‘YAN Kannywood sun cigaba da nuna alhinin su a kan rashin abokin aikin su, Alhaji Mu’azu Muhammad Birniwa (El-Mu’az), wanda ya rasu a daren shekaranjiya Laraba.
A zantawar da mujallar Fim ta yi da shahararren mawaƙi Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) a game da rasuwar abokin aikin nasa, cewa ya yi, “Kamar yadda dukkan ɗan Musulmi ya sani, har ma wanda ba Musulmi ba, ita mutuwa tana kan kowa. Duk wanda Allah ya ba shi aron rai, to akwai lokacin da Allah zai karɓi abin sa.”
“Mu’azu lokaci ya zo sa’i. Kuma mutuwa ta zo bagatatan, irin wadda ba mu yi tsammani ba. Allahn da ya halicce mu, shi ya halicce shi, kuma ya fi mu son sa. Kuma shi ya karɓe shi. Illa iyaka abin da za mu ce dangane da irin nuni da mutuwar sa ta yi, ta zamo wani allon gwajin misali na kyawawan mu’amala.”

Ala ya ƙara da cewa, “Da ma mun rubuta, mun shaide shi, mutum ne mai zumunci, mutum ne mai alheri, mutum ne mai kyakkyawar mu’amala da kowa.
“Na yi mamaki, duk da cewa abin an yi shi a ƙurarren lokaci, amma na san Mu’azu yana mu’amala da manyan malamai na kowane irin ɓangare.
“Kowane irin janibi na al’umma za ka ga Mu’azu yana hulɗa da su: ‘yan kasuwa ne, masu sai da filaye ne, masu harkar motoci ne, malaman addini, ‘yan siyasa, kowane irin rukunin al’umma.
“Kuma a cikin fim industiri, yana da kyakkyawar mu’amala da aktoci da mata da mawaƙa, kowane janibi.
“Kuma ka ga jana’izar sa ta nuna kyakkyawan zama da yake yi da maƙwabtan sa da kuma mutanen unguwar su suka fito aka raka shi maƙabarta. Allah ya karɓi wannan yanki nasa.”
Ala ya ce, “Dukkan Musulmi abin da aka bar mana, tawakkali da mai da lamari ga Allah. Duk abin da ya faru da mu, sharran wa khairan, sai mu ƙaddara haka Allah ya hukunta.
“Duk wanda ya rayu, tabbas sai ya mutu. Abu ne mara daɗi, saboda sabo da shaƙuwa.
“Ni awa uku mun yi magana da shi, sai kuma kawai na ji an ce ya mutu. ‘I was shocked.
“Ni ina Kano, shi yana Kaduna, saboda muna ta shirye-shiryen zuwa ɗaurin auren ƙanwar sa da ya gayyace mu, da kuma ɗaurin auren abokin sana’ar mu, Auta, kawai sai muka ji labari!
“Ka san abin ba zai wa kowa daɗi ba. Mutumin da ke da kyakkyawar hulɗa da kowa. Duk abin da muke yi a Kano, ko ba mu gaya masa ba, in ya ji labari sai ya zo.
“Ba na mantawa, zumunci na da shi na biyun ƙarshe shi ne auren ‘ya’ya na da ya je da dina. Amma akwai zumunci da aka yi na wani ɗan’uwan mu, aminin mu, Auwal Garba Ɗanbarno. Haka ya tashi ya zo aka yi addu’a, bayan an yi jana’iza da shi, kuma ya ba da gudunmawa ga iyalan mamaci.
“Kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake faɗa, ‘Addinu, al’mu’amala’, ka ga mu’amala ce ta yi nuni da halayen El-Mu’az. Ba shahararren malami ba ne, amma dubi yadda yake mu’amala da malamai da yara da manya da maza da mata da maƙwabta. Saboda haka, mu’amalar ka ta kyautatu.”
A ƙarshe, sha’irin ya yi jan hankali ga al’ummar Musulmi da cewa, “Ina jan hankalin mu al’ummar Musulmi, mu zama masu tsoron Allah. Mu kyautata mu’amalar mu. Duk inda mu’amala ta yi kyau, to addini ya tsaya a wurin. Shi ya sa aka ce addini ma shi ne mu’amala.
“Rasuwar El-Mu’az mu’amala ta nuna kyakkyawa ce, saboda zaman sa lafiya da al’umma da kuma alherin sa a cikin al’umma.”

A ɓangaren na hannun damar marigayi El-Mu’az, wato Sagir Mustapha Ɗanyaro (Baban Kausar), cewa ya yi, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Wannan rasuwa tana ɗaya daga cikin waɗanda suka girgiza rayuwa ta. Saboda ni zan iya cewa, ni wani ɓangare ne na rayuwar El-Mu’az, akwai abubuwan da da yawa na rayuwa ni nake gudanar da su. So, na san shi ciki da bai.
“Kuma mutum ne ba shi da wani abu a rayuwa sai alkhairi.
“Ɗan’adam tara yake, bai cika goma ba, za a iya samun kuskure, amma dai ni na san duk wanda za ka tuntuɓa zai faɗa maka alkhairin sa.
“Mutum ne mai alkhairi, mutum ne mai mutunta mutane, mutum ne mai ƙoƙarin ganin ya kamanta abin da ya dace.”
Baban Kausar ya ci gaba da cewa “To, shi irin wannan abu, Allah yakan yi abin sa yadda ya so, kuma ba ka da abin da za ka yi. Kuma da ma ya faɗa mana cewa dukkan rai za ta ɗanɗani mutuwa. Don haka wannan abin shi ne ya riske mu a ɓangaren sa.
“Muna ta addu’a Allah ya sa ya cika da imani, Allah ya jaddada masa rahamar sa, Allah ya sa makwancin sa ya zama dausayi daga dausayin Aljanna, Allah ya sa babu rabon wuta a jikin sa, Allah ya kula masa da iyalin sa, mu kuma da muka rayu da shi, Allah ba mu ikon ci gaba da kula da zumunci da iyalan sa da ‘yan’uwan sa.”
Ko yaya ji a lokacin da labarin rasuwar ya riske shi? Sai ya ce, “Ai ba labarin rasuwar sa na ji ba, ni ya rasu a hannu na ne. Ba labari na ji ba, sai dai in faɗa wa wasu.
“Babu daɗi, kowa ya san yadda mutuwa take, kullum sabuwa take komawa idan ta zo wa ɗan’adam.”

Shi kuwa jarumi kuma shugaban ƙungiyar Kadawood, Malam Nura MC, cewa ya yi: “Assalamu alaikum! Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Haƙiƙa mun yi imani da mutuwa da kuma ranar ƙiyama. Rasuwar El-Mu’az Birniwa rasuwa ce wadda ta zo mana a bazata. Sai dai mun san cewa, ‘Kullu nafsin za’ikatul maut’.
“A madadin shugabannin Kadawood, muna miƙa ta’aziyar mu ga ɗaukacin ‘yan’uwan da abokan arziki bisa wannan babban rashin da muka yi. Muna roƙon Allah (s.w.t.) ya jiƙan sa da mu ba ki ɗaya, ya raya abin da ya bari cikin aminci.
“Wannan rashi ba na iyalan sa ba ne kawai, rashi ne wanda ya shafe mu baki ɗaya fim na Arewa. Allah ya gafarta masa.”
Furodusa kuma jarumi Sabi’u M. Gidaje kuwa ya ce: “Allah Sarki El-Ma’az! Allah ya yi masa rahama, Allah ya sa Aljanna ta zama makoma a gare shi. Mun yi babban rashi wallahi. Allah ya kyauta ƙarshen mu, ya Allah.”
Ita ma Kungiyar Shugabannin Jihohi ta MOPPAN ta yi ta’aziyya. A saƙon da shugaban ƙungiyar, Waziri Dandaso Godowoli, ya fitar a rubuce, ƙungiyar ta ce: “A madadin Ƙungiyar Shugabannin MOPPAN na Jihohi, muna miƙa ta’aziyyar mu ga ɗaukacin al’ummar Kannywood, MOPPAN, Kadawood, al’ummar Jihar Jigawa, Jihar Kaduna da ɗaukacin al’ummar Arewacin Nijeriya bisa rasuwar El-Mu’az Birniwa.
“El-Mu’az ya kasance fitaccen mawaƙin Hausa wanda kyawawan waƙoƙin sa suka taɓa rayuwar mutane da dama. Gudunmawar sa ta kasance har abada a cikin zukatan mu da al’adun mu.
“Muna kuma yi wa iyalan sa addu’a a wannan mawuyacin lokaci. Allah ya ba su juriya, kuma ya sa Jannatul Firdausi ta zama masaukin sa na ƙarshe.”
Jarumi kuma dattijo a industiri, Malam Balarabe Jaji, shi ma ya yi jimamin rasuwar. Ya ce: “Daga Allah muke kuma zuwa gare shi dukkan mu za mu koma. Dukkan mu muna son Malam El-Mu’az Birniwa, amma Allah ya fi mu son shi. Ba za mu iya musun kiran Mahaliccin mu ba.
“Allah Ta’ala ya sanya shi a cikin Jannatul Firdausi, mu kuma da waɗanda aka yi wa rasuwa ya ba mu ƙarfin juriyar rashin sa.”
A nasa ɓangaren, mawaƙi a Kaduna, Ɗayyab Ɗa’a, ya ce: “Kwana ya riga ya ƙare, kowa nashi yake jira. Allahu Akbar kabiran, El-Mu’az Muhammad Birniwa! Dole in faɗi yadda zuciya ta ta kaɗu da rashin sa matuƙa.
“Na yi kewar sa tsawon watanni kamar shida muna samun saɓani na haɗuwa, sai dai a waya wani lokacin mu kan ɗan gaisa da shi.
“Babu wanda ba shi da ƙalubale a zamantakewa na rayuwa. El-Ma’az a cikin halayyar sa masu kyau, ba zan iya manta halin sa na barkwanci da alkhairi da jin tausayi ba.
“El-Mu’az matashi ne mai zummar neman na kan sa, domin yana ɗaya daga cikin waɗanda suka matsa mani da na rungumi sana’a, ba sana’ar waƙa kaɗai ba.
“Duk da ita rayuwa zo mu zauna ne zo mu saɓa ne. Wani lokacin ana ɓata wa juna rai, ai faɗa kuma a shirya.
“Wallahi na daɗe ban shiga ofishin El-Mu’az ba, amma saboda bankwana ta kusantar ƙarar kwana, na bi Auta Waziri domin zai faɗa masa tsare-tsaren da aka tattauna da bai samu halarta ba.
“A lokacin El-Mu’az ya ƙara ƙarfafa wa Auta lallai zai ga saƙon sa in-sha Allahu, kada ya samu damuwa.
“Daga nan sai ya juya ya kalle ni, ya ce, Ɗa’iyatu duniya!’ Da ma wani lokacin bai kira na da Ɗa’a. Ya ce da ni, ‘Kwana biyu,’ na ce, ‘Lafiya ƙalau wallahi Mu’azu, al’amura ne sukai mani yawa.’
“Na ce da shi, ‘Ashe ka gyara ofis haka?’ Ya ce, ‘Wallahi. Ka daɗe fa ba ka shigo ba.’ Muka yi ɗan barkwancin da muka saba, na fita.
“Allah ya yi masa rahama da dukkan ‘yan’uwa Musulmi baki ɗaya.”
Jarumin barkwanci, Baba Ari, ya ce: “Ubangiji Allah ya jiƙan El-Mu’az, ya gafarta masa, ya yafe masa, ya kyautata makwancin sa da zuriyar sa, don alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W).