A YAU Asabar, 17 ga Satumba, 2022 aka ɗaura auren fitaccen mawaƙi Musa Muhammad (Ɗan Musa Gombe) da masoyiyar sa Salma Abdulazeez Chado.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 10:00 na safe a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa, a birnin Kano.

‘Yan fim da dama sun halarta, irin su Ali Nuhu, Abdul Amart, Lawal Ahmad, Sadiq Sani Sadiq, Auta Waziri, Ado Isa Gwanja, Yunusa Mu’azu, Salisu S. Fulani, Malam Charki da sauran su.
Kafin wannan ranar an yi shagulgula kamar su Ranar Fulani, ƙwallon ƙafa, kamu da kuma dina.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.



