JARUMAR Kannywood, Zuwaira Musa, ta bi sahun masu yin aure a ƙarshen wannan shekara ta 2024 domin kuwa a jiya Asabar, 7 ga Disamba aka ɗaura auren ta da angon ta, Buhari Umar (General).
An ɗaura auren a masallacin Juma’a da ke Na’ibawa, Kano, da misalin ƙarfe 1 na rana.
Tun kafin ranar, jarumar ta shirya wani gagarumin taro na murnar bikin nata.


A ranar Juma’a aka yi taron bikin a Titin Lawan Dambazau wanda jarumai mata da yawa suka halarta.


Waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da Hadiza Kabara, Asma’u Sani, Maijidda Abbas, da sauran su.
Allah ya ba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auren.