HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya, wato ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN), reshen Jihar Bauchi, ta karrama fitattun jaruman Kannywood Jamila Umar Turaki Nagudu da Sulaiman Bosho a ranar Lahadi.
Haka kuma ƙungiyar ta karrama wasu fitattun jama’ar gari a taron farko da ta shirya cikin wannan shekara ta 2022.
An gudanar da taron a otal ɗin Zaranda da ke garin Bauchi a ranar Lahadi da ta gabata, 16 ga Janairu, 2022.
A wata sanarwa da ya bayar, ɗaya daga cikin jigogin MOPPAN a jihar, Alhaji Ɗanlami Adamu (Yanke-Yanke), ya bayyana cewa taken taron shi ne, “Sadarwa ta Hanyar Fim Don Inganta Tarbiyya Mai Ɗorewa”.
Ban da Nagudu da Bosho, mutanen da aka karrama ɗin sun haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Hon. Ɗanlami Ahmed Kawule (Barden Arewan Bauchi na farko), Hon. Abdurrazak Nuhu Zaki (Magajin Garin Ningi) da sauran su.
Taron ya samu halartar manyan mutane da su ka haɗa da kwamishinoni, sarakuna, malamai, da jami’an gwamnati da su ka haɗa da Shugaban Hukumar Raya Al’adu ta Ƙasa (National Troupe of Nigeria (NTN), Alhaji Ahmed Mohammed Ahmed.