AN naɗa Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Mohammed Sarari, ya jagoranci kwamitin tsare-tsare (LOC) na Bikin Baje-kolin Finafinai na Zuma (Zuma Film Festival, ZFF) na bana.
A sanarwar da ya bayar, kakakin MOPPAN na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ya ce za a yi bikin ne a tsakanin ranakun 2 da 8 ga Afrilu, 2022.
Ya ƙara da cewa sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin takardar da masu shirya bikin, wato Hukumar Finafinai ta Nijeriya (NFC), ta aiko wa Sarari.
Takardar naɗin, mai kwanan wata 15 ga Fabrairu, 2022, ta na ɗauke da sa-hannun Daraktan Bikin, Mista Edmund Peters.
Takardar ta ce ana sa ran Dakta Sarari zai jagoranci tare da jawo masu ruwa da tsaki daga yankunan Kano da Kaduna domin su shiga cikin bikin na bana sosai da sosai.
Sauran membobin kwamitin su ne tsohuwar shugabar MOPPAN reshen Jihar Kaduna kuma Sakatariyar Kuɗi ta ƙasa ta ƙungiyar a yanzu, Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj, da shugaban riƙo na MOPPAN, reshen Kano, Umar Gombe.
Hukumar ta bayyana matuƙar jin daɗi dangane da naɗin da ta yi wa waɗannan jagorori na Kannywood.