SABUWAR jarumar Kannywood, Shafa’atu Muhammad, ta ce babu irin abin da ƙawayen ta da maƙwaftan su ba su yi ba domin su haɗa ta da iyayen ta saboda ta shigo harkar fim, amma ba su cimma nasara ba.
Jarumar, wadda daga Jihar Adamawa ta zo Kano domin yin fim, ta bayyana haka ne a lokacin tattaunawar da mujallar Fim, inda ta ce, “A lokacin da na zo Kano harkar fim maƙwaftan mu har gidan mu su ke zuwa su na kai gulma ta a wajen iyaye na saboda su hana ni.
“Haka su ma ƙawaye na su ka riƙa zagi na, wai na shiga duniya na ƙi aure. Amma dai duk da haka iyaye na sun amince, don haka da yardar su na ke yin fim a yanzu.”
Da mu ka tambayi Shafa’atu ta ko a yaushe ta shigo harkar fim da kuma finafinan da ta yi za su kai guda nawa, sai ta ce “To, zan kai shekara guda a cikin masana’antar. Kuma na yi finafinai, daga cikin su akwai ‘Su Ma ‘Ya’ya Ne’, ‘Ƙanin Na’, ‘Sanda’, ‘Umarni’, da wasu kuma da na ke aikin su a yanzu.”
Ko menene Shafa’atu ba ta so a rayuwar ta? Amsa: “Gaskiya ba na son karya alƙawari, don ya na saurin ɓata mini rai. Kuma abin da ya ke saka ni farin ciki a rayuwa ta shi ne a yabe ni a duk lokacin da na yi wani abin ƙoƙari.”
Daga ƙarshe ta yi fatan samun nasara a dukkan abubuwan da ta sa a gaba na rayuwa.
![]()







