A YAU Asabar ne aka yi gagarumin taron ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar mata ‘yan fim mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) tare da rantsar da shugabannin ta.
Taron, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na ‘Meenah Event Centre’ da ke unguwar Nassarawa G.R.A. a Kano, an fara shi ne da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Tun da farko, ma’ajin ƙungiyar, Asma’u Sani, ta gabatar da jawabin maraba inda ta faɗi manufar kafa ƙungiyar, ta ce ƙungiya ce ta sada zumunci, saboda sun ga akwai rashin haɗuwar jarumai mata ‘yan fim, don haka su ka ga ya kamata su kafa ƙungiyar domin a riƙa haɗuwa da juna.
Ta ce, “Don haka ne wannan ƙungiyar ta ƙunshi dukkan matan da su ka yi fim a baya da kuma waɗanda su ke yin fim ɗin a yanzu.Sannan ta haɗa da zawarawa da matan aure da ma ‘ya’yan mu da jikokin mu.
“Don haka ma a wannan wajen za a gan mu da ‘ya’yan mu da jikokin mu, duk mun haɗu a wannan waje. Don haka a yanzu idan ma akwai waɗanda su ke da matsala a tsakanin su sai a haɗu a yafe wa juna, don yanzu mun koma mun zama ɗaya.”

Da yake masu lura da al’amuran industiri sun yi ittifaƙi da cewa an kafa AKAFA ne saboda a karya lagon Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeriya, wato ‘Kannywood Women’s Association of Nigeria’ (K-WAN), Asma’u ta bayyana cewa abin ba haka ba ne. Ta ce, “Ita wannan ƙungiyar ba an kafa ta ba ne domin ta kashe wata ƙungiyar ko kuma ta zama kishiya da wata ƙungiyar mata a cikin harkar fim. A’a, ta duk mata ‘yan fim ce; idan ki na wata ƙungiyar, to hakan bai hana ki zo a yi wannan tafiyar da ke ba, domin ni kai na ina cikin wasu ƙungiyoyin mata a cikin harkar fim, har ma ina riƙe da muƙami, amma hakan bai hana na zo a yi wannan tafiyar da ni ba.”
Asma’u, wadda jigo ce a ƙungiyar K-WAN, ta yi wa mahalarta taron barka da zuwa da kuma fatan za a yi taro lafiya a gama lafiya.
A nasa jawabin, babban baƙo, Alhaji Salisu Muhammad (Officer), ya jinjina wa matan da su ka samar da wannan babbar ƙungiyar, kuma ya yi fatan Allah ya sa su yi amfani da ita wajen samar da cigaba da kuma haɗin kai mai ɗorewa.
Haka kuma ya ja hankalin su da su tsara manufofin da za su magance irin kallon da ake yi wa ‘yan fim mata a matsayin matan da ba su kame kan su kuma ba su yin abin da ya dace.
Malam Salisu ya yi kira a gare su da su haɗa kai da sauran ƙungiyoyin cikin harkar fim kamar MOPPAN da ‘Arewa’ saboda a yanzu akwai mata masu yawa da su ke shigowa cikin masana’antar su na da aure ko ana shirin yi masu aure, sai an zo an saka su a fim sai wasu matsaloli su riƙa tasowa, wasu ma har a kai ga zuwa kotu, ko kuma a same su su na aikata abubuwan da su dace ba duk da sunan ‘yan Kannywood.
“Saboda haka wannan babban ƙalubale ne ga wannan ƙungiyar da ya kamata ta mayar da hankali a kan su,” inji shi.

Daga nan aka gabatar da ‘ya’yan ‘yan fim da jikokin su a wajen taron, sannan aka shirya masu wata dina tasu ta musamman.
Haka kuma an shaƙata da waƙoƙi tare da cin abinci.
Bayan an kammala cin abincin, sai Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Fim ta Ƙasa (‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’, MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya jagoranci rantsar da sababbin shugabannin AKAFA, inda ya hore su da su yi iya yin su don ganin sun dawo da ƙima da martabar Kannywood yadda za a riƙa ganin ta a matsayin masana’anta mai mutunci a idon jama’a.
A cewar sa, “Bai kamata ba ana ji ana kallo a bar wasu yara su na zubar da ƙimar masana’antar da sunan su ‘yan fim ne. Don haka matakin farko da ya kamata wannan ƙungiyar ta ɗauka shi ne samar da tsari ga mata masu irin wannan mummunar ɗabi’a. Idan har ‘yan wannan ƙungiyar su ka samar da wannan tsarin, to zai zama sun kafa tarihin da na bayan su za su yi alfahari da su.”
Bayan an rantsar da su a matsayin shugabanni, sai shugabar ƙungiyar ta AKAFA, Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a), ta yi godiya ga matan Kannywood da su ka ba ta wannan shugabanci saboda sun ga ta cancanta.
Rashida ta yi kira a gare su da su ba ta haɗin kai domin sauke nauyin da su ka ɗora mata, domin aikin nasu ne duka ba nata ne ita kaɗai ba.
Ta ci gaba da cewa, “Mu matan Kannywwod da mu ka kafa wannan ƙungiyar, mun kafa ta ne bisa kyakkyawar manufa ta taimaka wa junan mu da kuma samar da cigaban masana’antar.
“Don haka ƙungiyar AKAFA ta zo da manufofin tabbatar da ƙwarewa tare da bayar da gudunmawar cigaban masarautar Kannywood da taimakawa tare da daƙile hanyoyin satar fasaha a cikin sana’ar fim.
“Sannan za mu ƙulla alaƙa da sauran masu gudanar da harkar fim na dukkan ƙasar nan.
“Sannan ya na daga cikin manufar wannan ƙungiyar ta tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan fim baki ɗaya ta yadda za mu riƙa taimakon junan mu ta hanyoyin da su ka dace tare da taimakon na waje ma da waɗanda su ke buƙatar taimako daga wajen mu.”

Daga ƙarshe, shugabar ta yi fatan Allah ya sa wannan sabuwar tafiyar da su ka fara ta zamo wata hanyar da za ta magance matsalolin da masana’antar Kannywood ta ke ci da kuma kare aukuwar wasu a nan gaba.
An dai yi taron an tashi lafiya da misalin ƙarfe 9 na dare.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ‘yan fim da dama sun halarci taron, kuma kaɗan daga cikin su su ne Samira Ahmad, Zahra’u Shata, Fati Sulaiman, Maryam Mashahama Maijidda Ibrahim, Sakna Gadaz, Sadiya Gyale, Hafsat Shehu, Hafsat Idris, Asma’u Sani, Hadiza Kabara Ummi Gombe, Ladin Cima, Maryam CTV, Hadizan Saima, Mansurah Isah Maryam Ceeter, Jamila Gamdare, Rahama Sirace, Zuwaira Juda, Zakariyya Ibrahim, Maryam A. Baba, Halima Atete, Fauziyya Maikyau, Yahanasu Sani, da sauran su.


