TA tabbata a yau Asabar, 8 ga Yuli, 2023, furodusa a Kannywood, Alhaji El-Sa’eed Yakubu Lere, ya zama mai igiya uku.
An ɗaura auren sa da abar ƙaunar sa, Saudat Ibrahim Rigasa, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a gida mai lamba E97 Titin Sabon Afaka, ‘Yankifi, Rigasa, Kaduna, a bisa sadaki N150,000.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Alhaji Yerima Shettima, Alhaji Adamu Bello Ability, Jamilu Adamu Kochila, Shafi’u Magaji Usman Namaigero, Ibrahim Shasha, Nura Musa Kuriga, Al-Amin Abdullahi Albani, da kuma ma’aikatan Vision FM, DITV, Liberty, da sauran su.

Kafin ranar ɗaurin auren an yi wasu shagulgulan biki a gidan su amaryar da ke Rigasa.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa amarya Saudat ma’aikaciyar gidan rediyon Vision FM ce, inda Lere ya taɓa zama shugaba.
A yanzu Lere matan sa uku kenan.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.



