A YAU Juma’a, 17 ga Maris, 2023 aka ɗaura auren darakta a Kannywood, wato Kamal Sani Alƙali da kyakkyawar amaryar sa, jaruma Hauwa Shu’aibu Garba.
An ɗaura auren su da misalin ƙarfe 1:00 na rana, bayan idar da sallar Juma’a, a masallacin Juma’a da ke Titi na 19, Shagari Quarters, Kano.

Wasu daga cikin ‘yan fim da mujallar Fim ta gani a wajen ɗaurin auren sun haɗa da Ali Nuhu, Isma’ila Na-Abba (Afakallahu), Abdul Amart, Rabi’u Rikadawa, Nura Mado, Sani Sule Katsina, Sadiq Mafia da Sulaiman Costume.
Yanzu dai Kamal ya zama mai igiya biyu kenan.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

