AN tara aƙalla naira miliyan 14 a wajen taron ƙaddamar da wasu littattafai biyu na marubuciya Hajiya Fatima Ibrahim Abba Gana shekaranjiya Asabar, 8 ga Janairu, 2022 a Kaduna.
Marubuciyar ta rubuta littattafai biyu na hikaya masu suna ‘Raƙiba’ da ‘Karima’, waɗanda kamfanin buga littattafai na Gidan Dabino, Kano, ya wallafa. Yayin da ‘Raƙiba’ na da shafi 447, ‘Karima’ kuma na da shafi 87.
A taron, wanda aka gudanar a Hotel Seventeen, an bayyana cewa babban mai ƙaddamarwa, Talban Bauchi, Alhaji Tahir Ibrahim Tahir, wanda bai samu damar halarta ba, ya aiko da saƙon zai bada naira miliyan 5 a kan kwafe biyar-biyar na littattafan.

Mataimakin babban mai ƙaddamarwa, Alhaji Shamsudeen MD Yusuf (Bulaman Zazzau), ya aiko da saƙon ya bada naira miliyan 2, sannan ɗaya daga cikin manyan baƙi, Alhaji Umaru Ƙwairanga (Sarkin Fulanin Gombe), shi ma bai zo ba amma ya aiko da saƙon zai bada naira miliyan 1.
Wasu da su ka ƙaddamar da littafin su ne tsohon Ministan Wutar Lantarki, Dakta Muhammed Wakil (naira miliyan 2), Alhaji Abubakar Sadiq Abubakar (Lihiddan Gusau) wanda kwamishina ne a hukumar RMFC da ke Abuja (naira miliyan 1), sai kuma tawagar wasu jami’ai daga Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA) da su ka halarci taron a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammad Kudu Abubakar, sun bada N50,000.
Bugu da ƙari, Alhaji Muhammed Ibrahim Kuchi ya bada N100,000, Shugaban Bankin Taj, Hamid Joɗa, ya bada N100,000, Hajiya Aisha Musa ta Bankin Wema ta bada N100,000, yayin da Sarkin Mawaƙan Dutse, Alhaji Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya bada N20,000 lakadan.
Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa yawancin kuɗaɗen da aka bayyana bayarwa duk na alƙawari ne, wato waɗanda ake sa ran za a biya daga baya, domin kuwa tsabar kuɗi da aka tara ba su fi N400,000 ba.
Mai sharhi kan littattafan dai shi ne Farfesa Ibrahim Yakasai, wanda ya yi bayani kan abin da kowane littafi ya ƙunsa, kuma ya jinjina wa marubuciyar bisa ƙoƙarin da ta yi. Haka kuma ya nuna wasu wurare inda aka samu kurakurai a littattafan.
Bugu da ƙari, ya yi nuni da cewa akwai muhimmanci littafin ya samu shiga a wajen masu karatu, don haka ya kamata mutane su nema su karanta.
Shugaban kwamitin shirya ƙaddamarwar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ma ya yi jawabi kan littafin da kuma ƙoƙarin marubuciyar.
Marubuciyar littafin ta yi jawabin godiya ga mahalarta da ‘yan kwamitin shirya taron cikin harshen Hausa da Turanci, inda ta yi fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.
Taron ya yi armashi matuƙa, musamman yadda aka tsara shi, sannan Ala ya gabatar da wasu sanannun waƙoƙin sa irin su ‘Bakan Dabo Sankano’ da ‘Jami’a Gidan Ban-kashi,’ sannan kuma ya yi wa marubuciyar wata sabuwar waƙa ta musamman.
Mahalarta taron sun haɗa da Ado Gidan Dabino, Aminu Ala, Muhammad Kudu Abubakar, Abubakar Yusuf Ladan, Hajiya Binta Abba Gana, Hajiya Halima K/Mashi, Mariya Durumin Iya, Bilkisu Yusuf Ali, Hauwa Lawan Maiturare, Ummi Abba Gana, Mudan Gidan Dabino, da sauran su.

Ita dai Hajiya Fatima Abba Gana, wadda ‘yar Kanuri ce daga Jihar Borno, an haife ta a Kaduna. Ta samu digirin Ƙididdigar Kuɗi daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ta yi aiki a wasu bankuna.
Ita ce babbar ɗiyar fitaccen ma’aikacin rediyo da talbijin ɗin nan, marigayi Alhaji Ibrahim Abba Gana, wanda ya yi aiki a gidan rediyon BBC, FRCN da gidan talbijin na NTA, sannan fito a matsayin Waziri a cikin diramar ‘Magana Jari Ce’ da tashar NTA ta riƙa nunawa a shekarun baya; a taron an ma gabatar da wani guntun bidiyo mai nuna tarihin mahaifin nata da aikin wasan kwaikwayo da ya yi.
Fatima, wadda mazauniyar Abuja ce, memba ce a ƙungiyar marubuta ta Alƙalam da ke da Kaduna.



![]()







