• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mukhtar Hassan Hadi ne Hafsat ta aura, ba ɗan gidan Abacha ba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
February 27, 2022
in Ranar Murna
0
Amarya Hafsat da ango Mukhtar

Amarya Hafsat da ango Mukhtar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAHAIFIN Mukhtar Hassan Hadi, matashin da jarumar Kannywood Hafsat Idris ta aura jiya, da ita kan ta jarumar, sun kira mujallar Fim a waya a yau sun bayyana cewa ba ɗan gidan marigayi Janar Sani Abacha ta aura ba.

A safiyar yau Fim ta samu labarin cewa Hafsat, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Ɓarauniya’, ta yi aure jiya a asirce a Kano.

Wata ƙawar Hafsat ɗin, wadda ta buƙaci mu sakaya sunan ta, ita ce ta faɗa mana cewar ɗan gidan Abacha, wanda ba ta faɗi sunan sa ba amma ta ce “wanda aka haifa a Villa”, shi ne jarumar ta aura.

Ganin irin kusancin da ke tsakanin ƙawar da Hafsat, babu dalilin da zai sa mujallar Fim ta yi kokwanton labarin, musamman da ta ce Hafsat ɗin ce ta faɗa mata hakan da bakin ta.

Kafin wallafa labarin, mun nemi jin ta bakin Hafsat ɗin, amma hakan ya ci tura saboda ta kashe waya, sannan ba ta da niyyar zantawa da manema labarai a kan auren.

Sai dai ɓullar labarin ke da wuya sai Hafsat ta kira wakilin mujallar Fim a gigice ta faɗa masa cewa ita sam, ba ɗan gidan Abacha ta aura ba.

Ta faɗa wa wakilin mu cewa ta na so a gaggauta cire labarin daga gidan yanar mujallar.

Hafsat ta nuna cewa babban ɗan Janar Abacha, Alhaji Mohammed Abacha, shi ma ya damu kan lamarin.

“Mohammed ya fara magana, sai ku je ku cire shi,” inji ta.

Saƙon da Hafsat ta wallafa a Instagram

Da wakilin mu ya buƙace ta da ta yi masa ƙarin bayani dangane da auren, sai ta nuna abin da ta ke so a rubuta, ta ce, “Ba ku san wanda Hafsat Idris ta aura ba, kawai kun yi ‘mistake’. Ku je ku cire shi,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, “Babu wani bayani da zan ba ku… Ku je ku cire shi gaskiya tun kafin ya zama babban ‘issue'”.

Daga bisani, Hafsat ta hau Instagram inda ta faɗa wa jama’a cewa ba ɗan Abacha ta aura ba.

A saƙon da ta wallafa, jarumar ta ce, “Assalamu alaikum. Ina miƙa saƙon godiya na ga  dukkanin masoya, ‘yan’uwa da abokan arziki na fatan alkhairi da su ka min. Sai dai ina son na yi magana a kan raɗe-raɗin da ke yawo, musamman ‘bloggers’ da ke ‘update’ a kai na, cewa mijin da na aura na da alaƙa da gidan Abacha. To wannan ba gaskiya ba ne, ba shi da alaƙa da su. Na gode.”

Shi ma mahaifin angon, wanda sananne kuma babban ɗan kasuwa ne a Kano, ya kira wakilin mu inda ya tabbatar masa da cewa ɗan sa ne Hafsat ta aura, ba ɗan Abacha ba.

Daga nan ya buƙaci a gyara labarin.

Sakamakon ƙurar da labarin ya tayar, mujallar Fim ta tuntuɓi ƙawar Hafsat ɗin nan da ta ba mu labarin cewa ɗan Abacha ne jarumar ta aura.

Sai ta ce, “Ba shakka ita ta faɗa mani. Sai dai ko ɗan ‘family’ ɗin su Abacha ta ke nufi, ba ɗan Abacha na cikin sa ba. Amma ba shakka ta ce ɗan gidan su Abacha ne. Saboda haka idan ma kuskure ne ko ƙarya aka yi, to daga gare ta abin ya samo asali.”

Mujallar Fim dai ta cire sunan gidan Abacha daga labarin farko da ta buga kamar yadda Hafsat da surukin ta su ka buƙata.

Loading

Tags: aureƁarauniyaHafsat IdrisHassan HadiJanar Sani Abachakannywood actressMohammed AbachaMukhtar Hassan Hadi
Previous Post

Jarumar Kannywood Hafsat Idris ta yi aure a asirce

Next Post

Aure: Jarumin barkwanci Ali Artwork da Hauwa’u sun zama ɗaya

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Ango Ali Artwork da amarya Hauwa'u a cikin jirgin sama

Aure: Jarumin barkwanci Ali Artwork da Hauwa'u sun zama ɗaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!