• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An ɗaura auren A’isha ‘yar jaruma Asma’u Sani

by MUKHTAR YAKUBU
December 13, 2024
in Ranar Murna
0
An ɗaura auren A’isha ‘yar jaruma Asma’u Sani

Amarya A'isha Ibrahim Yusuf da angonta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU aka ɗaura auren A’isha Ibrahim Yusuf, ‘yar jarumar Kannywood, Asma’u Sani, bayan kwana uku da aka shafe ana shagulgulan bikin a Kano.

A ranar Talata amaryar da ƙawayen ta suka shirya taron wuni, sai kuma a ranar Laraba aka yi taron bikin Ranar Ƙauyawa a Gidan Ɗanhausa da ke Titin Sokoto a Nassarawa GRA.

An yi raye-raye da kaɗe-kaɗe na gargajiya tare da cin abinci irin na gargajiya kamar waina, dambu, goruba, kurna da magarya da dai sauran kayayyakin marmari.

A ranar Alhamis, uwar amarya ta shirya wani gagarumin taro a otal ɗin The Afficent da ke Sultan Road duk dai Nassarawa GRA.

Amarya tana yi wa ango liƙi a wurin taron
Amarya da ƙawayen ta

Taron dai za a iya kiran sa na kece raini da kuma nuna wa duniya isa domin kuwa babu mamaki Hajiya Asma’u ta shirya wannan taron ne don ta nuna ƙarfin alaƙar ta da jama’a. Kuma babu shakka an nuna mata kara.

Asma’u Sani, Ruƙayya Dawayya, da sauran jarumai

An fara taron ne da karfe 8 na dare, inda Halisa Muhammad ta buɗe taro da addu’a, sai kuma yayar amarya, Sumayya Abubakar, ta yi jawabin maraba, yayin da Hadiza Kabara ta yi nasiha ga sababbin ma’auratan.

Bayan wannan kuma sai aka yi kamu inda abokan ango suka yi sayen baki kamar yadda yake a al’adun Hausa.

Da abokan ango suka gama sayen baki sai amarya ta fito ta zauna a kan kujerar alfarma da aka saka mata yayin da mawaƙi Aminu Maidawayya da yaran sa suka baje-kolin waƙoƙin su.

A wajen dai amarya da uwar amarya sun sha liƙin kuɗi kamar zubar ruwan sama.

Uwar amarya tana shan liƙi daga wajen ango da amarya

Taro dai ya yi taro, an ci an sha, kuma jama’a ba ma ‘yan fim ba har da wasu ɗimbin masoya na Asma’u Sani sun halarci taron.

A ɓangaren ‘yan fim kuwa, duk wata tsohuwar jaruma da ma waɗanda ake damawa da su a yanzu sun halarta.

Tsofaffin jarumai mata da suka halarci taron

Haka nan marubuta mata irin su Bilkisu Yusuf Ali, Sadiya Garba Yakasai, Lubabatu Ya’u, Hadiza Nuhu Gudaji, da Bushira Nakura suna daga cikin waɗanda suka halarta.

Wajen misalin ƙarfe 10 da aka tashi daga taron.

Daga dama: Asma’u Sani, Mansurah Isah da Sumayya Abubakar yayar amarya, kuma babbar ‘yar Asma’u Sani

A ranar Juma’a aka ɗaura auren bayan sallar Juma’a a Masallacin Ƙuba da ke Tunkuntawa, inda nan ma jama’a da dama suka halarta.

Kaɗan daga cikin su sun haɗa da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, da Ado Ahmad Gidan Dabino, Al-Mustapha Adam Muhammad, Baballe Hayatu, Sadiq Mafia da sauran su.

Sai kuma taron yini da uwar amarya ta shirya bayan ɗaurin auren a gidan ta da ke Tunkuntawa inda abokan arziki da ‘yan’uwa na jini suka riƙa zuwa don taya murna.

An dai yi biki an gama lafiya, kuma amarya ta tare a ɗakin mijin ta.

Allah ya ba da zaman lafiya.

Loading

Previous Post

Gwamnatin Tinubu na amfani da kuɗaɗen tallafin mai don cigaban al’umma, cewar Minista

Next Post

‘Yan fim da marubuta sun fidda ni kunya a bikin ‘ya ta, inji jaruma Asma’u Sani

Related Posts

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi
Ranar Murna

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi

December 26, 2025
Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 
Ranar Murna

Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

December 20, 2025
Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa
Ranar Murna

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

December 14, 2025
Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar
Ranar Murna

Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar

December 3, 2025
Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam
Ranar Murna

Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam

December 3, 2025
Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum
Ranar Murna

Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

November 28, 2025
Next Post
‘Yan fim da marubuta sun fidda ni kunya a bikin ‘ya ta, inji jaruma Asma’u Sani

'Yan fim da marubuta sun fidda ni kunya a bikin 'ya ta, inji jaruma Asma'u Sani

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!