ALLAH ya kyauta makwanci! ‘Yan watanni kaɗan da su ka wuce na kirawo wani abokin mu wanda makusanci ne ga Alhaji Bashir Tofa, wanda kuma shi ne sanadiyyar alaƙar mu da shi, na roƙe shi cewa, “Don Allah ina so ka isar da wannan saƙon ga Alhaji Bashir Tofa cewa na san shi a matsayin ƙwararren marubuci da ya yi rubuce-rubuce masu ɗimbin yawa da kuma fa’ida. Ina so ya rubuta tarihin rayuwar sa da kan sa, kada sai bayan ya rasu a rubuta. Ina ganin za a fa’idantu ƙwarai da gaske. Ina son rubutun ya ɗauki salo irin na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Dakta Isma’ila Tsiga ya taimaka masa wajen rubuta littafin ‘Where I Stand’, aka fassara shi zuwa ‘Manufata’ yadda shi da kan sa ya faɗi cikakken tarihin sa, wanda ba shakka salo ne da ke bada cikakken tarihi da faɗi-tashi da gwagwarmaya yadda al’umma za su karanta tarihin kai-tsaye daga bakin mai shi.”
Wannan abokin namu ya yi mini alƙawarin zai isar da wannan saƙon, amma kwatsam ba zato ba tsammani sai na ji labarin rasuwar wannan shahararren mutum da ke da abin faɗa a rayuwar sa. Ina roƙon Allah ya jiƙan Alhaji Bashir Othman Tofa.
A lokacin da za a ƙaddamar da littafan sa da ya rubuta, ya faɗa a wata hira da aka yi da shi cewa Allah ya taimake shi a rayuwar sa ya yi abubuwa guda uku waɗanda kowanne ya na zaman kan sa ne, watau ba wanda ke da alaƙa da wani: shi marubuci ne, kuma ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa.
Ban san wani mutum da Allah ya yi masa baiwar haɗa waɗannan abubuwa guda uku a lokaci guda ba a wannan lokacin. Kamar yadda tarihi ya nuna, mutane ƙalilan ne Allah ya ke masu baiwar haɗa abubuwa masu yawa, kuma duka su yi fice a cikin su. Misali, Shehun Borno Muhammad Al-Amin El-Kanemi, Allah ya yi masa baiwar sarauta, shi hamshaƙin basarake ne, a lokaci guda kuma malami ne, alaramma, gangaran na Alƙur’ani.
Sai Khalifa Ishaƙa Rab’iu, Khadimul Ƙur’an, wanda alaramma ne, gangaran, kuma malami Khalifan Tijjaniyya, kuma shahararren ɗan kasuwa da Allah ya yi masa ɗimbin dukiya.
Ga kuma Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda Allah ya hukunta masa hawa karagar sarautar Kano a matsayin Sarkin Kano na goma sha huɗu, a lokacin kuma malami masanin addini da zamanin sa.
Waɗannan mutanen da na ambata misali ne na waɗanda Allah ya haɗa masu baye-bayen sa fiye da ɗaya. Alhaji Bashir Tofa Allah ya yi masa karimci da abubuwa guda uku da mu ka ambata a sama.
Alhaji Bashir Tofa jarumi ne mara tsoro, domin duk girman ka ya na iya faɗa maka gaskiya ba tare da jin tsoron ka ba
Na san Bashir Tofa tun lokacin da ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya. A lokacin ina sakandire, amma na samu alaƙa da shi ne ta sanadiyyar rubutun littafin fassarar ‘Tafsirin Ibn Kathir’, wanda ya nuna sha’awa da kulawa ƙwarai da gaske a kan wannan rubutun. Bashir Tofa ya damu ƙwarai da gyaruwar wannan al’ummar tamu, kuma ya na cike da baƙin cikin yadda al’ummar mu ta kasa samun saiti. Na daɗe ban ga mutumin da ke son taimaka wa al’ummar mu domin tsamo ta daga kwarin da ta faɗa, amma abin ya gagare shi kamar Bashir Tofa ba.
Alhaji Bashir Tofa jarumi ne mara tsoro, domin duk girman ka ya na iya faɗa maka gaskiya ba tare da jin tsoron ka ba. Akwai wani labari da ya ba mu da ke nuna rashin tsoron sa, amma dai na sa shi a mala.
Haka nan kuma bayan Khalifa Ishaƙa Rabi’u da na gani, ban ga mutumin da Allah ya yi masa ɗimbin dukiya da ta ke a hannun sa ba a zuciyar sa ba kamar Bashir Tofa. Ya na iya yin kyautar da ta wuce misali ba tare da ya waiwaye ta ba. Shi ne mutumin da ya tara abokan sa a ƙoƙarin sa na ganin sun zama masu arziki kamar yadda Allah ya ba shi arziki, ya ba su kyautar kuɗin da a yanzu kuɗi ne na yanke talauci. Ni da kai na ya taɓa yi min tayin zai ba ni kuɗi kimanin naira miliyan goma ta wancan lokacin.
Wani misali da ke nuna yadda dukiyar sa ba ta daɗa shi da ƙasa ba, wani aboki na da ya san alaƙar mu da Bashir Tofa ya nemi da na haɗa shi da shi domin ya ba su aron wani gidan sa da ke Abuja, a guri mafi daraja. Sai na ce matsayi na bai kai yadda zan iya neman wannan alfarmar a gurin sa ba, amma akwai mutumin da na san ya na da kusanci da Bashir Tofa da komai zai iya nema a gurin sa, ni kuma malami na ne, don haka na sanya aka yi masa magana. Kai-tsaye mu ka je mu ka same shi mu uku. Mu na faɗa masa, ya ce wannan ai ƙaramin aiki ne a wajen Bashir Tofa, amma dai ya san an sanya gidan a kasuwa, har ya yi mini wasa ya ce, “Malam Aliyu ai kuɗin gidan ba shi da yawa, ko za ka biya? Naira biliyan ɗaya ne kacal!” Mu ka yi dariya.
Ina tsammanin domin tabbatarwa, sai ya buga masa waya, kuma ya buɗe wurin jin magana kai-tsaye domin mu ji maganar da za su yi. Abin sha’awa a lokacin ya fito ne daga Harami. Bayan sun gaisa, su ka yi wasu maganganun su da su ka shafe su, sannan ya ce, “Wasu mutane na ne su ke so a ba su aron wannan gidan da ke guri kaza.” Sai ya ce, “Ai ka san an sanya shi a kasuwa, ba don haka ba ai da sai a ba su.”
Wannan kalmar ta ba ni sha’awa, kuma ta tsaya a rai na, cewa za a iya bada aron guri mai wannan matuƙar daraja, ba tare da an ji ko wane irin abu ba.
Bashir Tofa ya rasu ya bar babban giɓin da zai yi wahala wajen cike shi. Mu na roƙon Allah ya yi jinƙai a gare shi, ya saka masa da alheri bisa kyawawan ayyukan da ya gabatar a rayuwar sa, ya jiɓinci bayan sa. Allah ya hakurkurtar da al’ummar mu, ya ba ta makwafin sa. Allah ya ba mu ikon kwaikwayo da ayyuka nagari.
![]()







