DA safiyar wannan rana ta Asabar, 3 ga Yuni, 2023 aka ɗaura auren Zainab Sunusi, babbar ‘yar fitacciyar marubuciya Alawiyya Wada Isa.
An ɗaura auren a masallacin Juma’a na Umar Ibn Khattab da ke daura da shatale-talen Dangi kan Titin zuwa Zariya a cikin garin Kano. Jama’a da dama sun taru domin shaidawa.

Tun a ranar Laraba uwar amarya, wato Alawiyya Wada Isa, ta shirya taron biki na musamman don marubuta ‘yan’uwan ta su taru su taya ta murna.
Taron bikin ya ƙayatar sosai duk da ruwan sama da aka yi kamar da bakin ƙwarya. Marubuta da dama sun taru in da aka yi jawabai da nasihohi, sannan kuma a gefe guda aka sada zumunci.
Ɗimbin marubutan da su ka halarci taron bikin sun haɗa da Fauziyya D. Sulaiman, Umma Sulaiman ‘Yan’awaki (Aunty Baby), Hadiza Nuhu Gudaji, Zainab Lawan Birged, Maimuna Idris Sani Beli, Sadiya Garba Yakasai, Zulfa’u Aliyu, Nafisa Tasi’u Lili, da sauran su.

Uwar amaryar, wato Hajiya Alawiyya Wada Isa, ita ce uwargidan shahararren mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).
Allah ya ba amarya da ango zaman lafiya da ƙaruwar arziki, amin.






