A YAU aka ɗaura auren A’isha Ibrahim Yusuf, ‘yar jarumar Kannywood, Asma’u Sani, bayan kwana uku da aka shafe ana shagulgulan bikin a Kano.
A ranar Talata amaryar da ƙawayen ta suka shirya taron wuni, sai kuma a ranar Laraba aka yi taron bikin Ranar Ƙauyawa a Gidan Ɗanhausa da ke Titin Sokoto a Nassarawa GRA.
An yi raye-raye da kaɗe-kaɗe na gargajiya tare da cin abinci irin na gargajiya kamar waina, dambu, goruba, kurna da magarya da dai sauran kayayyakin marmari.
A ranar Alhamis, uwar amarya ta shirya wani gagarumin taro a otal ɗin The Afficent da ke Sultan Road duk dai Nassarawa GRA.


Taron dai za a iya kiran sa na kece raini da kuma nuna wa duniya isa domin kuwa babu mamaki Hajiya Asma’u ta shirya wannan taron ne don ta nuna ƙarfin alaƙar ta da jama’a. Kuma babu shakka an nuna mata kara.

An fara taron ne da karfe 8 na dare, inda Halisa Muhammad ta buɗe taro da addu’a, sai kuma yayar amarya, Sumayya Abubakar, ta yi jawabin maraba, yayin da Hadiza Kabara ta yi nasiha ga sababbin ma’auratan.
Bayan wannan kuma sai aka yi kamu inda abokan ango suka yi sayen baki kamar yadda yake a al’adun Hausa.
Da abokan ango suka gama sayen baki sai amarya ta fito ta zauna a kan kujerar alfarma da aka saka mata yayin da mawaƙi Aminu Maidawayya da yaran sa suka baje-kolin waƙoƙin su.
A wajen dai amarya da uwar amarya sun sha liƙin kuɗi kamar zubar ruwan sama.

Taro dai ya yi taro, an ci an sha, kuma jama’a ba ma ‘yan fim ba har da wasu ɗimbin masoya na Asma’u Sani sun halarci taron.
A ɓangaren ‘yan fim kuwa, duk wata tsohuwar jaruma da ma waɗanda ake damawa da su a yanzu sun halarta.

Haka nan marubuta mata irin su Bilkisu Yusuf Ali, Sadiya Garba Yakasai, Lubabatu Ya’u, Hadiza Nuhu Gudaji, da Bushira Nakura suna daga cikin waɗanda suka halarta.
Wajen misalin ƙarfe 10 da aka tashi daga taron.

A ranar Juma’a aka ɗaura auren bayan sallar Juma’a a Masallacin Ƙuba da ke Tunkuntawa, inda nan ma jama’a da dama suka halarta.
Kaɗan daga cikin su sun haɗa da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, da Ado Ahmad Gidan Dabino, Al-Mustapha Adam Muhammad, Baballe Hayatu, Sadiq Mafia da sauran su.
Sai kuma taron yini da uwar amarya ta shirya bayan ɗaurin auren a gidan ta da ke Tunkuntawa inda abokan arziki da ‘yan’uwa na jini suka riƙa zuwa don taya murna.
An dai yi biki an gama lafiya, kuma amarya ta tare a ɗakin mijin ta.
Allah ya ba da zaman lafiya.