a cikin 2023 ya wallafa wani guntun bidiyo a Tiktok inda ya yi bayani kan rikicin auren sa da Safiyya, wadda a lokacin ta yi yaji. A bidiyon, Zango ya bayyana cewa ya san irin kallon da mutane su ke yi masa na aure-aure, har ya sha alwashin in dai har auren sa da Safiyya ya mutu to ba zai ƙara yin aure ba har abada.

A bidiyon, mai tsawon minti uku, jarumin ya ce: “Ina ganin na gama aure. Da izinin Allah na gama aure, kuma ina roƙon Allah ya kare ni daga dukkanin abubuwan da na ke gujewa ya sa na ke ta yin wannan auren.

“Daga na rabu da mace in sake yin wani auren, wanda in mutum ya zama maɗaukaki, zai dinga ganin irin waɗannan abubuwan da za su dinga bin shi. Idan mutum ba imani ne da shi ba ko kuma ya na addu’a da dauriya, sai ya kauce hanya.

“Kada mutum ya koma ya dinga bin ‘yan mata da sauran su, wanda hakan ya sa ina rabuwa da mace na ke sake yin auren saboda in kauce wa wannan hanyar.”

Mujallar Fim dai ta lura da cewa Adam A. Zango ya goge rubutun da ya yi a Instagram jiya. Irin hakan da ma tsohuwar ɗabi’ar sa ce, wato ya ɗora abu a soshiyal midiya, zuwa wani lokaci kuma ya goge, musamman idan al’amari ne da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Loading

Tags: Adam A. Zangoaddu'aaureauri-saki
Previous Post

Yau Laraba za a yi addu’ar ukun rasuwar mahaifin Muhibbat Abdulsalam

Next Post

Gwamnatin Kano ta hana shirya fim kan daba ko ‘yan daudu

Related Posts

Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Next Post
Gwamnatin Kano ta hana shirya fim kan daba ko ‘yan daudu

Gwamnatin Kano ta hana shirya fim kan daba ko 'yan daudu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!