WATA jarumar Kannywood ta zama babban misali na yadda ake yaudarar wasu matan (har ma maza) a karɓi kuɗin su amma a ƙi yin fim ɗin, ko a zalunce su wajen shirya fim ɗin. Sunan wannan daɗaɗɗiyar al’ada a industiri shi ne kan-ta-waye. Ita wannan jarumar ta shigo harkar fim ne shekara biyu da ta gabata da zummar yin fim, amma aka dinga yin wasa da hankalin ta, ana karɓe mata kuɗi da sunan za a yi mata fim. A ƙarshe ba a yi mata fim ba, aka yi watsi da ita, babu kuɗi babu fim.
Jarumar, mai suna Fa’iza Muhammad, ta bayyana haka ne a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim dangane da shigowar ta harkar fim.
Fa’iza dai ‘yar asalin garin Girei ce a Jihar Adamawa. Ta yi aure a cikin 2008, ta zauna da mijin ta tsawon shekara 10 a Benin, babban birnin Jihar Edo, kuma sun samu ‘ya’ya uku kafin su rabu. Abin ikon Allah, daga baya mijin ya rasu.
“A shekarar 2020 na dawo Kano da zama, kuma hakan ya ba ni damar shiga harkar fim, wadda da man can ina sha’awar ta tun ina ƙarama,” inji Fa’iza.
To sai dai akwai matsala. A cewar Fa’iza: “Na ɗauka shiga harkar fim abu ne mai sauƙi wanda daga ka zo za ka fara kuma duniya ta san ka. Sai da na shigo na ga abin ba haka ya ke ba, saboda gaskiya na fuskanci matsaloli da dama, don ka san harkar ana da yawa yanzu, kuma a komai idan za ka yi in dai ba ka natsu ba, ka karanci yadda abin ya ke ba, to za ka sha wahala.

“Da na zo a farko – duk da dai ba a kama suna – akwai wanda ya ce zai yi mani fim, na kawo kuɗi. Na ɗauki kuɗi na ba shi, naira 400,000. Aka zo aka samu matsala ba a yi mani fim ɗin ba, kuma babu kuɗin.
“Kuma na yi ta ba da kuɗi haka a kai a kai; in ba da 200,000, in ba da 300,000, in ba da 400,000. Haka dai na yi ta ba su kuɗi su na cinyewa, don gaskiya kuɗin da na kashe a banza waɗanda na san ba su amfane ni ba sun fi miliyan ɗaya ba tare da na yi nasarar yin fim ɗin ba.”
A ƙarshe, Aminu Bala Mailalle ya kira ta saka ta a fim ɗin sa mai suna ‘Sawun Giwa’, ta fito a matsayin jaruma. Shi ne fim ɗin ta na farko. “Ina fatan ya zame mani matakin nasarar da na ke nema na zama babbar jaruma,” inji Fa’iza. Ta ƙara da cewa, “Ina godiya a gare shi, shi Aminu Bala Mailalle, da ya ba ni wannan damar a fim ɗin sa, Sawun Giwa.”
Allah Sarki Fa’iza Muhammad Na tausaya Maki Komai Daman Rabone kiyi Hakuri Ki Kuma Godewa Allah.