Tsakure daga cikin jawabin shugaban Kwalejin Ilmi ta Tarayya (FCE) da ke Katsina, Farfesa Aliyu Idris Funtua, a taron ƙara wa juna sani kan ƙa’idojin rubutun Hausa wanda aka fara gudanarwa a yau a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU):
“Mu na godiya ga Allah maɗaukakin Sarki. Ina mai matuƙar farin ciki da godiya saboda gayyata da wannan sashe ya yi domin in shugabanci wannan taro mai muhimmanci. Lokacin da aka buƙaci da in zo in shugabanci wannan taro, na so in ja jiki a matsayi na na almajiri domin ina ganin fage ne da ya kamata a ƙyale shaihunan malamai a fagen harshen Hausa su zo su yi ruwa da tsaki.
“Hausa, kamar yadda na fahimta, harshe ne mai yaɗo, mai kuma amsar canje-canje kamar sauran manyan harsuna na duniya.
Hausawa da harshen su da kuma al’adun su sun shahara matuƙa a duniya. Shaharar su ce ta jawo baƙin masana da ‘yan kasuwa, abin da kuma ya taimaka wajen samun bunƙasar ciniki da al’adu da sha’anin mulki da kuma halin zamantakewa. Don haka ne na ke ganin muhimmancin wannan taro a kan daidaitacciyar Hausa tare da ƙa’idojin rubutun ta.
“Ko da yake Turawa sun zo mana da al’amura na ci-gaba waɗanda su ka shafi fannonin rayuwar mu na yau da kullum, to amma a gani na wata babbar ɓarna da su ka yi mana ita ce ta rushe rubutun Ajami tare da maye shi da na boko. Duk da yake dai haruffan Larabci Bahaushe ya lanƙwasa ya mayar da su Hausa, to amma da an bar mana abin mu da yanzu mu na da namu salon rubutun abin tinƙaho a gare mu ‘ya’ya da jikoki.
“Ajami rubutu ne da manyan malamai irin su Malam Abduljalil Ɗanmasani, da Ibn Sabbagh Muhammad bin Abubakar Al-Kashnawi Arabi (Ɗanmarna) da Malam Na Birnin Gwari su ka yi a cikin ƙarni na 17 da kuma 18, da kuma dai ayyukan da aka samu an yi a kan Ajami a cikin ƙarni na 19 zamanin jihadin Ɗanfodiyo sun nuna cewa Bahaushe, kamar Larabawa da Indiyawa da Sinawa, mutum ne da ya so ya ƙirƙiri hanyar rubutun sa na kan sa. Irin ƙoƙarin da Wali Ɗanmasani ya yi na daidaita sautin ‘tsa’ da ‘ƙa’ wanda babu su a sauti na Larabci da dai sauran aikace-aikacen da aka gabatar a cikin Ajami ba ƙaramin al’amari ba ne.
“Turawa sun kawo rubutun boko ga Hausawa bisa manufa da tsari wanda ya dace da su. Tun kuwa daga lokacin da su ka kawo wannan tsarin har zuwa yanzu, masana su na ta ƙoƙarin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa domin a sami sauƙin fahimta ta bai ɗaya tun da kuwa Hausa ta na da kare-karen harshe da dama. Turawa kamar su J.F. Schon, C.C.H. Robinson, Frank Edgar, R.S. Fletcher, Professor D. Westermann, Sir Hanns Vischer, da dai sauran Turawa da dama sun yi aikace-aikace domin fito da daidaitacciyar Hausa wadda za ta zama karɓaɓɓiya ga kowa, kuma domin a sami sauƙin rubutu a cikin Hausa. Idan aka duba, rubutun Hausa yanzu aka kuma duba rubutu musamman ma irin wanda G.P. Bergery ya yi, za a ga cewa lallai an sami cigaba. Tun daga shekara ta 1932 lokacin da Gwamnatin Jihar Arewa ta kafa kwamitin daidaita ƙa’idojin rubutu ake ta samun aikace-aikace a kan wannan al’amari har zuwa yau. Wannan kuwa abin yabawa ne matuƙa.
“Abin lura a yau shi ne, akwai matsaloli da su ke sosa zuciya dangane da aiki da daidaitacciyar Hausa da ƙa’idojin rubutu. A yau an samu ƙaruwar marubuta da su ke saɓa ƙa’idojin da aka tanada don mai rubutu da Hausa a kowane fanni na rayuwa. Akasarin ɗaliban makarantu tun daga firamare har zuwa jami’a ba su kula sosai da ƙa’idojin da aka tanada wajen magana da rubutu da Hausa. Haka kuma ana yi wa ƙa’idojin rubutu da Hausa karan tsaye a shafukan sadarwa na zamani (social media). Kaso mafi tsoka daga masu amfani da waɗannan kafofi na ci wa ƙa’idojin rubutu fuska matuƙa, kuma ana ji ana gani an sa ido.

“Yau mun yi dace, wannan sashe mai albarka ya shirya taron masana daga ciki da wajen ƙasar nan domin neman bakin zaren. Wajibin mahalarta taro ne da su tattauna tare da kawo shawarwari ƙwarara waɗanda masu ruwa da tsaki za su bi don shawo kan ɗaukacin matsaloli ko dalilan da su ke sanyawa ake kaucewa ko saɓa daidaitacciyar Hausa da ƙa’idojin rubutu da kuma Magana da Hausa.
“Ina ƙara jaddada godiya ta ga wannan jami’a, musamman kwamitin shirya wannan taro. Haka kuma, mu na godiya ga duk wanda ya samu damar halartar wannan taro mai albarka.
“Allah Ya sa a yi taro lafiya, a tashi lafiya. Allah Ya albarkaci abin da za a tattauna a kai. Allah Ya ƙara ɗaukaka wannan harshe namu mai albarka.”
