HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana haramcin shirya fim da ake faɗan daba da kuma nuna daudanci.
Hukumar ta yanke wannan hukunci ne a yau Laraba, bayan ganawar da Babban Sakataren hukumar, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ta Alhaji Abba El-Mustapha, ya yi da manyan ma’aikatan hukumar.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne wanda ya ba sanarwar haka a wani saƙon manema labarai da ya fitar.
Malam Abdullahi ya ce, “Biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’umma ke yi a kan shirya finafinan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a Jihar Kano, Shugaban Hukumar Tace finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ba da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan finafinan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a faɗin Jihar Kano.”
El-mustapha ya ba da wannan umarni ne a yau jim kaɗan bayan wata ganawa da ya yi da manyan ma’aikatan hukumar tare da wasu daga cikin wakilan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood waɗanda su ka haɗa da da ƙungiyoyin MOPPAN, Arewa Film Makers, daraktoci da kuma furodusoshi.

Babban sakataren ya ƙara da cewa, “Doka ce ta ba wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani fim da ta ke ganin ya ci karo da tarbiyya tare da al’adar al’ummar da ke jihar.
“Saboda haka tuni lokaci ya yi da za a saka ido don ganin irin waɗannan gurɓatattun finafinai ba su ci gaba da yaɗuwa a cikin al’umma ba.
El-mustapha ya gode wa ‘yan Kannywood dangane da haɗin kai da kuma goyon bayan da su ke ba hukumar a ko da yaushe.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar kan irin haɗin kan da su ke ba hukumar, musamman na sanar da ita duk wani abu da su ke ganin ya saɓa wa al’ada da tarbiyyar addinin Musulunci.
El-mustapha ya kuma yi alƙawarin ci gaba da barin ƙofar sa a buɗe domin karɓar shawarwari ga duk wanda su ke da buƙatar hakan.
A ƙarshe ya ba masu shirya irin waɗannan finafinan damar wata ɗaya da su gyara ayyukan su kafin doka ta fara aiki gadan-gadan a kan su.
![]()







