ƘUNGIYOYIN da ke bayar da tallafi da taimaka wa mabuƙata da marayu na cikin ‘yan fim da marubuta a Kano sun kai ziyara ga uwargidan tsohon Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Buhari, a garin Daura domin su nuna godiyar su da kuma ban-gajiya kan yadda maigidan ta ya kammala mulki ya koma gida lafiya.
Tawagar marubutan da ‘yan fim ɗin, a ƙarƙashin jagorancin Fauziyya D. Sulaiman, ta haɗa dukkan shugabannin ƙungiyoyin mata marubuta da ‘yan fim da su ke bayar da tallafi ga mabuƙata a Jihar Kano.
A lokacin da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani dangane da ziyarar tasu, marubuciya Fauziyya D Sulaiman ta ce: “Mun je ziyara ne Daura. Ka san mun daɗe ko mun yi shekaru mu na aiki a ƙarƙashin ƙungiyar uwargidan tsohon Shugaban Ƙasa, wacce ta ke ba mu kayan abinci mu ke rarrabawa. Duk da ta na rabawa a dukkan jihohi, amma wanda ta ke rabawa a Kano ya fi yawa.

“To sai mu ka yanke shawarar tunda Allah ya sa sun gama mulki lafiya, ya kamata mu ƙungiyoyin da ta ba mu aikin rarrabawa mu yi mata karramawa ta musamman, kuma mu je har gida mu same ta.
“Duk da dai wannan ba shi ne karo na farko da mu ka haɗu da ita ba, don tun su na kan mulki mun haɗu, amma dai wannan mun je ne domin yabawa da kuma ba ta ƙwarin gwiwa tare da murnar an gama mulki lafiya an baro Abuja lafiya. To shi ne mu ka je Daura mu ka kai mata wannan lambar karramawa, kuma ta ji daɗi, ita ma ta karrama mu sosai ita da maigidan ta Baba Buhari.”
Fauziyya ta faɗi sunayen abokan tafiyar ta, ta ce, “A ƙungiyoyin, kamar yadda ka ke gani, akwai na su Umma Sulaiman ‘Yan’awaki, Zuwairiyya Adamu Girei, Mansurah Isah, Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a, Saratu Giɗaɗo (Daso), A’isha Dangi, da dai sauran su. Kuma akwai waɗanda ba su samu zuwa ba saboda ayyuka sun yi musu yawa.
“To wannan dai shi ne manufar zuwan namu, kuma alhamdu lillahi mun cimma nasara.”

