• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ali Nuhu: Ni da mahaifiya ta

by DAGA IRO MAMMAN
September 21, 2021
in Tattaunawa
0
Ali Nuhu: 'Mahaifiya ta, Hajiya Fatima Kardiram Digirema, ta rasu a shekarar da na fara fim'

Ali Nuhu: 'Mahaifiya ta, Hajiya Fatima Kardiram Digirema, ta rasu a shekarar da na fara fim'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BA kasafai Ali Nuhu ya ke yin magana game da iyayen sa ba. Har yau ba a ga inda ya yi hira da ‘yan jarida a game da mahaifin sa ba, wato Mista Nuhu Emmanuel Poloma, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 8 ga Yuni, 2020, ya na da shekara 79.

To amma ya taɓa yin doguwar hira game da mahaifiyar sa, Hajiya Fatima Kardiram Digirema, wadda ta rasu a cikin 1999 – yau shekara 21 kenan. Idan kun tuna, haruffan farko na sunan ta ne Ali ya ɗauka ya raɗa wa kamfanin sa suna, wato ‘FKD Productions’. 

 Ali ya yi wannan hirar ne da wakiliyar jaridar SUN wadda ake bugawa a Legas mai suna Bolatiti Adebayo, aka buga ta a ranar 22 ga Yuni, 2017, wato shekara uku da su ka gabata kenan. A ciki, ya bayyana abubuwan da ya kan tuno game da mahaifiyar tasa, musamman irin tarbiyyar da ta yi masa da yadda ta ba shi goyon baya da zai shiga harkar fim da kuma halayen ta na ƙwarai a cikin al’umma. 

Tun da farko, sai da wakiliyar jaridar ta yi wa masu karatu gabatarwa, ta ce: “Ali Nuhu shi ne sarkin Kannywood kuma ya yi fice wajen iya wasan fim. Ya fito a finafinan Hausa da na Turanci sama da ɗari. Wannan jarumin Kannywood mai ɗimbin masoya ya na daga cikin ‘yan fim da su ka cimma nasara a arewacin Nijeriya. Bugu da ƙari, Ali Nuhu furodusa ne, darakta kuma marubucin fim.” 

Wannan hira muhimmiya ce, kuma ba ta tsufa. Ganin cewa kwanan nan mahaifin Alin ya rasu, mujallar Fim ta fassara maku hirar domin samun ƙarin haske game da wannan shahararren jarumi, mai basira, wanda Allah ya yi nasibin masoya da kuma arziki, kamar haka:

TAMBAYA: Ya sunan mahaifiyar ka? 

ALI NUHU: Sunan mahaifiya ta Fatima Kardiram Digirema kuma ‘yar asalin ƙauyen Bamam a Jihar Borno ce.

TAMBAYA: Ita mecece?

ALI NUHU: Malamar makaranta ce, sannan ta zama hedimasta, daga baya kuma ta yi sana’ar saida abinci. 

TAMBAYA: Me ka fi saurin tunawa game da ita? 

ALI NUHU: Kai! Akwai abubuwa da dama da na ke jin daɗin tunawa game da ita. Misali, ita kaɗai ce ta ba ni ƙwarin gwiwar in shiga harkar dirama. Na tuna lokacin da na fara faɗa mata cewa ina so in zama ɗan wasa; sai ta ce ya na da kyau ai, kuma in shiga kawai. Ganin cewa ni mai yawan son kallon talbijin ne tun ina ƙarami, ina jin shi ne ya sa ta ga cewa abin da na ke so kawai in yi kenan, don haka ta ba ni cikakken goyon baya. Sai dai kash! Allah ya yi mata rasuwa a shekarar da na shiga harkar dirama.

TAMBAYA: Me ya same ta?

ALI NUHU: Rashin lafiya ta yi. Kin san abin da mu ke magana kenan tun da fari; tsarin asibitocin mu ba haka ya kamata ya kasance ba. Rashin lafiya ta yi ta rasu.

TAMBAYA: An kai shekara nawa yanzu?

ALI NUHI: Abin ya faru a cikin 1999. Yanzu shekara goma sha takwas kenan.

TAMBAYA: Wace shawara ta taɓa ba ka wadda ba za ka iya mantawa da ita ba?

ALI NUHU: Abin da na ke yawan tunawa shi ne ta faɗa mani cewa a duk inda na je kuma ko da wa na yi hulɗa, to, in zauna lafiya da su. Abu na farko da ta faɗa mani kenan. Na biyu, ta ce in kasance mai ƙasƙantar da kai, sannan na uku a duk irin yanayin da na samu kai na a ciki to in riƙa tunawa da Allah a ko da yaushe. 

Ali Nuhu tare da matar sa Maimuna Garba Ja Abdulƙadir da ‘ya’yan su, Fatima da Ahmad

TAMBAYA: Wane irin abinci da ta dafa ka fi so ka ci?

ALI NUHU: Tuwon shinkafa. Abincin mu ne na gargajiya.

TAMBAYA: Lokacin da ka fara girma, menene ya fi janyo matsala tsakanin ka da ita?

ALI NUHU: To, a gaskiya lokacin da na fara girma, babbar matsala ta da ita ita ce a duk lokacin da na ce ta saya mani wani abu, ita kuma ta ƙiya, to na kan rinƙa yi mata rigingimu, wanda hakan na sanya ta ta yi fushi sosai. Hasali ma dai, akwai lokacin da ta fara kira na da sarkin rigima. Har ma ta taɓa sawo mani riga tishat daga Amerika wadda a jikin ta aka rubuta “ALI – Official Trouble Maker”, wato Ali Sarkin Rigima! (dariya).

TAMBAYA: Mahaifiyar ka ta yi ilimi, amma ka san cewa mata da yawa a wancan zamanin ba su yi ba. Ita ya aka yi ta yi sa’ar tsallakewa?

ALI NUHU: Haka ne, mahaifiya ta ta yi karatu. Lokacin da mahaifin ta ya rasu, sai mahaifiyar ta ta auri wani mutum, sannan ita sai aka kai ta gidan kakan ta, wanda babban gida ne.To, saboda baban ta ya rasu, lokacin da ‘yan mishan su ka zo ɗaukar ‘yan makaranta sai aka haɗa har da ita da yara maza da ke gidan. Sauran yaran mata babu wadda aka ɗauka, sai ita kaɗai. Allah ya taimake ta, ta na da ƙoƙari sosai, don haka sai ta burge mata daga cikin ‘yan mishan ɗin. Matar ta yi sha’awar ganin ƙwazon ta, don haka ta ci gaba da ba ta ƙwarin gwiwa har dai ta gama karatun ta. Daga baya, ta samu aikin koyarwa a wata makarantar firamare inda ta dinga samun ƙarin girma har dai ta zama ita ce hedimasta.Kwanan baya ma ɗaya daga cikin ɗaliban da ta koyar ya kira ni ya ce mani, “Ya kamata ka yi alfahari da mahaifiyar ka. Mahaifiyar ka macen kirki ce; ka je ‘YAWA Special Primary School’ a yau ɗin nan, za ka ga sunan ta a kan allon da aka rubuta sunayen mutanen da su ka jagoranci makarantar.”

TAMBAYA: Lokacin da ka fara girma, me mahaifiyar ka ta faɗa maka game da ‘yan mata?

ALI NUHU: Na tashi a cikin mutane masu yaruka da addinai daban-daban. Kamar “garin ka-zo-na-zo” ne. Akwai Ibo, Yarabawa, Igala, Barebari, da Hausawa, kuma duk ana zaune kamar ‘yan gida ɗaya ne. Don haka mun tashi tare da ‘yan matan kamar dai ‘yan babban gida guda ɗaya. Ba zan iya tuna wani lokaci ƙwaya ɗaya da ta ba ni wata shawara kan ‘yan mata ba, amma dai na san ta gargaɗe ni game da shan taba domin ina da wani ɗan’uwa wanda ya ke yawan zuƙar taba, ta ce, “Don Allah, don Allah kada ka zama kamar shi.”

TAMBAYA: Za ka so a ce da ma ta na da rai a yau? 

ALI NUHU: Sosai ma kuwa zan so hakan. Kin san a yau Allah ya albarkace ni, kuma ina matuƙar gode masa. Na so a ce ta na nan don ta ci moriyar shukar da ta yi.

TAMBAYA: Me ka ke tunanin za ta yi in da a ce ta na tare da kai a yau?

ALI NUHU: Mace ce mai kirki da ƙaunar jama’a, wadda ba ta da ɓoye-ɓoye, kuma ta kan yi bakin ƙoƙarin ta wajen taimakon mutane ko da ita za ta cutu. Misali, za ki iya zuwa wajen ta da wata matsala kuma ba ta kuɗi da sosai, to sai ta ɗauka ta ba ki don hankalin ki ya kwanta. Haka Allah ya yi ta.

TAMBAYA: Me ka ke ganin ka gada daga wajen ta? 

ALI NUHU: Haka ne, abin da na fi gani a zahiri wanda hatta ‘yan’uwa na na jini su ke gaya mani shi ne mutane na so na kamar yadda mutane ke son ta, saboda kamar uwa ce ga kowa a layin mu. Ta kan dafa abinci ta ba duk wanda ya zo gidan mu ya ce mata, “Mama, ina jin yunwa.” Yawancin matasan layin mu kan taru a gidan mu, kuma ni ma haka ya ke faruwa da ni a yau. Yawancin matasa su kan zo su kewaye ni. Su na zama da ni, kuma na yi sa’ar samun mata wadda ta ke da fahimta ƙwarai da gaske.

Loading

Previous Post

Gwamnatin Kano ta haramta shirya fim kan kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya

Next Post

Sani Ciyaman, shugaban mawaƙan Kaduna, ya kwanta dama

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Marigayi Alhaji Sani Ciyaman Ɗangiwa

Sani Ciyaman, shugaban mawaƙan Kaduna, ya kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!