KWAMITIN shirya gasar rubuta gajerun ƙagaggun labaran Hausa ta jaridun ‘Aminiya’ da ‘Tust’ ya fitar da sunayen labarai uku da su ka lashe gasar.
A rahoton da mujallar Fim ta gani, an bayyana cewa alƙaluman da alƙalan gasar su ka miƙa wa masu gudanar da gasar ta farko sun daidaita da zaɓar labaran uku daga cikin 20 da aka tantance daga cikin labarai sama da 350 da su ka shiga gasar a bana.
Jigon gasar shi ne matsalolin dimokiraɗiyya da dambarwar siyasa.
Alƙalan gasar dai su ne malaman jami’a biyu, Dakta Aliyah Adamu Ahmad ta Jami’ar Jihar Sakkwato (SSU) da Dakta Umar Aliyu Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo (UDUS), Sokoto, da kuma fitaccen marubuci mazaunin Kano, Malam Nazir Adam Salih.
Labaran da alƙalan su ka zaɓa zuwa matakin ƙarshe, waɗanda kowane daga cikin su zai iya lashe gasar su ne:
1. ‘Tufka Da Warwara’
2. Dimokiraɗiyyar Talaka’
3. ‘Ranar Ƙin Dillanci’
Labaran da su ka cancanci yabo kuwa su 12 daga cikin waɗanda alƙalan su ka tantance su ne:
1. ‘Komai Nisan Dare’
2. ‘Hassada Ga Mai Rabo’
3. ‘Baki Guba Ne’
4. ‘Tsaka Mai Wuya’
5. ‘Ƙwawalwalniya’
6. ‘Kazar Kwanci’
7. ‘Ci Ga Rashi’
8. ‘Igiyar Linƙaya’
9. ‘Kotun Allah Ya Isa’
10. ‘Zaɓin Allah’
11. ‘Tsalle Ɗaya’
12. ‘Yanayi’
Jagoran gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi, babban malami a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ya bayyana cewa
waɗannan labarai guda 15 da su ka yi zarra, za a sake tace su domin sake tsarawa da buga su a matsayin littafi da za a ƙaddamar a wajen wani ƙwarya-ƙwaryan biki da hukumar gudanarwar kamfanin jaridun ‘Aminiya’ da ‘Trust’ za su gudanar a garin Kaduna a ranar 2 ga Janairu, 2021.
Ya ce, “A wajen wannan biki ne za a bayyana waɗanda su ka lashe gasar ta bana, wato na 1 zuwa na 3, a kuma ba su awalajar kuɗi da kambun yabo da satifiket.
“Su kuma waɗanda su ka samu yabo na musamman kowane za a ba shi satifiket na shiga wannan gasa, in Allah ya kai mu.
“Gasar rubutun gajeren labaran dai haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts da ke Kaduna da hukumar gudanarwar jaridun ‘Aminiya’ da ‘Trust’ da ke Abuja, domin sa wa matasa, maza da mata shauƙin rubuta gajerun labarai da su ke tattauna matsalolin al’umma daban-daban da nema musu mafita, domin bada gudunmuwa wajen raya da bunƙasa adabin Hausa wadda za a dinga gabatarwa a kowace shekara da yardar Allah.”
Sai dai wakilin mu ya lura da wani salo a wannan gasa ta Aminiya-Trust: wato ba a faɗin ko ɗaya daga cikin zakarun marubutan ba, sai dai sunayen littattafan su.
A kan hakan, Farfesa Malumfashi ya faɗa wa wakilin namu cewa: “Sai a sanarwar ƙarshe za a bayyana sunayen kowa da kowa in-sha Allah.”