• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Atiku ya yi wa ‘yan Neja matashiya: Ku tuna da ibtila’in da mulkin APC ya jefa ku ciki

by DAGA WAKILIN MU
January 22, 2023
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar ya na yawani a taron Minna

Atiku Abubakar ya na yawani a taron Minna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’ar Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya da su tuno da shekaru sha shida na mulkin PDP kuma su kwatanta su da shekaru bakwai na mulkin gwamnatin APC da ya kawo matsanancin baƙin ciki da wahala da fatara da yunwa da bala’i da rashin tsaro ga al’umma. 

Daga nan ya yi kira ga ‘ya’yan jihar da ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya da su tabbatar sun aje kyakkyawan tarihi da kyautata wa ‘yan baya ta hanyar korar gwamnatin APC ta hanyar ƙin zaɓen dukkan ‘yan takarar ta a zaɓuɓɓukan da za a yi a watan gobe. 

Atiku ya yi wannan kalamin ne a wajen taron yaƙin neman zaɓen PDP da aka yi a Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Asabar.

Akwai alamun cewa filin Kasuwar Bajekoli da ke unguwar Shango a garin Minna bai taɓa ganin dandazon mutane ba irin wanda ya gani a ranar Asabar wajen karɓar baƙuncin Atiku da Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.

Rundunar yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ta isa Minna ne a ranar Asabar inda jama’a su ka yi dafifi domin tarbar su ta yadda filin ya cika ba masaka tsinke.  

Tun misalin ƙarfe 8 na safe magoya bayan jam’iyyar su ka cika filin Kasuwar Bajekolin, a yayin da wasu kuma su ka nufi babban filin jirgin sama na Minna mai nisan kimanin kilomita daga cikin gari domin tarbar Atiku da Okowa, da kuma sauran manyan baƙi da su ka haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, Gwamnan Jihar Akwa Ibom,  Emmanuel Udom, da tsofaffin gwamnoni Boni Haruna na Adamawa, Liyel Imoke na Kuros Riba, Malam Ibrahim Shekarau na Kano, da sauran su da dama.

Cinkus ɗakin tsumma! Dandazon masoyan Atiku a taron Minna

Filin Kasuwar Bajekolin da ke Shango ya cika maƙil da dubban magoya bayan jam’iyyar PDP. Wasu ma daga wajen filin su ka tsaya, wanda hakan ya jawo cinkoson motoci  cika a kan manyan hanyoyin Minna.

Tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna), wanda shi ne shugaban rundunar yaƙin neman zaɓen PDP a jihar a zaɓen 2023, shi ma ya yi kira ga jama’a da su fitar da APC daga mulkin jihar domin, a cewar sa, ba ta tsinana komai ba sai jawo baƙin ciki da wahala ga jama’a.

Sauran waɗanda su ka yi jawabi a taron sun haɗa da mataimakin Atiku a takara, wato Gwamna Okowa, da Shugaban PDP na ƙasa,  Dakta Iyorchia Ayu, da Gwamna Aminu Tambuwal, da Dino Melaye, da Gimbiya Rakiya Atiku (maiɗakin Atiku Abubakar) da Sanata Zaynab Kure, da shugaban PDP na Neja, Tanko Beji, da Gwamna Emmanuel Udom na Akwa Ibom, da sauran su, waɗanda kowannen su ya shawarci masu zaɓe a jihar da su fitar da APC daga mulkin jihar da ma tarayya. 

An ƙawata taron da hawan raƙuma da dawakai da raye-rayen gargajiya da waƙoƙin mawaƙa irin su Naziru Sarkin Waƙa da sauran su.

A ƙarshe, Dakta Babangida Aliyu ya shirya wa Atiku da sauran jiga-jigan jam’iyya walimar cin abincin rana a gidan sa.

Loading

Previous Post

Abale zai angwance a mako mai zuwa

Next Post

Hankali bai ishi Tinubu ba, inji Naja’atu Mohammed bayan ta koma wajen Atiku

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Hajiya Naja'atu Mohammed tare da Atiku Abubakar da kakakin kamfen ɗin Atiku, Sanata Dino Melaye, a gidan Atiku a Abuja a ranar Lahadi

Hankali bai ishi Tinubu ba, inji Naja'atu Mohammed bayan ta koma wajen Atiku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!