• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gobe Asabar za a ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar matan Kannywood ta AKAFA

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 22, 2022
in Labarai
0
Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa'a), Shugabar AKAFA

Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa'a), Shugabar AKAFA

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YANZU haka shirye-shirye sun kammala domin gudanar da taron ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar matan Kannywood mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) wanda za a yi a gobe Asabar, 23 ga Yuli, 2022.

Za a yi taron a ɗakin taro na ‘Meenah Events Centre’ da ke Kano.

Shugabar ƙungiyar ta ƙasa, Hajiya Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a, ita ce ta sanar da hakan a lokacin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim a game da taron.

Hajiya Rashida ta yi bayanin cewa: “A gaskiya, mu a yanzu mun kammala shirin taron, ranar kawai mu ke jira domin gudanar da shi. Kuma wannan taron zai bai wa kowa mamaki, domin mun gayyaci manyan mutane na masana’antar Kannywood da malamai da ‘yan siyasa da sauran jama’a domin su zo su ga abin da ‘yan fim su ke yi na alheri, ba kamar yadda a ke ba su labarin mu ba. 

Cewar Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a: “AKAFA za ta riƙa bi wa matan Kannywood haƙƙin su”

“Domin kuwa mu ‘yan fim mutane ne masu abubuwan alheri, to sai dai ba a faɗa, sai ya zama abin da wasu kaɗan daga cikin mu su ke yi shi ne ya ke zama labari a wajen mutane. To mutane za su zo su ga aikin mu na alheri.”

A game da halartar ‘yan fim a taron kuwa, Rashida ta ce: “Ba mu ɗauke wa duk wata jaruma ba domin taron na duk matan da su ke yin fim ne, tun daga farkon Kannywood har zuwa wannan lokacin. Don haka masu ‘ya’ya da jikoki duk kowa ya zo da su, don taron na sada zumunci ne a tsakanin ‘yan fim da ‘ya’yan su, wanda kuma mu na sa ran abin ya ɗore har zuwa jikokin mu, don ba ma fatan abin ya tsaya a iya kan mu.”

Ta ci gaba da cewa: “Ina tabbatar wa da mutane wannan taron ya bambanta da duk wani taro da aka ta yi a cikin masana’antar Kannywood, domin zan iya faɗa maka cewa ba a taɓa yin taro irin wanda za mu yi ba saboda harkar fim ta mata ce. Don haka a yanzu mun haɗu jaruman mu da furodusas ɗin mu da mawaƙan mu da ma duk wata mace da ta ke yin aiki a cikin masana’antar, mun dunƙule za mu yi tafiya tare domin neman ‘yancin kan mu. 

“Don haka daga yanzu mu na da tsarin da ba za mu rinƙa zama kara-zube ba kamar yadda mu ke yi a baya. Don za mu rinƙa taimakon junan mu; ko mace ba ta da lafiya, ko ta samu kan ta cikin matsala, za mu shiga mu fita domin ganin ta samu ‘yanci. 

“Kuma daga ‘yanzu duk jarumar da ta yi aiki aka hana ta kuɗin ta za mu shiga cikin maganar don ganin a karɓar mata haƙƙin ta.”

Daga ƙarshe, shugabar ta ƙungiyar AKAFA ta yi fatan za su yi taron lafiya su gama lafiya.

Loading

Tags: actressesAKAFAAssociation of Kannywood Female ArtistesjarumaiKanomatan KannywoodRasheeda Adamu Abdullahi Maisa'a.Taro
Previous Post

Lokacin da na fara fim an so a haɗa ni da iyaye na, cewar jaruma Shafa’atu Muhammad

Next Post

An rantsar da shugabannin sabuwar ƙungiyar matan Kannywood ta AKAFA a taron ƙaddamarwa

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Sababbin shugabannin AKAFA lokacin da ake rantsar da su

An rantsar da shugabannin sabuwar ƙungiyar matan Kannywood ta AKAFA a taron ƙaddamarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!