• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ali Nuhu ya taya maiɗakin sa murnar ranar haihuwa

by DAGA ABBA MUHAMMAD
January 1, 2023
in Ranar Murna
0
Ali Nuhu ya na taya Maimuna yanka kek ɗin murnar zagayowar ranar haihuwar ta

Ali Nuhu ya na taya Maimuna yanka kek ɗin murnar zagayowar ranar haihuwar ta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI kuma darakta a Kannywood, Ali Nuhu, ya taya matar sa Hajiya Maimuna Garba Ja Abdulƙadir murnar ƙara shekara a rayuwar ta.

A yau Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 Alin ya ɗora kyawawan hotunan da su ka ɗauka a wurin taron ‘get-together’ da ya shirya mata tare da ‘yan’uwan su da ‘ya’yan su Fatima da Ahmad a Instagram. 

Sannan ya yi rubutu da Turanci a ƙasan hotunan, ya ce,  “Happy birthday to my lovely wife as the New year begins. May Allah make our bond stronger, guide and protect us, ameen.”

Bayan haka, Ali Nuhu ya yi amfani da wannan rana ya yi juyayin aminin sa, jarumi Ahmed S. Nuhu, wanda ya cika shekara shida cur da rasuwa.

Duk shekara abokan sa’ar Ahmed su na tunawa shi, su na ɗora hotunan sa a soshiyal midiya tare da yi masa addu’a, sannan su na nema masa addu’a da masoyan su.

Maimuna Garba Ja Abdulƙadir a gaban kek ɗin ta

A yau Ali ya ɗora hoton shi tare da marigayi Ahmed, ya rubuta cewa, “Allah ya jaddada rahama a gare ka Ahmad. Mu na barar addu’a yau shekara 16 da rasuwar ka Ahmad S. Nuhu.”

Kamar yadda mujallar Fim ta ba da labarin, Ahmed, wanda a lokacin rayuwar sa an ɗauka ɗan’uwan Ali ne na jini, ya rasu a ranar Litinin, 1 ga Janairu, 2007 a kan hanyar sa ta zuwa Maiduguri, a daidai Azare, sanadiyyar haɗarin mota tare da abokan sa Abubakar Didos, Hamza da kuma Ahmad Singa Boy. Shi Singa Boy shi ne kaɗai ya rayu a cikin su.

Allah ya jiƙan su da rahama, amin.

Maimuna da Ali za su yanka kek
Soyayya mai daɗi: Ali Nuhu da Maimuna
Ali Nuhu da iyalin sa. A hagu, yayar sa ce, Hajiya Amina
Rai baƙon duniya! Marigayi Ahmed S. Nuhu (a hagu) da Ali Nuhu

Loading

Tags: Ahmed S. NuhuAli NuhuaurejuyayiMaimuna Garba Ja Abdulƙadirmutuwaranar haihuwa
Previous Post

Jarumin Kannywood Ahlan ya bayyana shauƙin rashin mahaifiyar sa

Next Post

Bilal ‘Lion’ zai fara buɗe ƙofar yin aure a Kannywood a bana

Related Posts

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar
Ranar Murna

Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar

December 16, 2024
Next Post

Bilal 'Lion' zai fara buɗe ƙofar yin aure a Kannywood a bana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!