ƘARSHEN tika-tika, tik! Fitattun ‘yanbiyun nan mawaƙan hip-hop, Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar (waɗanda ake kira da Tagwayen Asali), sun auri wasu tagwayen Katsinawa a jiya.
An ɗaura auren tagwayen masu kama ɗaya da kuma wasu tagwayen masu kama da juna a jiya Asabar, 8 ga Janairu, 2022 a gidan Alhaji Bawa Mechanic da ke Titin Kaduna, Unguwar Tsamiya, a Dutsin-ma, Jihar Katsina, a kan sadaki N100,000.

Hassana Abdu Bawa ta auri Hassan Sani Abubakar yayin da Hussaina Abdu Bawa ta auri Hussaini Sani Abubakar.
A daren jiya ɗin an shirya ƙasaitacciyar dina a ‘Amani Event Centre’ da ke daura da Prince Hotel a unguwar Nassarawa GRA, Kano.
‘Yan fim da mawaƙa irin su Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, Hafsat Shehu, Hamisu Breaker, Fresh Emir, Ado Gwanja, Rabi’u Dalle da sauran su sun halarta.
Tagwayen Asali sun nuna godiyar su ga Allah game da wannan rana ta farin ciki a gare su, inda su ka ce, “Wannan rana babbar rana ce a gare mu wadda bai za mu taɓa mantawa da ita ba, kasancewar mun daɗe mu na jiran wannan lokaci, wanda kamar wani abu ne da ka saka a ran ka kuma ka ke tunanin ba zai yiwu ba, cikin ikon Allah, Allah ya tabbatar da shi.

“Wannan ya sa mu ke murna ƙwarai da gaske. Mu na murna, murna, mu na murna! Allah ya sanya mana albarka a tarayyar mu ta aure. Allah ya sa kowa ya koma gida lafiya. Mun gode ƙwarai da gaske.”
Can a cikin shekarar da ta gabata dai an yaɗa wasu hotuna na Tagwayen Asali da waɗannan ‘yanbiyun mata, ana nuni da cewa za su auri matan. Amma a lokacin da mujallar Fim ta tuntuɓi Tagwayen Asalin kan batun, sai su ka kada baki su ka ce ba aure ne za su yi ba, aikin waƙoƙin su ne kurum su ka yi da su, amma auren nasu na nan zuwa ba da jimawa ba.

Yanzu Allah cikin ikon sa ya cika masu burin su, sun auri kyawawan ‘yanbiyu masu kama ɗaya kamar su. To, Allah ya bada zaman lafiya, amin.