1. ‘Yan’uwa na zo in faɗa muku,
Ra’ayi na don ku ji gaskiya.
Bisa waƙar Zungur da yai,
Da ya tsara batun jamhuriya.
2. Wato ta Arewa batun da yai,
Jamhuriya da mulukiya.
Har ma a cikin waƙar ya ce,
Babu damar rushe mulukiya.
3. Ya wo dai zance mai yawa,
Mai daɗi ga kuma gaskiya.
Ya dai dage ya ƙarfafa,
Bisa kan mulki na mulukiya.
4. Bisa kan hanyar da ya dogara,
Tutocin Shehu abin biya.
Ko ni ma dai na gaskata,
Bisa kan mulki na mulukiyya.
5. Ɗanfodiyo ya ba malamai,
Tutar sa fa don su bi gaskiya.
Su ka ko zauna bisa kan haka,
Bisa kan mulki na mulukiya.
6. ‘Yan baya fa sai su ka shantake,
Su ka sau hanya mai gaskiya.
Su ka dinga biyar son zuciya,
Su ka sa wa kan su rububiya.
7. Sai Gwamna ya zo daga Ingila,
Wani mai gashin bakin tsiya.
Sunan sa fa Lugga ake kira,
Sai ya karɓe tutar gaskiya.
8. Yanzu ma a Kaduna akwai su duk,
A cikin wani ɗaki gu ɗaya.
Sai Gwamna ya ba su fa daftari,
Su ka zama shaiɗanun duniya.
9. In sun hau har da bajujala,
Da su begila duk baki ɗaya.
Ingilish sun ka ɓatar da su,
Su ka bar hanyar mai gaskiya.
10. In ma kai niyyar gaida su,
Sai kai sujjada baki ɗaya.
Haka ma shari’ar su idan ka je,
Sai sun so za su bi gaskiya.
11. Cutar talakawa ta yi yawa,
Wasu ma da yawa sai shan giya.
To don haka ne ban yarda ba,
Bisa waƙar nan ta Sa’adiya.
12. Amma a wajen da ya ce kurum,
Babu damar rushe mulukiya.
Shi ne na taho zan bayyana,
Jama’a ku taho ku ji gaskiya.
13. Asalin Sarki ba gardama,
A cikin Daura ne ka jiya.
Da maciji ne wani mai faɗa,
Ya fito a cikin wata rijiya.
14. Shi ne asalin kalmar ku san,
Don ku gane zancen gaskiya.
Daga baya ga halin zamani,
Su ka ƙara har da Sarauniya.
15. Kuma rushe gini na mulukiya,
Ya taho mana ba wata kariya.
Ba daɗewa kan ‘yan shekaru,
Za mu tsunduma kan jamhuriya.
16. Ingilishi nan na ƙasar mu duk,
Za su bar mana nan Najeriya.
Wato mulkin kai zai iso,
Mu fice daga mulkin danniya.
17. Na faɗa na ƙara faɗa muku,
Za mu san mulkin Najeriya.
Ku tuno zancen kuma Ja’afaru,
Sarkin Zazzau mai gaskiya.
18. Ya sa jama’a kishin ƙasa,
Ya nuna nufin Najeriya.
Ga Tafawa-Ɓalewa da yai batu,
Turawa nai mana danniya.
19. Har Aminu na Bauci da yai batu,
Mun sami jawabin gaskiya.
Mun ƙaru da haske mai yawa,
Mun lura da halin duniya.
20. Ingilishi na cutar mu yau,
Mun zamo bayin su a duniya.
Tan gyaɗa wai yau fam sha shida,
Babu imani daga zuciya.
21. Auduga kuwa sai ɗiba su ke,
Ba a zance wannan ko ɗaya.
Haka nan kuza can Jos in ka je,
Ta’ajibi zai cika zuciya.
22. Sun ɗiba sun je sun sayar,
Ramukan sun bar su waje ɗaya.
Ko rufewa ma ba sa kula,
Sun ɓata ƙasar baki ɗaya.
23. Ko’ina sun samu sarakuna,
Sun haɗe kai duk baki ɗaya.
Ba mai magana ko ƙanƙani,
Wa zai magana ai tankiya?
24. Ga mutanen ƙauye sai gwadduna,
Ba abinci bare gun kwanciya.
Abin ajabi ko tausayi,
Sai ka zaga Najeriya.
25. Ko’ina ba kwalta ko kaɗan,
Babu hanya mai kyau ko ɗaya.
Duk Arewa fa sai kwaleji guda,
To bare yunibastin duniya.
26. Ga ta nan wa zai ba mu shi,
Ingilishi na nan Najeriya?
Da dai mulkin en’e duka,
Mai kyau ne ba wata danniya.
27. To me zai sa haka nan da nan,
Har a rushe Sarakin Indiya?
Mulkin su ya zam ya faɗi duk,
Har ƙasar ta zamo jamhuriya.
28. Haka ma a ƙasar nan za a yi,
Hanya kusa ba wata tankiya.
Ni a zato na ma jibi ne,
Ko ko ma gobe da safiya.
29. Shugaba na nan ne zan tsaya,
Ni ne yaron ka na gaskiya,
Ilimin ka ƙwarai da ka bayyana,
Shi ne tsarin Najeriya.
30. Waƙar nan taka haƙiƙatan,
Na yabe ta ƙwarai baki ɗaya.
Kuma ba ni da suka ko kaɗan,
Jumlatan sai baitin nan ɗaya.
31. Ka san ra’ayi ba ya ɓata,
Dole ne in faɗe shi a gaskiya.
Kuma Allah shi ne Shahidi,
Ƙaunar ka na ke duk safiya.
32. Ni ne Mudi daga can Kano,
Unguwar Darma ka ji gaskiya.