FITACCEN jarumin barkwanci kuma ƙwarren mai yin zanen fostar finafinai, Ali Muhammad Idris (Ali Artwork), ya yi bankwana da kwanan shago.
A ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 aka ɗaura auren sa da sahibar sa Hauwa’u Muhammad Bello.
An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a masallacin Juma’a na Filin Kashu da ke Unguwa Uku, Kano, a kan sadaki N100,000.
Jarumin, wanda kuma ake yi wa laƙabi da ‘Maɗagwal’, ya shaida wa mujallar Fim cewa Naziru M. Ahmad da Isah Bawa Doro kaɗai ne ‘yan Kannywood da su ka halarci ɗaurin auren, amma kuma wasu daga cikin manyan mutanen da ya ke mu’amala da su sun tura wakilai.

Kafin ranar ɗaurin auren, an yi walima a masallacin Habibu Yalo da ke Unguwa Uku, inda Sheikh Abdulrasheed Maƙarfi ya halarta.
Da mujallar Fim ta tambayi Ali Artwork abin da zai ce game da wannan rana ta farin ciki a gare shi, sai ya ce, “Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Mu na godiya ga Allah (s.w.t.) da ya nuna mana wannan rana mai albarka, wanda aka ɗaura aure na da masoyiya ta Hauwa’u.
“Mu na roƙon Allah ya sa mana albarka a cikin wannan aure, Allah ya ba mu zuri’a nagari, mai albarka, darajar Annabi Muhammad (s.a.w.).

“A ƙarshe, mu na miƙa saƙon ban-gajiya da godiya ga ‘yan’uwa, masoya da abokan arziƙi waɗanda su ka samu damar halartar auren mu da waɗanda su ka yi mana addu’ar fatan alkhairi. Allah ya saka masu da alkhairi. Na gode.
A jiya Asabar, 26 ga Fabrairu, jarumin da amaryar sa sun shilla zuwa Legas, inda aka gayyace shi wani bikin bada awad mai suna ‘Nigerian Youth Achievers Awards’.

Da alama kuma a can ne Ali da Hauwa’u za su yi zaman amarci, wanda a turance ake kira ‘honeymoon’.
Allah ya ba su zaman lafiya da dattin ɗaki, amin.


